MDD na kira ga ƙasashen duniya su ceci tattalin arzikin Afghanistan daga durƙushewa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana cewa dole ne ƙasashen duniya su ɗauki mataki domin ceto Afghanistan daga durƙushewa ta hanyar saka kuɗi cikin tattalin arzikin ƙasar.
Mista Guterres ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke New York.
Tun bayan da Taliban ta karɓe iko da gwamnatin ƙasar a watan Agusta ne aka dakatar da asusun ajiyar Afghanistan ɗin da ke ƙasashen ƙetare, haka su ma ƙungiyoyi da ke bayar da tallafi suka daina tura kuɗi zuwa bankunan ƙasar.
Sai dai Mista Guterres ɗin ya bayyana cewa za a iya gyara al'amura ba tare da kuɗin da za a bayar ba sun shiga hannun ƴan Taliban ɗin ba.
''Akwai buƙatar mu nemi duk wata hanya da za mu sa tattalin arzƙin ƙasar ya farfaɗo ba ba tare da saɓa ƙa'idar ƙasa da ƙasa ba. Dole ne mu nemi hanyoyin da za su bai wa ƙwararru da ma'aikatan farar hulan Afghanistan damar ci gaba da aiki ga ƙasarsu. Ina kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki mataki ta hanyar zuba kuɗi cikin tattalin arziƙin Afghanistan domin ceto shi daga durƙushewa.," in ji shi
*A halin yanzu dai Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin agaji na samun abinci da magunguna ƙalilan domin taimaka wa mabuƙata.
Batun bayar da agaji da kuma shawo kan wahala da yunwar da ake ciki a Afghanistan na daga cikin muhimman abubuwan da za a tattauna a taron ƙungiyar ƙasashe 20 mafi ƙarfin tattalin arziki na duniya wato G20 da za a yi a ranar Talata.
Haka kuma za su tattauna kan barazanar da ake samu daga wasu sabbin masu riƙe da makamai a ƙasar.











