Katse sadarwa: Ina ma'aikatan jihar Zamfara za su karbi albashi?

Garin Gusau

Asalin hoton, Maibiredi Tv

Bayanan hoto, Mazauna Zamfara sun ce matsalar katse layukan sadarwa ta shafi bankunan jihar
An wallafa

Hankalin ma'aikata a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ya koma kan yadda za su karbi albashinsu yayin da suke rayuwa babu hanyoyin sadarwa da toshe intanet a fadin jihar.

Fiye da makwanni uku kenan da aka toshe hanyoyin sadarwa da intanet a faɗin Zamfara, matakin da hukumomi suka ce sun ɗauka domin ƙoƙarin magance matsalolin ƴan bindiga masu kai hare-hare da satar mutane a jihar.

Matakin toshe layukan salula ya shafi harakokin banki, inda wasu mutanen jihar suka ce sai sun tafi wasu jihohi makwabta kafin su iya cire kudi a asusunsu na banki.

Wani mazauni jihar da ya tsallako yankin Kaduna ya ce mutane na cikin mayuwacin hali, kuma yanzu hankalin ma'aikata ya koma kan albashinsu da kuma yadda za su karbi haƙƙinsu.

"Yawancin ƙananan hukumomi babu na'urar ATM, sai an shigo Gusau, kuma wannan matakin na toshe layuka ya shafi wasu bankunan garin," in ji shi.

Ya kara da cewa da bankunan kawai aka dogara, saboda toshe layukan sadarwa ya shafi masu sana'ar hada-hadar kudi da na'urar POS.

Matakin da aka ɗauka ya shafi kama duk wanda aka kama yana amfani da hanyoyin sadarwa ta ɓarauniyar hanya.

Sadarwa ta yi wahala a Zamfara musamman ga manema labarai domin tuntubar gwamnati kan matakin da suka ɗauka na yadda za a biya ma'aikata albashi.

Ko da yake wata sanarwa da hukumomin Zamfara suka fitar sun ce sun fara rabon kayan tallafi ga al'ummar jihar, bisa la'akari da mawuyacin hali da jama'a ke ciki sanadin matakan murkushe 'yan fashin daji da aka dauka.

Wannan layi ne

Za a biya albashi?

Rahotanni sun ce mutane na shan wahala kafin su karɓi kuɗi a banki, kasancewar wasu bankuna sun takaita aiki saboda toshe hanyoyin sadarwa ya shafe su.

"Idan ka je banki za a ce babu network kuma taron mutane ya yi yawa a bankin."

Wannan yanayi a cewar wasu ma'aikatan ba su da tabbas kan albashinsu da kuma yadda za su karɓa cikin lokaci a bankunan.

Ko da yake wani ma'aikacin jihar ya ce ya ga tallafin kuɗi da aka tura masa daga gwamnatin Zamfara.

A cewarsa: "Bayan na fito daga jihar na ga an turo min kudi N10,000 kuma sakon na cewa daga gwamnatin Zamfara."

Don haka a ganinsa ma'aikata za su samu albashinsu kuma gwamnati ba ta fitar da wata sanarwa ba da ke cewa za a samu matsala ba.

Zaɓin da ya ragewa ma'aikata

Mazauna Zamfara sun ce matsalar katse layukan sadarwa ta shafi bankunan jihar

Asalin hoton, Maibiredi Tv

Idan dai har ba a buɗe layukan sadarwa ba da intanet, akwai yiyuwar za a samu cincirindon ma'aikata a bankuna domin albashinsu.

A wata hira da BBC, gwamnan Zamfara Bello Muhammad, Matawallen Maradun, ya ce babu ranar buɗe layukan sadarwa a jiharsa.

Gwamnatin Zamfara kuma yanzu watakila na iya yanke shawarar dawo da hanyoyin sadarwar don ta biya ma'aikata albashi.

Ma'aikatu a jihar kuma na iya yanke shawarar biyan ma'aikata kuɗin albashinsu a hannu.

Ma'aikatan kuma na da zaɓin samun albashinsu idan sun tsallaka zuwa Sokoto ko Zaria, Zaɓi mai cike da hatsari.

Hatsarin ƴan bindiga

Duk da babu rahotannin da ke tabbatar da halin da ake ciki a Zamfara, amma ma'aikata za su iya faɗawa hannun ƴan fashi a hanyarsu ta zuwa karbo albashi.

Halin da mutane da dama suka shiga da kokawa da suke game da karancin abinci a yankuna, sakamakon rufe kasuwannin mako-mako da katse layukan sadarwa, zai sa ma'aikata shiga tsaka mai wuya.

Al'umma a Zamfara sun daɗe suna fuskantar hara-haren tare da ƙone garuruwansu daga ƴan fashi masu ɗauke da manyan bindigogi.

Hukumomi da jami'an tsaron sun yi iƙirarin cewa kwalliya na biyan kudin sabulu kan matakin da aka ɗauka na toshe layukan sadarwa da hana cin kasuwar mako-mako, amma har yanzu wasu yankuna na jihar da makwabta da rahotanni na cewa ana kai hare-hare da garkuwa da mutane.

Wannan layi ne