Indiya: Malamar da ta bai wa dalibai marasa galihu kyautar daruruwan manyan wayoyi

Bharti Kalra in her schcool

Asalin hoton, Bharti Kalra

Bayanan hoto, Bharti Kalra ta taimaka wa dalibai dama ta wajen samo musu wayoyi
    • Marubuci, Daga Swaminathan Natarajan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

A lokacin da annobar cutar korona ta bulla, an koma koyarwa ta intanet a makarantu da dama a fadin duniya.

Hakan ba shi da wata matsala idan har za ka iya sayen komfutar hannu ta yayi kuma intanet dinka na da kyawu, amma wadanda ba su da wannan damar fa?

Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (Unicef) ya ce rufe makarantu miliyan 1.5 da aka yi a Indiya sakamakon dokar kulle da aka sanya ya shafi dalibai miliyan 247, inda yaro daya cikin hudu ne kawai ke samun intanet.

Wannan wani abu ne da Malama Bharti Kalra ta sani sosai, don haka ta sanya a ranta cewa za ta tabbatar da dalibanta sun samu fasahar da suke bukata, don haka ba a bar kowa a baya ba.

"Mun samu yara 'yan aji 4 da 6 na sakandare sun yi nasara 100%, duk da ba su je makaranta ba, sai don koyar da su ta intanet. Abin na da gamsarwa sosai," a cewar malamar, wacce mataimakiyar shugabar wata makarantar gwamnati ce a Delhi.

"A tsarin ilimi na Indiya, sakamakon jarrabawar 'yan aji 4 da 6 na sakandare suke nuna hanyar da daliban ke kai.

Amma wannan ba abu ne mai sauki ba.

Deputy Chief Mister of Delhi Manish Sisodia giving away phones to students

Asalin hoton, Bharti Kalra

Bayanan hoto, Daliban Kalra sun karbi wayoyin a cikin wata biyu

Akwai dalibai 2,600 a makarantar da Malama Kalra ke koyarwa, inda mafi yawan daliban 'ya'yan marasa galihu ne.

A yayin da cutar korona ta fara yaduwa a Indiya, Kalra ta san cewa za a koma koyarwa ta intanet amma kuma ta san babu dalibinta da zai iya samun kayan fasahar da suke bukata.

Don haka sai ta dogara da neman tallafi daga wajen 'yan uwa da abokan arziki har aka hada manyan wayoyi (smartphones) 321 aka bai wa dalibanta marasa galihu.

Tana ganin saboda wadannan daliban sun samu damar karbar wayoyin don koyon karatu, shi yasa makarantar ta samu kyakkyawan sakamako kuma gwamnatin Delhi ta amince da zancenta, inda har ta samu lambar yabo a Ranar Malamai a watan Satumba.

To ko me ya sa ta yi irin wannan hobbasa ga dalibanta?

An yi wa wani dalibi rasuwa

A watan Yulin bara lokacin da annobar ta janyo aka rufe makarantar da take koyarwa, an dora wa Kalra nauyin kula da koyarwa ta intanet.

Students taking a oath saying they won't misuse it

Asalin hoton, Bharti Kalra

Bayanan hoto, Kalra ta umarci dalibai su yi rantsuwa cewa ba za su dinga amfani da wayoyinsu wajen aikata abin da bai dace ba

"Malamai suna gaya min cewa a ajin da ake da mutum 40 sai ka ga 10 zuwa 12 ne kawai suke karatu ta intanet."

A yayin da Kalra ke tunanin samo mafita don hana dalibai barin makaranta, sai ta ci karo da wasu iyali da ke cikin damuwa.

"Wani dalibina ya gaya min cewa ba zai iya sayen babbar waya ba saboda mahafinsa ya rasu kwana biyar da suka wuce."

Sunan dalibin Rohan Kumar.

Mahaifin yaron maigadi ne da ya ci gaba da aikinsa duk da bullar annobar don ya nema wa iyalinsa abin rufin asiri don da shi suka dogara. Sai dai abin takaici, sai ya kamu da cutar korona kuma ya rasu sakamakonta.

"Na kasa barci a daren nan," in ji Kalra.

"Ina ta tunanin: 'Ta yaya mahaifiyar wannan yaro za ta iya ci gaba da kula da iyalin nan?' Sai na hada kayayyaki kamar shinkafa da wake da man girki na ba su."

Rohan na zaune ne a gida mai daki biyu shi da mamarsa da kaninsa. A matsayina na malama, Kalra ta san cewa yana da muhimmanci ga Rohan ya ci gaba da karatunsa, duk da wahalhalun da iyalinsa ke fuskanta.

"Na sayi sabuwar waya da kudinta ya kai dala 110 na bai wa Rohan washegari. Ya yi farin ciki sosai."

A sakamakon haka Rohan ya koma bakin karatunsa, inda yake shiga ajin intanet da wayarsa ta smartphone.

Matsin tattalin arziki

Iyaye da dama da wasu daliban da suke kananan ayyuka a yanzu duk suna rasa ayyukansu, sannan harkokin kasuwanci da dama sun durkushe sakamakon annobar.

Bharti Kalra with a student

Asalin hoton, Bharti Kalra

Bayanan hoto, Dalibai da yawa sun sha wahala lokacin da aka koma koyarwa ta intanet

"Dalibanmu na gaya mana cewa iyalansu ba za su iya sayen abinci ba. Don haka babu batun ma sayen manyan wayoyi."

Kalra ta ce wa sauran malamai su ba ta sunayen daliban da ba za su iya sayen wayoyin ba. Daga nan sai ta fara shelar neman tallafi daga 'yan uwa da abokan arziki ta shafukan sada zumunta.

Kalra ta bayyana cewa dukkan daliban za su samu waya iri daya. Don haka ta gaya wa mutane irin samfurin da take so don duk su sayo iri daya.

Taimako daga 'yan uwa da abokan arziki

A cikin wata biyu duk masu bukatar waya suka samu, godiya ga Malama Kalra da 'yan uwa da abokan arzikinta.

"Wani dan uwana da ke zaune a Amurka ya aika taimakon manyan wayoyi 50, don tunawa da dansa da ya rasu sakamakon cutar numoniya," in ji Kalra.

Kanin Kalra da dan yayarta ne suka dauki dawainiyar ba da har wayoyi 100. Wani kawunta da ya yi ritaya ya ba da guda biyu sai wata kungiya mai zaman kanta da wani dan uwanta ke jagoranta ya ba da kyautar wayoyi 60. Sannan kawayenta da dama ma sun bayar.

"Wasu daliban ba ma su da kudin sayen nambar wayar da data. Don haka ni da sauran malamai muka taimaka ta wannan fannin."

Amma ba daliban makarantar ba ne kawai suka amfana da wayar, wasu daliban sun dinga barin kannensu na amfani da ita su ma a gida don shiga ajujuwansu ta intanet.

Students posing with new phones

Asalin hoton, Bharti Kalra

Bayanan hoto, Kalra ta ce ba tare da samun wayoyi ba, da daliban ba za su iya ci gaba da karatunsu ba

"Mutane da dama sun ce min sun koyi abubuwa da waya ta wayar."

Sakamakon jarrabawar yaran ya kawar da fargabar da wasu suka nuna da farko cewa wayoyin na iya bata yara. Yaron da ya zo na daya a wani aji na daga cikin daliban da suka samu wayar kyauta.

Manyan buruka

Rohan Kumar ya ci jarrabawarsa kashi 90 bisa 100 kuma a yanzu yana fatan shiga kwalejin fasaha don yana so ya kirkiri wata manhaja.

Kumar reading at his home

Asalin hoton, Rohan Kumar

Bayanan hoto, Kumar na son shiga kwalejin fasaha

"Na koyi abubuwa da dama a intanet. Na san abubuwa kan kasuwar hannayen jari, da kasuwancin intanet da sauran su," in ji shi.

Maigidan da su Kumar ke haya a ciki yana ba shi dama ya yi amfani da wifi dinsa wanda haka ke sa ya samu damar kallon bidiyo na tsawon sa'o'i. Ya ce wannan karamci ya yi tasiri sosai a rayuwarsa.

A yanzu yana son bai wa kanina mai shekara 10 kuncen wayar.

Ga shi kuma mahaifiyar Kumar tuni ta samu aiki a matsayin mai yi wa baki maraba a wata ma'aikata. Sai dai duk da haka aikin nata ba zai iya daukar nauyin biyan karatun Kumar na fasaha ba.

Don haka sai da Kalra ta taimaka.

Bharti Kalra receiving an award

Asalin hoton, Bharti Kalra

Bayanan hoto, Kalra ta samu lambar yabo ta musamman daga gwamnati saboda kokarinta na aiki

"Na gaya masa ya yi kokari ya samu shiga wata kwaleji mai kyau. Zan yi kokari na ga na biya kudin makarantar ko yaushe."

Daliban sun yi matukar jin dadin abin da malamarsu ta yi musu na sadaukarwa, amma ita ma ta koyi wani abu daga wannan lamari.

"Ban san wane kalubale ne zai sake bullowa ba. Amma na san da taimakon shafukan sada zumunta zan iya neman tallafi a saukake. Ina fatan dai kar ma bukatar hakan ta taso."