IPhone 13 za ta inganta tsarin daukar hoto da bidiyo

    • Marubuci, Daga Cristina Criddle da David Molloy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology reporter
  • An wallafa

Kamfanin Apple ya sanar da sabon samfurin wayarsa ta iPhone 13, wacce za ta iya daukar faifen bidiyon ''hoton fuska'' mai cikakken fasali - wanda hakan ke nufin wani bangare na hoton da abin da ka dauka zai kasance ya fita sosai, a yayin da sauran bangarorin kamar na baya da kuma gefensa za su kasance dusu-dusu.

Sabon yanayin daukar bidiyo ''na nuna yadda wani ke shirin shiga cikin bangon kewayen hoton'' kana ya kan mayar da hankali a kan su, in ji kamfanin Apple - wani abu da ake kira ''mayar da daukacin hankali kan abu''.

Ita kadai ce wayar tafi-da-gidanka da za ta bai wa masu amfani da ita damar yin gyare-gyare da kwaskwarima bayan daukar hoton, jagoran kamfanin na Apple Tim Cook ya bayyana.

Amma kuma, akasarin sauran abubuwan da sabuwar samfurin wayar ta kunsa an kara sabuntawa ne daga samufurin na baya.

Haka kuma labarai game da aibun da ya shafi sirri a tattare da wayoyin kamfanin na Apple wanda ka iya bankada sakonnin kar-ta-kwana na masu amfani da wayoyin sun kankane wannan sabon batu.

A ranar Litinin ne kamfanin na Apple fitar da wani tsari na tsaro ga aibun da aka bayyana a baya wanda bata san da shi ba - wanda zai bai wa masu kutse damar shiga cikin bangaren sakonnin kar-ta-kwana ba tare da mai mai amfani da wayar ya latsa a kan layin da zai bude musu wani shafi ba ko kuma kundi.

Sabbin abubuwa

Sabuwar iPhone din ta kunshi guntun karfe mai sauri na A15, da kuma fuska mafi haske, da karfin batirin da zai kai tsawon sa'oi biyu da rabi, kana ta zo da sabbin launuka da suka hada da ruwan hoda, da shudi, da ja, da baki da kuma fari.

Sabuwar wayar ta iPhone na kuma da ma'ajiya mai daukar nauyin gigabait 500(500GB) wanda mafi karancin ma'ajiyarta ke kai wa har gigabait 128 (128GB) idan aka kwatanta da samfurin irinta na baya masu nauyin gigabait 64 (64GB) kawai.

Apple ya kuma bugi kirjin nuna goyon bayansa wajen kare muhalli, yana mai cewa an sarrafa wayar da kayyaki da dama da aka gama amfani da su - da suka hada da wayoyin eriyar da aka sarrafa daga robobin ruwan sha.

Kaddamarwar na zuwa ne a yayin da masu sayen ke cigaba da barin wayoyinsu na kai wa tsawon lokaci kafin su kara inganta su.

Kamfanin zuba jari na Wedbush Securities ya kididdige cewa masu amfani da wayoyin na iPhone kusan miliyan dari biyu da hamsin ne bas u inganta wayoyin na sub a har na tsawon shekara uku da rabi.

Paolo Pescatore, wani mai sharhi ne a hukumar PP Foresight da ya bayyana cewa da dama har yanzu ba su samu amfana da sabbin fasalin wayoyi na zamani ba.

"A yayin da da dama za su dauki inganta wayoyin a matsayin karuwa, akwai miliyoyin masu amfani da wayoyin da har yanzu ba su inganta su zuwa fasahar intanet ta 5G ba," ya ce.

Ana iya amfani da fasahar intanet ta 5G ne kawai a kan samfurin wayar iPhone 12, wacce aka fitar cikin shekarar da ta gabata, da kuma sabbin samfurin da aka sanar.

A cikin watanni ukun tsakiyar wannan shekarar, kamfanin Apple ya sayar da kusan kasha uku bisa dari (25.9%) na duka wayoyinsa masu amfani da fasahar intanet ta 5G a fadin duniya, kamar yadda kamfanin IDC na ma sharhin ya bayyana.

Marta Pinto, babban manajan bincike a kamfanin na IDC ya ce: "Da wannan sabon matsayi, wadannan alkaluma za su karu tare da kara karfi wajen maye gurbin mamayar da kamfanin Apple ya yi a wancan gurbin.''

"Rashin kasancewa na farko wajen Not being the first [kaddamar da wayoyi masu amfani da fasahar 5G] ya yi amfani.''

Shi ma kamfanin Apple ya kaddamar da samfurin kananan wayoyi na iPhone 13 Mini, da Pro da kuma Pro Max.

Samufurin wayoyin iPhone 13, da Pro da kuma Pro Max na kunshe da kyamarori uku kuma wanda Apple din ke kira " tsari n kyamara mafi inganci a yanzu".

Kudin samfurin wayoyin iPhone 13 mini ya fara daga fan dari shida da saba'in da bakwai (£679), yayin da iPhone 13 ya fara daga fan dari bakwai da saba'in da tara (£779).

Samfurin iPhone 13 Pro ita kuma kudin ta ya fara daga fan dari tara da arba'in da tara, kana mafi girma samfurin Pro Max ita kuma fan dubu daya da arba'in da tara (£1,049).

Ana daukaka kamfanin Apple wajen kirkirar sabuwar fasaha. Amma muddin wannan kaddamarwa ta kasancewa wani abu na daban, wannan daukaka ta zama tsohon ya

Babu wani sabon abu ko na musamman da aka sanar a nan. Kara sabunta wayoyinsa na iPhone, da Apple Watch da kuma iPad ya zama wani abu da aka saba gani, da rashin bayar da sha'awa, da kuma kariya.

Inganta sabon tsarin kyamara mai daukar bidiyo (wanda a kashin gaskiya ya yi kyau) sake sabunta na baya ne.

Ita kan ta gabatarwar, duk da cewa cikin sauki ne, amma babu takamaimen abubuwan da musamman ko na wata basira da za a rika tunawa da su a ciki.

Jita-jita game da kara inganta wasu abubuwan armashi, kamar misali wayoyin iPhones masu iya amfani da tauraron dan adam, duk daga karshe sun zama shaci-fadi.

"Wannan wata gagarumar sanarwa ce,'' in ji shugaban kamfanin na Apple Tim Cook - yana danganta wa da kayyaki kamar su sabuwar wayar iPhone 13, wacce ta ke kusan kama da samfurin iPhone 12.

Wasu na rade-radin cewa mai yiwuwa kamfanin na Apple zai daina lakaba wa samfurin wayoyinsa lambobi (kasancewar lamba 13 rashin sa'a ce ga wasu) - amma babu wani yunkuri mai kama da haka.

Har yanzu, Apple zai sayar da kayyakinsa da dama - sun saba yin hakan.

Ka yi tunanin da ya wuce batun gagarumin kiran kasuwar kana wanda ya kasance kaddamarwar da bata bayar da sha'awa ba - musamman ma daga kamfanin da ke son bayyana kan sa a matsayin mai basirar fito da sabuwar fasaha.

yi.

Agogon Apple Series 7

Kamfanin Apple ya kuma sanar da sabon samfurin sa na agogon Apple Watch.

Sabon samfurin na Series 7 ya fito da sake sabunta fasaali na farko ga agogon tun a shekarar 2018, kana zai kasance wanda ya dara girma kadan.

Mai sabon fasalin girman zai dace da kusan kashi hamsin bisa dari (50%) na karin rubutu a fuskarsa, kana yana da wurin lambobin yin rubutu a kai. Kana yana jurewa kura a karon farko.

Samfurin Apple Watch iOS 8 zai kuma iya gano tukin kekuna da suka hada da masu amfani da lantarki.

Amma kuma kamar yadda kafar yada labarai ta Blomberg ta bayyanam samfurin Apple Watch Series 7 ka iya fuskantar tsaiko wajen kerawa.

Kamfanin Apple ya ce sabon samfurin zai fita nan gaba kadan a bayan lokacin bazara, a yayin da za sauran kayyakin da ya kera kamar su sabuwar babbar wayar kan cinya ta iPad da kuma iPhone - da aka sanar a lokaci daya - za su fita a cikin mako mai zuwa.

Apple na da kasha arba'in da bakwai bisa dari (47%) na kasuwar agogon tafi-da-gidanka a duniya, kamar yadda wani bincike daga kafanin CCS ya bayyana.

"A dubawa ta farko, sabon samfurin agogon Apple wani sabon maimacin ne, amma mafi girman fuska da zai bayar damar amfani da manyan madannai, kana yanayin tsarin lambobi da haruffan tabbas za su kara saukaka yadda za a yi amfani da shi," Leo Gebbie, babban mai sharhi a kamfanin CCS ya bayyana.

Ya kuma ce ya yi tsammanin ganin batiri mai tsawon rai, yayin da masu amfani da shi suka dade suna fatan ganin cewa agogunan sun yi karko'', amma ba a sanar da wannan ba - ko da kuwa saurin caji ne.

"Duk da wannan damuwa, agogon na Apple na cigaba da samun kasuwa da dama, kuma ya kashe kasuwar sauran agogunan tafi-da-gidan-ka a kasuwanni ba kadan ba,'' ya ce.

Sabbin bayanai game da iPad

Apple ya kuma kaddamar da sabon samufurin iPad. Tim Cook ya ce cinikin iPad ya kara bunkasa zuwa kasha 40 bisa dari (40%) a cikin shekarar da ta gaba

Yana kunshe da karfin allon lantarki na A13, da kashi ashirin bisa dari (20%) na mafi saurin aiki daga irin samfurin irin na baya.

Apple ya ce za ta linka sau uku wajen sauri fiye da Chromebook".

Kudin sabuwar iPad ya fara daga dala dari uku da ashirin da tara ($329) kwatankwacin fan dari uku da sha tara (£319) kana akwai ragin farashi na dala dat biyu da casa'in da tara ($299) ga makarantu.

An kuma kaddamar da sabon samfurin iPad mini, wacce ke aiki da wayar USB-C, da taimakon fensirin Apple, kana babu madannai na sama - farashin ta ya fara daga fan dari hudu da sabain da tara (£479).ta.