Rikicin Afghanistan: Yadda dangantakar Turai da Amurka ta yi tsami

    • Marubuci, Daga Mark Lowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Europe correspondent
  • An wallafa

Wasu jerin rashin fahimta da aka samu musamman akan rikicin Afghanistan ya sanya wasu shugabannin kasashen Turai sake bibiyar alkarsu da shugaban Amurka Joe Biden, da kuma tunanin yadda za su iya rayuwa a gaba ba tare da Amurka ba.

Daga fargabar da aka shiga kan Donald Trump da kuma makomar dakarun Amurka karkashin Shugaba Biden, Emmanuel Macron ya ce shugabannin Turai sun ga sauyi daga gwamnatocin Amurka.

Yayin taron kungiyar Nato a watan Mayun 2017, Shugaban Faransa ya sanya dan yatsansa a hannun Shugaban Trump, yana kallon fuskarsa. "Ba abin a dauke kai ba ne", in ji shugaba Macron.

"A tattaunawar da za mu yi ba zan bar komai ya wuce ba."

Bayan shekara hudu, a taron G7 na farko da Joe Biden ya halarta a matsayin shugaban Amurka, haka dai Macron ya kara nuna fushinsa a lokacin.

A daidai lokacin kyamara ta dauki hoton abin, ya tsallaka duka tazarar da ke tsakaninsu ya nuna Biden a kirji. A zahiri ya nuna cewa akwai matsala tsakaninsu.

Amma a manyan biranen Turai kama daga Landan zuwa Berlin, Afghanistan ta dandani zaki da madacin mulkin Joe Biden.

Ba wai batun janye sojojin ne abin takaicin ba, sai na yadda Amurka ba ta tuntubi kawayenta ba yayin tsara janyewar, musamman ma ganin cewa a tun farko an tsara lamarin ne a karkashin shirin kungiyar tsaro ta Nato, inda aka aike dakaru daga kasashe 36, kashi uku cikin hudu ba na Amurka ba ne, abin da ya rikirkita tsarin kwashe dakarun kasashen duniyar kenan.

Aike dakarun kasar Jamus shi ne irinsa na farko gagarumi da kasar ta yi tun bayan Yakin Duniya Na Biyu, don haka damuwar yadda lamarin ya kaya ya matukar dugunzuma rai.

Wani dan takarar shugabancin gwamnatin Jamus a jam'iyyar masu ra'ayin rikau Armin Laschet, ya kira janyewar dakarun Amurkan da "babbar faduwar bakar tasar da Nato ta yi tun da aka kafa ta."

Shugaban kasar Czech Milos Zeman, ya kira lamarin da "ragwanci", yana mai cewa "Amurka ta rasa martabarta ta zama jagorar duniya."

Tsohon firaministan Sweden Carl Bildt, ya shaida wa BBC cewa: "An sa buruka sosai a lokacin da Joe Biden ya zama shugaban kasa - irin burukan da ba za iya cim musu ba.

Wata kididdigar jin ra'ayin jama'a ta Cibiyar Bincike ta Pew, a bara ya nuna cewa yawan Jamusawan da suke da yakinin cewa shugaban kasar Amurka zai yi abin a zo a gani a lamurran duniya ya karu daga kashi 10 cikin 100 a lokacin Donald Trump zuwa kashi 79 cikin 100 a lokacin Joe Biden.

Haka ma lamarin yake a Faransa.

Shugabannin nahiyar Turai na kallon salon da Amurka ta bi wajen janye dakarunta da kuma kalaman Joe Biden na cewa Amurkar ba za ta ci gaba da aika sojoji "don magance matsalolin wasu kasashen ba" - a matsayin abin da ke dawo musu da batun da Shugaba Trump ya sha nanatawa na tsarin sanya muradun Amurka a gaba fiye da komai.

Amma yayin da ake cikin wannan damuwar kan rashin samun bayanai tsakanin kasashen Turai da Amurka, mai yiwuwa ya yi wuri a fadi me hakan ke nufi wajen irin sauyin da aka samu tsakanin gwamnatocin Amurkan na yanzu da wacce ta gabata.

"Babbar barakar da aka fara samu a karkashin Trump ba ta da alaka da manufofin kasashen waje kuma lokaci guda sai ga shi manufofinmu sun bambanta," a cewar Nathalie Tocci, wata mai bai wa shugaban Tarayyar Turai shawara kan manufofin kasashen waje Josep Borrell, kuma farfesa a Jami'ar Harvard.

"Babban tashin hankalin da ke tattare da manufofin Trump ba kawai na kare muradun Amurka da sanya ta gaba da komai ba ne, har ma da alamun da ya nuna na son yin shiri da ire-iren Xi Jingpin da Putin.

"Maganar cewa ra'ayinmu ya zo daya da shi, shi ya sa ba a tuhume shi kan ra'yoyinmu kan lamarin Afghanistan ba.

"Yadda Amurka ke janye kanta daga harkokin kasashen duniya kamar yadda ta janye daga Afghanistan, za ta fi mai da hankali ne kan kare muradunta - to ina ga sauran kasashe kuma?"

Hakika, kan lamarin Afghanistan wasu na ganin kawai ci gaba ne na abin da aka san Amurka da shi, wato yin komai ita kadai. "Hakan sabon abu ne?" Mrs Tocci ta tambaya.

"Wannan shi ne korafin Turai a ko yaushe dangane da Amurka. Amma a yanzu Amurkar ce ta tsara ficewar ba tare da tuntuba ba, ba kamar lokacin shigar ba."

Rikicin Afghanistan da ya bullo wanda ya karu kan dama matsalolin da ke tsakanin Amurka da Turai, na kara ta'azzara dusashewar fatan da a da suke da shi na samun kyakkyawar alaka.

Mataimakin shugaban hukumar Turai Margaritis Schinas ya ce ya soke shirinsa na bulaguron da zai yi Amurka a mako mai zuwa "saboda ban gamsu da dangantaka kan dokokin tafiye-tafiye ba."

A yanzu EU ta cire Amurka cikin jerinta na kasashen da za a iya zuwa cikin nutsuwar rai: abin da wasu ke ganin a matsayin lamari da ke ta'azzara tsamin dangantakar.

A yanzu damuwar EU biyu ce. Ta farko, abin da ya faru a Afghanistan ka iya janyo wata matsalar ta kwararar 'yan gudun hijira, lamarin da zai dawo da irin abin da ya faru a 2015, lokacin da fiye da mutum miliyan suka tsere daga Syria da sauran wurare suka shiga Turai.

Na biyu kuma, watakila mayar da hankalin da Amurka za ta yi a kan kasarta kawai, hadi da Jamus babu Angela Merkel da Faransa wacce shugabanta ke fuskantar sake zabe da ke gabansa, za su bar gibi na shugabanci wadanda tuni Rasha da China sun fara cike shi.

Kuma hakan zai sa China ta ci gaba da yi wa Taiwan barazana ba tare da fargabar kutsen kasashen yamma ba.

"Akwai lokacind a Amurka ta yi magana kan ci gaba da tafiyar da ragamar duniya," in ji Carl Bildt.

"Amma a yanzu ba wannan ne yaren da ke fitowa daga Fadar White House ba. An tauye fatan da aka yi na farfado da dangantaka tsakanin Amurka da Turai. A yanzu an saddakar Amurka za ta dinga abubuwanta ne yadda ta so."