Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dubban 'yan Najeriya da ke rububin zuwa karatu domin yin rayuwa a Turai
- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
Bayan neman aiki akalla sau 200 a shafin LinkedIn ba tare da samun nasara ba, karshe dai ɗaliba yar Najeriya Modupe Osunkoya ta gane cewa lokaci yana kure mata don tsawaita zamanta a Belgium.
Zaman wata uku ne kawai ya rage mata, ko dai ta samu aiki ko ta bar kasar baki daya.
Sai dai akwai zabi na uku da take da shi, shi ne na yin rijista domin karatun digiri na uku tun bayan barin Najeriya a 2017.
"Ban taba tsammanin wai gani ina yin PhD ba amma idan na koma gida yanzu, babu wani aiki da ke jirana," kamar yadda matashiyar mai shekaru 28 ta shaida wa BBC.
Matsalar rashin aikin yi babbar matsala ce a Najeriya, kimanin matasa biyu cikin uku ba su da aikin yi, kuma suna rayuwa ne cikin ukubar talauci, sannan saboda yanayin rayuwa 'yan kasar da dama sun gwammace su niki gari su tafi kasashen waje maimakon zama a gida.
Don haka a bara Ms Osunkoya ta yi rijista don yin digiri na uku a Estonia wanda ke gudana tare tare da digiri na biyu na Master a Belgium.
Ta zauna a Estonia bayan da ta kasa samun aiki ko tayin yin PhD a Belgium ba.
Dalilin ke nan da ya sa take shirin ƙaura zuwa wata kasar da ke gabashin Turai domin samun damar yin karatunta.
Osunkoya ɗaya ce daga cikin ɗaliban Najeriya da yawa da basu kasance cikin, ko yayan manyan attajiran da ke karatu a kasashen waje ba.
A bara, kusan 'yan Najeriya 100,000 ne suka yi balaguro zuwa ƙasashen waje don yin karatu, a cewar ICEF Monitor, wata cibiya da ke bibiyar yawan daliban Najeriya da ke tafiya kasashen duniya yin karatu.
Mutane da yawa suna fatan zama mazaunan dindindin na ƙasashen da suka je karatu, musamman yan Afrika da ke zuwa Belgium
Foluwakemi, (wadda ba shi ne sunanta na ainihi ba) wata daliba ce 'yar Najeriya da ke Belgium, ta ce: "Mutane da dama sun kammala karatun digiri na biyu a kasar, maimakon su koma gida sun gwammace su tsaya su ci gaba da yin wani karatun walau difiloma ko ma Satifiket masu arha, duk a yunƙurin zama 'yan kasa."
Duk da samun digiri a fannin tattalin arziki a Najeriya, ta yanke shawarar farawa tun daga farko lokacin da ta isa Belgium, inda ta kammala kwas na shekaru uku a fannin gudanar da kasuwanci.
Ba ta yi watsi da yiwuwar samun digiri na biyu na Master da PhD ba idan ta kasa samun aikin da zai bude mata hanyar samun biza ta dindindin.
Daliba ta uku, Ifeoma, (ita ma ba sunanta na ainihi ba) wadda a yanzu haka take yin digiri na biyu tun lokacin da ta isa kasar a shekarar 2019 ta ce "ba na daukar shi da mahimmanci, kawai bata lokaci ne, ina yi ne kawai don bani da abun da zan yi''
Kudin makaranta kan kama daga yuro 1,000 a kowace shekara, sannan akwai ƙarancin tsadar rayuwa ga ɗalibai a Belgium, idan aka kwatanta da wasu ƙasashen Turai, abun da ya sa 'yan Afrika da yawa ke son kasar.
Za ka iya samun daki a kan yuro 300 a kowanne wata, in ji Osunkoya.
Kamar sauran mutane da yawa, ta bar gida ne da kudin zangon karatu daya kacal.
Ta dauki nauyin karatunta ne ta hanyar yin aiki har tsaron awanni 20 a mako, kamar yadda doka ta ba ta damar yin hakan, inda ta wannan hanya take samun yuro 1,000 a kowane wata.
Amma wurin da aka fi so ga ɗalibai da iyayensu ke da wadata sune kasashe masu magana da Ingilishi kamar Canada, Burtaniya da Amurka, inda akwai ɗaliban Najeriya sama da 13,000.
Daliban Najeriya a yanzu sun fara rae sha'awar zuwa wadannan kasashe, inda yawansu ya ragu daga 18,020 a 2013/14 zuwa 10,540 a 2017/18, raguwar kashi 41%, a cewar ICEF Monitor.
Ana biyan kudade masu yawa a wadannan kasashe, ga wahalar izinin zuwa, sabanin ita Belgium da za ka samu rarar kuɗi da ƙarancin tsarin biza mai wahala, da ingantattun hanyoyi zuwa aikin digiri na biyu da zama dan kasar.
Kamar yawancin baƙi, ɗaliban Najeriya suna biyan fiye da ninki uku na kuɗin da ɗaliban Birtaniya ko na ƙasashen EU suke biya.
Amma zai yi wahala 'yan Najeriya su samu ayyukan fararen fata a Birtaniya, har ma fiye da haka a wurare kamar Belgium inda harshe ke bayar da su.
Yaren Flemish, Faransanci da Jamusanci harsunan hukuma ne na Belgium kuma galibin ma'aikata suna son wadanda za su iya magana da aƙalla biyu daga cikinsu.
Kamar yawancin sauran ɗaliban Najeriya, Ms Osunkoya ƙwararriya ta fuskar magana da Ingilishi, ko da yake tana dan jin Flemish ma.
Ta ce "Ko da kuna da biza bayan karatun za ku yi gasa don neman aiki tare da mazauna yankin da suka fi ku yare," in ji ta.
Wasu ɗaliban kuma suna korafin nuna wariyar launin fata, yayin da wasu ke cewa sun ƙware sosai amma duk da haka ba su da ƙwarewar aiki.
A makon da ya gabata, Belgium ta sake fasalin manufofin shige da fice don ba wa ɗalibai damar ci gaba da zama har zuwa shekara guda a kan bizar wucin gadi don neman aiki.
Amma Foluwakemi ta ce ba za ta ɗauki wannan zaɓin ba, tunda da zarar ta yi rijista, ba za ta iya komawa makaranta don ƙarin digiri ba idan ba ta sami aiki ba.