Afghanistan: Abin da ya sa Taliban ke samun nasarar mamaye ƙasar da gaggawa

Taliban fighters in the city of Ghazni, Afghanistan. Photo: 12 August 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kididdiga ta nuna cewa kungiyar Taliban na da mayakan da yawansu ya kai 60,000
    • Marubuci, Daga Jonathan Beale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Tsaro, BBC News
  • An wallafa

Yadda kungiyar Taliban ke ƙara samun galabar ƙwace ikon yankuna a Afghanistan cikin sauri ya zo wa mutane da dama da mamaki - manyan biranen yankunan na ta komawa hannunsu.

A bayyane yake cewa ƙara samun galabar na daga ɓangaren masu tayar da ƙayar bayan, yayin da gwamnatin Afghanistan ke ta fadi-tashin ganin ta riƙe ikon da take da shi.

A cikin wannan mako, wani rahoton bayanan sirri na Amurka da aka kwarmata ya ƙididdige cewa birnin Kabul ka iya fuskantar hari nan da makonni masu zuwa, kana gwamnati ka iya faɗuwa ƙasa warwas a cikin kawanaki 90.

Ta yaya lamarin ya rikiɗe da gaggawa haka?

Amurka da ƙawayenta na ƙungiyar tsaro ta Nato - da suka haɗa da Birtaniya - sun shafe shekara 20 suna horar da dakarun tsaron Afghanistan.

Janar-janar ɗin sojojin Amurka da Birtaniya da dama sun yi ikirarin samar da sojojin Afghanistan masu jarumta da hazaƙa da kuma jajircewa.

Amma kuma sun ce a yanzu da alamu tamkar ba su samu horon komai ba.

Ƙarfin Taliban

Ya kamata gwamnatin Afghanistan a ce har yanzu ita ke da samun galaba saboda ƙarfi da kuma yawan dakarun tsaron da take da su.

Adadin yawan dakarun tsaron Afghanistan ya kai fiye da 300,000, akalla a kan takarda.

Hakan ya haɗa da jami'an sojojin sama da na ƙasa da kuma ƴan sanda.

Afghan government soldiers in the western city of Herat, Afghanistan. Photo: July 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Rundunar sojin Afghanistan na da mummunan tarihin asarar jami'anta da dama, da kaurace wa aikin soji da kuma cin hanci da rashawa

Amma a zahiri kasar a ko da yaushe tana cikin faman cimma adadin da ya kamata na ɗaukar ayyukan soji.

Rundunonin soji da ta ƴan sandan Afghanistan na da mummunan tarihin asarar rayukan jami'ansu da dama, da cin hanci da rashawa da kuma ƙauracewa aikin soji - da kuma yadda wasu ɓata-garin kwamandojin ke karɓar albashin dakarun da babu su - wato "sojan gona".

Wannan sabon rahoto ne ga Majalisar Dokokin Amurka, Babban Sifeto na kasar Afghanistan (SIGAR) ya bayyana "babban abin damuwa game da mummunan tasirin cin hanci da rashawa …. da kuma babbar ayar tambaya game da ainihin adadin yawan dakarun''.

Jack Watling, na cibiyar Royal United Services ya ce ita kanta rundunar sojin Afghanistan ba ta san yawan adadin dakarun da take da su ba.

Ya kuma ƙara da cewa, akwai matsaloli game da ci gaba da alkinta kayan aiki da kuma nuna hali nagari.

Galibi a kan tura sojoji su gudanar da aiki a wuraren da ba su da alaƙar da ta shafi dangantaka ko ƙabila.

Wannan shi ne daya daga cikin dalilan da me yiwuwa suka saka wasu ke barin wuraren aikinsu da wuri ba tare da yin wani artabu ba.

Children in makeshift camps

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dubban mutane na zaune a rumfunan da aka kakkafa a bKabul bayan da suka tsere daga hare-haren Taliban

Yana da matuƙar wahala a kwatanta adadin yawan mayaƙan Taliban.

Kamar yadda Cibiyar Yaki da Ta'addanci ta Amurka da ke West Point ta bayyana, ƙididdiga ta nuna cewa ƙungiyar na da yawan mayaƙa 60,000.

Idan kuma aka hada da sauran ƙungiyoyin masu gwagwarmaya da makamai masu goya musu baya, wannan adadi zai iya kai wa 200,000.

Amma kuma Dakta Mike Martin, tsohon jami'in sojan Birtaniya da ya bi diddigin tarihin rikici a yankin Helmand a littafinsa mai suna 'An Intimate War', ya yi gargadi game da daukar Taliban a matsayin wata dunƙulalliyar kungiya daya kawai.

A maimakon haka ya ce "Taliban na gab da zama wata gamayyar kungiyoyi mai ƙarfin iko a kaikaice - kana mai yiwuwa na takaitaccen lokaci - kasancewa cikin alaƙa tare da juna.''

Ya yi nuni da cewa ita ma gwamnati Afghanistan na fama da matsaloli na nuna bangarancin yanki.

Yanayin sauyawar tarihin kasar Afghanistan na nuni da yadda iyalai, da kabilu, da su kan su jami'an gwamnati suka sauya halayya - galibi don su tabbatar da inganta ta su rayuwar.

Samun makamai

Har ila yau, ya kamata gwamnatin Afghanistan ta yi amfani da damar da take da ita a ɓangaren samu kuɗaɗen tallafi da kuma makamai.

Ta samu biliyoyin daloli na biyan albashin sojojinta da kuma kayan aiki - akasari daga Amurka.

A rahotonta na watan Yulin shekarar 2021, SIGAR ya ce an kashe fiye da dala biliyan 88 kwatankwacin fan biliyan 64 a kan harkokin tsaron Afghanistan.

Amma kuma ya ƙara da yin hasashen cewa: "Batun ko an kashe kudin a kan hanyoyin da suka dace wani abu ne da manuniya za ta nuna daga sakamakon fadan da yanzu haka aka gwabzawa."

Ya kamata rundunar sojin saman Afghanistan ta yi mata mummunan lahani a fagen yaƙin.

Amma kuma, tana ci gaba da kai farmaki da jirgin yaƙinta na 211 (wata matsala da ke ƙara tsanani a yayin da ƙungiyar Taliban ke kokarin kai wa matuka jirgin hari kai tsaye).

Rundunar Sojin Amurka ta taɓa kai farmaki kan birane irin su Lashkar Gah, wanda ya fuskanci harin kungiyar Taliban.

Har yanzu babu tabbaci kan tsawon lokacin da Amurka za ta kai wannan dauki.

Internally displaced Afghans in a public park in Kabul, Afghanistan. Photo: 10 August 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dubban mutane ke zama a sansanonin wucin gadi a Kabul bayan tsere wa hare-haren ƴan Taliban

Galibi mayakan Taliban na dogara ne da kuɗaɗen shigar da take samu na daga cinikin magunguna, amma suna kuma samun tallafi daga waje - musamman kasar Pakistan.

Ba da jimawa ba ne kuma Taliban ta ƙwace makamai da sauran kayan aiki daga hannun dakarun tsaron Afghanistan - akasari wadanda Amurka ta ba su - da suka hada da manyan motocin yaki, da tabaron gani a cikin duhun dare, da bindigogin masu sarrafa kan su, da sauran manyan bindigogi.

1px transparent line

Afghanistan ta riga ta cika da makamai tun bayan mamayar sojojin Soviet, kana kungiyar Taliban ta nuna cewa ko da mafi lalaci zai iya samun galaba a kan dakarun da ke riƙe da manyan makamai na zamani.

Ka yi tunanin irin mummunan tasirin ababen fashewa a kan dakarun Amurka da Birtaniya.

Sanin lungu da saƙon yankuna da na daya daga cikin damar da suke da ita.

Mayar da hankali a arewaci da yammaci

Duk da irin yanayin kungiyar ta Taliban, har yanzu wasun a ganin alamun an tanadi kyakkyawan tsari a irin nasarorin kutsawar da suka samu a baya-bayan nan.

Ben Barry, tsohon babban jami'in sojin Birtaniya kuma a yanzu babban jami'i a Cibiyar Koyon Dabarun Yaki, ya yi nuni da cewa samun nasarar kungiyar Taliban ka iya zama wata dama ce da suka yi amfani da ita.

Amma ya kara da cewa: "Idan da za a ce in rubuta tsare-tsaren dabarun yaki, zan kasance mai tsananin tunanin yadda zan bullo da wani abu wanda ya fi wannan kyau."

Ya yi nuni da yadda mayakan Taliban suka mayar da hankulansu a arewaci da kuma yammaci, ba a yankunan kudanci da suka fi ƙarfi ba, a yayin da suka samu galabar da manyan biranen yankin na fadawa hannunsu.

Kungiyar ta Taliban ta kuma karbe ikon yankunan tsallaken kan iyakoki da shingayen bincike masu matukar muhimmanci, inda suke karɓe kudaden shiga na kwastan da gwamnati ke karɓa.

Sun kuma ƙara ƙaimi wajen kisan manyan jami'ai, da masu rajin kare hakkin bil adama, da manema labarai.

Sannu a hankali sun kakkaɓe wasu ƙananan nasarori da aka samu cikin shekaru 20.

Ta bangaren tsare-tsaren gwamnatin Afghanistan kuwa - yana da matukar wahala.

Alwashin sake karɓe duka yankunan da Taliban ta kwace na kara nuna alamun kamar da wuya.

Mista Barry ya ce da alamu akwai shirin riƙe manyan birane. An riga an aike da kwamandojin Afghanistan don kare yankunan Lashkar Gah da Helmand daga fadawa hannun Taliban.

Amma har na tsawon wane lokaci?

Dakarun Afghanistan na musamman ba su da yawa, su 10,000 ne, kuma ayyuka sun rincaɓe musu.

Da alamu kungiyar Taliban tana kuma samun galabar yaƙin farfaganda da kuma na labarai.

Mista Barry ya ce ƙarfin nausawar a fagen yaƙin ya ƙarfafa musu gwuiwa da kuma hadin kai.

A yayin da ita kuwa gwamnatin Afghanistan aka bar ta a baya tana faman sa-in-sa da kuma korar manyan jami'an sojinta.

Me zai faru daga ƙarshe?

Ko shakka babu al'amuran da ke tafiya sun nuna cewa gwamnatin Afghanistan na da raunin samun nasara.

Amma kuma Jack Watling na cibiyar RUSI yayin da hakan ke kara kasancewa sanyaya gwiwa ga rundunar sojin Afghanistan, "siyasa za ta iya shawo kan matsalar da ake ciki".

Muddin gwamnati za ta shawo kan shugabannin ƙabilu daban-daban, ya ce har yanzu akwai wata dama ta gyara dangantakar.

Wannan wani ra'ayi ne da Mike Martin ya jaddada, wanda ya yi nuni da dawowar tsohon jagoran mayaka Abdul Rashid Dostum zuwa yankin Mazar-i-Sharif a matsayin wani muhimmin lokaci.

Nan da dan lokaci ƙanƙani za a kawo ƙarshen yaƙin lokacin bazarar, a yayin da hunturu ke shirin kunno kai - wanda dai kawo cikas wa dakarun da ke kasa wajen fafatawa.

Har yanzu akwai yiwuwar nan da zuwa karshen shekara za a fuskanci sa-in-sa, kana gwamnatin Afghanistan za ta yi kokarin rike birnin Kabul da sauran manyan birane.

Amma a halin da ake ciki yanzu da alamu cewa yunkurin Amurka da Nato na samar da wanzuwar zaman lafiya da tsaro ga Afghanistan ya kasa cimma nasara kamar Soviet da ya gabace su.