Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ranar Giwa Ta Duniya: Yadda giwaye da mutane ke zaune a gari ɗaya a Indiya
- Marubuci, Daga Swaminathan Natarajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
A wasu shekaru da suka gabata, Tarsh Thekaekara ya hangi wani toron giwa maras haƙori yana zuwa wajensa a lokacin da yake wucewa ta wata hanya mai tsaunuka a Indiya.
"Babu hanyar da zan juya, saboda haka sai na dakatar da mota, na fito na zura a guje," kamar yadda Thekaekara ya faɗa wa BBC.
"In ka matsa kusa da giwaye za su kai maka hari sannan idan kana kan abin hawa za su hari abin hawan."
Sai kawai yaran da ke wucewa a gefen titi suka fara yi masa dariya saboda tsoron da ya ji.
"Suka ce kar ka ji tsoro, wannan toron giwar kamar saniya ce. Yana zuwa ne don ya sha ruwa kawai kuma ba zai yi maka komai ba."
Kuma sun yi gaskiya.
Cikin mamaki, toron ya share Thekaekara ya wuce kai tsaye zuwa wajen wani tafki abinsa.
Thekaekara wanda mai bincike ne kan giwaye da ke aiki da gandun dajin Gudalur na Indiya (inda ya haɗu da giwayen), ya yi tunanin cewa wannan lamari ba irin wanda aka saba gani kullum ba ne kuma ya zurfafa bincike.
Giwaye na shigowa gari... kuma su yi zamansu
Thekaekara ya fahimci cewa mazauna yankin sun saka wa wannan toron giwar suna Ganesan. (Sunan ya dace da na wata giwa da ake ɗauka abar bauta cikin tatsuniyoyin ƙabilar Hindu}.
A wurare da yawa na duniya, giwaye na yawan zuwa inda mutane ke zaune don neman abinci da ruwan sha.
A mafi yawan lokaci sukan koma daji bayan 'yan kwanaki. Amma a kudancin Indiya, akasarin giwayen daji kamar wannan, suna ta ƙoƙrin iya zama cikin mutane, hasali ma suna son shafe lokaci mmai tsawo a garuruwan da ke kusa da manyan dazuka.
Mutum fiye da 250,000 ne ke zaune a garin da maƙotan ƙauyukan. Dajin mai faɗin murabba'in 500, na ƙunshe da itatuwa kamar gahawa sannan akwai giwaye kusan 150.
Wasu daga cikin giwayen sun saba da zaman cikin gari ta yadda ko da an kunna wutar wasa a yayin bukukuwa ko an buga ganga ba sa far wa mutane ko kuma kai hari.
"Wannan ya saɓa da duk abubuwan da na sani," a cewar Thekaekara. "Bai nuna alamar wani faɗa ba."
Shan ruwa daga tankin ruwa da satar abinci amma ban da kai wa mutane hari
A mastayinsa na jagoran masu bainciken giwaye na Gudalur Elephant Monitoring Project, Thekaekara ya yanke shawarar bincika dukkan giwayen da ke yankin, abin da ya sa ya ɓige da samun giwayen daji 90, ciki har da wasu biyar da ke zaune a cikin al'umma.
Binciken ya gano akasarin waɗnda ke cikin garin dattijan giwaye ne waɗanda suka fahimci yadda za su dinga samun abinci da ruwansu.
"Mun bibiyi Ganesan tsawon shekara uku. Bai taɓa shiga daji ba. A cikin mutane yake shafe rayuwarsa baki ɗaya.
"Kusan ko yaushe yana barci a gefen titi. Yakan tura hancinsa cikin manyan motoci har ma ya fasa gilashi wani lokacin. Haka nan ya taɓa kai wa masu babur mai ƙfa uku hari."
Kazalika, Ganesan ya san yadda yake ɗebo ruwa daga tankuna na gidajen mutane.
Wani lokacin yakan farfasa kayayyakin aiki a unguwar, ya haddasa cunkoson ababen hawa, ya ƙwace kayan marmari daga wajen masu talla amma bai taɓa cutar da kowa ba.
Wani bidiyo ya karaɗe shafukan zumunta na wani toro da yake ƙwace dafaffiyar kaza daga hannun wani mutum, kuma ya bai wa mutane mamaki.
Amma a matsayinsa na mai binciken giwaye, Thekaekara ya iya gano abin da ke faruwa ke cikin sauƙi.
"Ai da ma giwaye na son shinkafa kuma gishiri. Amma kazar tsautsayi ne," a cewarsa. Giwaye dabbobi ne da ke cin itatuwa.
Giwayen daji kan shafe mafi yawan lokacinsu a neman abinci da ruwa. Thekaekara ya ce giwayen da ke zaune a garuruwa kan samu abincinsu cikin ƙasa da awa biyu.
Ya kamata su ma mutane su saba
Tsawon lokaci, su ma mazauna ƙuyukan sun tabbatar cewa idan suna so su ci gaba da neman abincinsu tare da giwayen, akwai buƙatar su saba kamar yadda giwayen suka yi - ba tare da sun hari kowa ba.
Bharadan na ɗaya daga cikin giwayen da suka fi girma da ke zaune a garuruwa. Yana yawan zuwa wani ƙaramin wurin sayar da abinci a garin Thorapalli, inda suke ajiye masa ragowar abinci don ya ci.
Ƙin tafiya
Masu kula da dajin yankin sun yi fargabar cewa wasu za su iya mutuwa idan giwayen suka kai musu hari. Saboda hakaa ne suka yanke shawarar mayar da Rivaldo daji.
Rivaldo ya fara zuwa garin Ooty "bayan wani mutum ya fara ajiye wa giwayen abinci," a cewar Thekaekara.
Tsawon shekaru, mutanen da giwayen sun daina jin tsoron juna. Masu kula da dajin sai suka fara ciyar da giwayen, suka mayar da shi wajen yawon buɗe ido.
Toron kan koma cikin gari mai nisan kilomita 40 a cikin aa 24 bayan sun mayar da shi daji bisa fargabar zai iya kai wa mutanen garin hari.
Thekaekara ya ce ya zauna a garin tsawon kusan shekara 15, kuma yana cikin na farko da suka saba da zama da dabbobin.
Ƙaruwar giwayen da ke zama a cikin jama'a
Indiya na da giwaye kusan 27,000, da yawa daga cikinsu na zaune a dazukan da ba a killace ba.
Thekaekara ya yi imanin cewa yadda dabbobin da kuma mutane ke zaune da juna ka iya taimakawa wajen tsawon rayuwa ga dabbobin.
"Ilimin nazarin rayuka na ganin cewa halittu na rayuwa ne daban-daban. Saboda haka, muna buƙatar mu karanci rayuwar kowane giwa domin sanin abubuwa game da shi. Kuma an fara yin hakan."