Gano amsoshin dalilin matsalar ruwan da duniya ke fuskanta

    • Marubuci, Daga Natalie Lisbona
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter
  • An wallafa

Babu tantama, ruwa abu ne mai matukar muhimmanci a ban kasa. Baya ga haka, shi ne ya mamaye kusan kashi 70 na duniya, amma duk da haka ana fuskantar karancinsa.

Sauyin yanayi, da tashin hankali, da yawan al'umma na daga cikin abin da ya janyo ake cikin tsaka mai wuyar karancin ruwa a wasu sassan duniya. Hakan na nufin mutum biliyan biyu, wato kwatar al'ummar duniya ba sa samun tsaftataccen ruwan sha.

Ya yin da al'ummar duniya ke dosar biliyan takwas, an fara maida hankali kan samar da kimiyyar da za ta taimaka wajen shawo kan matsalar kafin lokaci ya kure.

Daya daga cikn masu gabatar da mafitar shi ne Michael Mirilashvili, shugaban kamfanin Watergen, mai mazauni a Isra'ila, wanda ke amfani da fasahar iska zuwa ruwa, domin samar da ruwan sha ga al'ummar yankunan da ke da wuyar isa, da kuma sauyin yanayi da tashe-tashen hankula suka daidaita.

'Hakkin dan adam'

"Samun ruwa na daga cikin hakkokin dan adam, amma duk da hka miliyoyin mutane ba sa samun ruwan nan," inji shi lokacin hira da BBC.

Fitar da ruwa daga iska tamkar kirkira ce ta kimiyya, amma fasahar sassauka ce fiye da yadda ake tunani.

Sararin duniya na dauke da tan biliyan 13 na ruwa, don haka kamfanin Watergen na amfani da wasu injinan da suke tace ruwan daga iskar da aka zuko.

Ya ce ana amfani da shi yadda ya dace, kuma kimiyyar da suke amfani da ita kamfanoni za su amfana da ita wajen samar da maslaha kan matsalar karancin ruwa.

"Babbar nasara ce amfani da ruwan da ke cikin iska, ba a bukatar yin wani bututun da zai kai ruwa, don haka babu damuwa kan manyan bututan karfe, ko tsaftace ruwan da ya gurbata da kura ko na cikin roba maras tsafta."

Daya daga cikin abin da ya ke janyo tarnaki shi ne gurbatacciyar iska, wadda ta zama barazana da kowa ke nuna damuwa akan ta a biranen kasashen duniya.

Misali a Birtaniya, wani bincike da kwalejin Imperial da ke birnin Landan, sun gano gubar dalma wadda ke cutar da dan adam, ta na nan makare a cikin iskar a shekarar 2021, duk da cewa an haramta hakan a shekarar 1999.

Duk da haka, wannna ba zai zama damuwa ba. Binciken da masana kimiyya na jami'ar Tel Aviv da ke Isra'ila , sun gano za a iya tace ruwan sha daga cikin iska, kuma hukumar lafiya ta duniya ta amince da hakan. Ta wata fuskar za a iya sarrafa ruwa mai tsafta daga gurbatacciyar iska.

Babban injin Watergen, ya na iya samar da lita 6,000 a kowacce rana.

An dade ana kai ruwan asibitocin da ke zirin Gaza, da kauyukan da ke tsakiyar Afurka, yankunan da mutane sai sun yi tafiyar sa'o'i kafin su samu ruwa.

Haka kuma an taimakawa gwamnatin Australia, wajen sanya su a robobi da rabawa wadanda mummunar gobarar daji ta raba da muhallansu a farkon shekarar nan da mutane 34 suka mutu, tare da lalata gidaje 3,500.

"Ba wai kawai ceto rayuwar mutane ba, a'a ana son inganta rayuwar miliyoyin mutane," inji Mista Mirilashvili. "Ko a kasashen da suka ci gaba, wasu mutanen ba sa samun tsaftataccen ruwan sha, wanda hakan na janyo wa lafiyarsu illa da koma baya a fannin noma."

Gurabacewa mai hadari

Kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana, mutane fiye da biliyan biyu ne bas a samun ruwa sai wanada ya gurbata da ba-haya.

Kurba daya kadai ta isa ta jefa su cikin hadarin kamuwa da cututtuka kamar kwalara da typhoid, kana ta kididdige cewa mutane kusan 500,0000 ne ke mutuwa a ko wace shekara sakamakon haka.

Idan ana maganar samu tsaftataccen ruwa, ana samu a tekunanmu. Kankarar tekun na kunshe da ruwa mafi tsafta a duniya tun a dubban shekaru da suka gabata.

Manyan guma-guman kankarar ka iya zama babbar barazana ga jiragen ruwa tare da lalata yanayin rayuwar halaittun ruwa, da kuma tara ruwa mai yawan gaske da zarar sun narke.

An fara aikin tattara su saboda samun riba a kasar Canada, inda ya zama babban kasuwanci a bakin tekun kasar. Amma wannan sana'a ta kara fadada zuwa wasu bangarori na duniya.

Wani dan kasuwa kuma masana kan abubuwan da suka shafi muhalli Abdulla Al-Shehi, na aiki da hukumar ayyukan kan kankarar teku a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Karancin ruwa na haifar da mummunar barazana a kasar, yayin da sauyin yanayi ke zuwa tare da dumama kan irin zafin da aka riga ake fuskanta a wurare masu zafi a duniya.

"Gungumen madaidaiciyar kankara daya ka iya samar wa da miliyoyin mutane ruwa na tsawon shekaru 3 zuwa 5,'' ya yi ikirari.

"Don haka me zai hana mu yi amfani da wannan dama kan alfarmar da muka samu daga Allah? Ina fatan ganin kawo guma-guman kankarar zuwa tsakiyar yankin kasashen Larabawa.''

Amma kuma lamarin na tattare da hadari. Saboda girman kankarar ka iya yin tuntsurewa a yayin tafiya, tare da haddasa mummunan hadari.

Har ila yau dole sai an lullube su a wasu abubuwa da masu karfi wadanda za su rage adadin narkewarsu a yayin tafiyar. Don haka, ba abin mamaki bane idan aka ce aikin zai ci makudan kudade.

Ayyukan gungumen kankara na Hadaddiyar Daular Larabawa zai fara ne ta hanyar harhada kananan duwatsun kankarar tare da kai su zuwa birnin Perth a Yammacin Australia ko Cape Town a kasar Afirka Ta Kudu.

"Akwai yiwuwar aikin zai lashe daga dala miliyan sittin zuwa tamanin ($60 zuwa 80) kwatankwacin fan miliyan arba'in da biyu zuwa hamsin da bakwai (£42 zuwa 57).

"Kana daukacin aikin da alamu zai ci dala miliyan dari dari da hamsin zuwa dari biyu ($150-200m)," in ji Mista Al-Shehi.

Shin teku ne amsa?

Yayin da ake cigaba da aikin tattarawa da samar da guma-guman kankarar, akwai sauran hanyoyin amfani da tekunan duniya.

A shekarun baya, an gudanar da aikin tace gishiri daga ruwan teku da ake kira 'desalinisation' - ta hanyar amfani da zafi.

Yanzu haka, ana amfani da irin wannan hanya ta 'desalinisation' wajen amfani da ruwan tekun.

Wasu gwamnatocin na da matatun tace gishiri daga ruwan tekun da ke samar wa da yawan 'alummarsu ruwan sha, yayin da wasu ke dogara da kamfanoni masu zaman kan su wajen gudanarwa.

Babbar matata mai samar da ruwa ta Dupont, da ke da mazauni a birnin Delaware, na tace galan miliyan 25 na Amurka (lita miliyan 94) na ruwa a fadin duniya.

"Aikin ya kan bai wa ruwa damar wucewa ta cikin matacin yayin da yake rabuwa da gishirin.

A sakamakon haka, an samar da abubuwa biyu, daya ruwan sha, yayin da kuma dayan ruwa mai kunshe da gishiri mai yawa,'' in ji Verónica García Molina, jagorar bangaren kasuwancin duniya na matatar ruwan ta DuPont Water Solutions.

"Akan mayar da ruwan da ke kunshe da gishirin kai tsaye cikin tekun, amma saboda wasu hanyoyi masu inganci da aka bi babu wani mummunan tasiri a kan tekun.''

Duk da cewa matatun ruwan na zamani tasirinsu kadan ne ko kuma babu a kan tekun, ba za a iya bayyana hakan ba ga tsofaffin matatun da har yanzu ke amfani da hanyoyin da ba na zamanai sosai ba wajen tace gishiri daga ruwan tekun.

Wadannan su ne sake mayar da ruwan gishirin cikin teku wanda ka iya haifar da barazana ga rayuwar halittun ruwa wajen rage ingancin iskar shaka ta oxygen tare da akara yawan adadin gishirin.

Akasarin wadannan tsofaffin matatun na Yankin Gabas Ta Tsakiya, inda kasha hamsin da biyar bisa dari (55%) na aikin sake mayar ta tataccen ruwan gishiri zuwa cikin tekuan

Daya babbar sukar da ake yi wa aikin tace gishirin ruwan tekun na 'desalination' itace, yana amfani da makamashi mai yawa wajen aikin tace ruwan tekun, akasari wanda akan yi ta hanyar amfani da gurbataccen makamashi.

Amma kuma, Miss Molina ta ce cigaban fasahar zamani da aka samu a shekarun baya-bayan nan ta haifar da hanya mafi inganci ajen shawo kan matsalar karancin ruwan sha a fadin duniya.

"Makamashin da ake bukata wajen aikin sarrafa ruwan tekun ya ragu fiye da sau uku a cikin shekaru da dama da suka gabata, kuma a yanzu akan yi amfani da sau hudu zuwa biyar na makamashin ko kuma kasa da haka fiye da tsohuwar hanyar amfani da zafin,'' ta kara bayyanawa.

Amma kuma, babu tabbaci kan ko wadannan hanyoyin sun wadata wajen warware matsalar.

A yayin da hanyoyin samar da ruwan na duniya ke kara yin karanci, masana kimiyya na ta fafutukar ganin sun bullo da sauran amsoshin cewa suna da karanci ko kuma rashin tasiri a kan tsarin yanayin rayuwar halittun ruwa.an.