Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mahaucin da ya koma zanen shanu a Ghana
- Marubuci, Daga Andy Jones
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, London
- An wallafa
Kojo Marfi mahauci ne da a yanzu ya zama mai zane, wanda kuma ya jajirce don bayyana wa duniya muhimmancin shanu.
"Shanu ne ke kafa ci-gaba," in ji Marfo. "A Ghana muna amfani da su wajen noma kuma idan kana da dabbobin biyu zuwa uku, kana iya samun kyakkyawar mace ka aura. A wasu sassan Indiya, shanu kamar abin bauta ne."
Ya fara martaba shanu ne tun yana yaro a wani kauye a Ghana, inda ya girma tare da mahaifiyarsa da kakarsa, kuma abin ya ci gaba bayan da ya koma birnin New York don yin aiki inda ya afka sana'ar fawa.
"Ba ni da wani buri, kuma babu abin da na sani dangane da nama ko fawa," a cewar mutumin mai shekara 41.
"A kan bango akwai zane-zanen sassan jikin dabbobin da aka yanka kuma da su nake amfani wajen yanka wa mutane nama. Ko a lokacin, shugabana na wurin aiki ya sha kama ni ina hira da kwastomomi."
Duk da cewa a baya ya taɓa sayar da nama, amma zane-zanensa masu alaƙa da shanu a yanzu suna samar masa da kudi da yawansu ya rubanya sau uku na abin da yake samu a baya.
A yanzu, ana amfani da zane-zanen Marfo a kan dan kwalayen kayan ƙawa na Aspinal of London.
Wasu maudu'in da ke faranta wa mai zanen rai su ne darajar zama mace da darajar kasancewa mahaifi marar miji ko mata da kyawun mele.
Daga farko idan aka ga ayyukansa suna nuna al'adun nahiyar Afrika - ya girma a garin Kwahu mai tsaunuka, kusan tafiyar awa hudu daga Accra - amma ko wane zane wani bangare ne na nahiyoyi daban-daban.
Marfo ya tuna rayuwarsa ta ƙuruciya a dakin karatun unguwarsu inda ya ke kallon zane-zanen Picasso da kuma kallon masu aikin hannu a Accra suna sayar wa masu yawon bude ido kayansu.
"Na yi tunanin kamar ya fi dacewa in zama likita ko akanta, amma sai in je bakin rafin in debi laka sannan in debi ƴaƴan itatuwa in niƙe su su zama kamar tawada.
"Sai in shafa man shafawa na basilin a kan takarda don ta zama shara-shara sai in riƙa bin zane-zanen da ke jikin littafai da mujallu a kai. Amma sai da na bar Ghana ne na fara mayar da hankali kan zane na.
Daga baya ya bar New York ya koma Burtaniya, inda ya fara aiki a hsagon kayan masarufi na gwoggonsa.
A shekarun 2000 me Marfo ya watsar da zane amma ya koma daga baya.
"Na yi ƙoƙarin nuna martabar iyaye masu 'ya'ya da ba su da miji ko mata," a cewarsa.
"A ƙauyuka, mata sun fi kowa mayar da hankali kuma mata ne suka raine ni. Wata mai fafutukar kare hakkin mata ta taba gaya min cewa ko yaushe maza ne ke jan ragama, ko yaushe mata na fuskantar mayuwacin hali. Amma mata a inda na fito, mata ne ke jan ragama."
Haka kuma, zanensa ya fara tabo batun kyau - inda yake zana mutane da mele a fuskarsu.
Marfo ya fara sayar da zanensa a intanet, sannan ya shigar da shi wata gasa mai suna Isolation Mastered.
Kyawunsu ya ja hankalin alkalan gasar - ciki har da babban masanin zane-zanen tarihi nan David Bellingham da mai sha'awar zane Gavin Rossdale.
Nan da nan aka fara sayen zane-zanen Marfo.
"Ban sani ba ko don zane-zanena sun kunshi fafutukar kare hakkin bakar fata ta Black Lives Matter ne," a cewar Marfo.
"Masu saye na fadar abu biyu: Zane-zanena sun fita daban - su kan ce 'babu mai yin abin da kake yi,' - kuma suna son yadda nake alakanta labarin da wani abu da ya shafe ni."
Amma Marfo, yaron da aka haifa a cikin tsaunuka, bai damu da kudin ba. So yake kawai ya samu ci gaba.
"A Kwahu, kasar ba ta da kyawun yin noma don haka sai mutum ya jajirce wurin neman yadda zai yi.
"A Ghana, idan daga Kwahu ya fito ana kallonka a matsayin mai son kudi amma ni an yi min tarbiyyar da a duk halin da na tsinci kaina ina gode wa Allah da dan abin da nake da shi."
Kuma bai cire tsammanin komawa aikin fawa ba nan gaba.
"Har yanzu aikin fawa na burge ni, zan so in kara koyon aikin sosai."
Ana nuna zanen Kojo Marfo na Dreaming of identity a JD Malat Gallery a birnin London.