Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotuna masu ƙayatarwa da mata ke ɗauka a Somalia duk da tsangwamarsu da ake yi
An saba ganin hotunan tayar da zaune tsaye da tashe-tashen hankula da suka fito daga kasar Somalia, amma bikin baje kolin daukar hoto da aka yi a birnin Mogadishu, ya sanya ɗan-ba, ba wai kawai na kalubalantar yadda ake kallon hakan ba, har da wadanda ke daukar hoton kamar yadda za ku ji da gani a rahoton wakiyar BBC Mary Harper.
Makale a jikin farin bangon farfajiyar Otal din, wasu hotuna ne masu kyau da ƙayatarwa da wasu mata biyu masu daukar hoto suka dauka.
''Yana da muhimmanci mata su mamaye wuraren taruwar jama'a,'' daya daga cikin masu daukar hoton Fardowsa Hussein ta bayyana.
Ta ce idan tana daukar hoto ko bidiyo a kan tituna, maza kan yi mata tsawa, tare da fada mata ta koma gida maimakon wulakanta kanta a bainar jama'a.
''Ina son a gane ƙarara cewa ba wani abu ba ne don mata irina sun fita daukar hoto ko bidiyo, ba tare da sun ji tsoron yi musu wulaƙanci ba.''
Bikin baje kolin da a kai wa lakabi da suna Still Life, Sagal Ali, daraktar gidauniyar wasan kwaikwayo ta Somalia SAF ce ta kaddamar a watan Satumbar 2020.
Ta ce a kasar Somalia an dauki sana'ar daukar hoto a matsayin ta maza, musamman idan ana magana a kan daukar hotuna a kan tituna. Ba a cika ganin mata na yin ayyukan da suka shafi rayuwar yau da kullum musamman a waje, ba a cikin gida ba.
''Sama da shekara 30 ke nan da al'ada da kirkira suka mutu a kasar Somalia,'' in ji ta. ''Manufar gidauniyar Saf, ita ce farfado da al'adun da bai wa mutane damar shakar iska.''
Tana kuma son sauya yadda mutane ke kallon sana'ar daukar hoto, a wannan bikin baje kolin take fatan kalubalen da mata ke fuskanta a fannin za su kau.
''Lamuran mata na daukar hankalina, yadda suke gudanar da al'amura a hotunan da na dauka. Ba na jin maza za su iya daukar hotunan kamar haka,'' in ji Ali.
"Na dauki wannan hoton ne a kudu maso gabashin garin Hudur," in ji Hussein.
"Kiwon rakuma abu ne mai matukar kyau da ban sha'awa. Alhakin kai su kiwo a daji ya rataya wuyan maza matasa. Yara maza biyu ne suke kula da kusan rakuma 50, su kan yi kiwon kwanaki biyar zuwa shida ba tare da shan ruwa ba.
"'Yan Somalia sun ce wannan shi ne aiki mafi wahala da maza ke yi, amma shi ne mai tagomashi mafi tsoka a al'adarmu.''
"Ana cikin keke mai kafa uku a titin birnin Mogadishu, kawai sai na gano wadannan 'yan yaran mata biyu," daya daga cikin mata masu daukar hoton mai suna, Hana Mire.
"Abu ne da ban taba tsammanin gani ba. Sai na yi tsalle na sauko daga cikin babur, yaran ba su san abin da zan yi ba sai gani sukai na fara daukar hoto. Bayan na gama na nuna musu, kuma sun yi matukar yabawa.
Wannan hoton wata mace ce da Hussein ta dauka a cikin teku.
''Akwai wani abu mai ban sha'awa game da matar, duk da irin hayaniyar da ke kusa da ita.
Hussein ta ce ganin ita ma tana sanye da hijabi shi ya bai wa matar kwarin gwiwar bari ta dauki hoton a wannan lokacin.
Ta kuma dauki hoton wasu mata biyu da ke wasa da ruwa a gabar kogi, inda suke dibar ruwan da hannu suna watsawa a kafafunsu.
"Awais yana kaunar hoton nan," in ji Mire.
"Yana da kirki. Ya shaida min wannan ne hoto na farko da aka taba daukar sa. Ya dade yana fuskantar tsangwama da nuna wariya daban-daban."
Mire na ganin yana da muhimmanci a nuna bambance-bambancen da ke tsakanin al'umar Somalia.
"Lokuta da dama, mutane na tunanin 'yan Somalia kabila daya ne, kuma suna magana da harshe guda. Wannan ba gaskiya ba ne."
An dauki wannan hoton a ranar Sallar Layya, a daya daga cikin tsofaffin masallatan da ke yankin Hamar Weyne, daya daga cikin tsofaffin gundumomin Mogadishu.
"Na dauki hoton lokacin da matar ta mike tsaye, ya yin da sauran mutane ke durkushe suna addu'a, fanka na kada hijabin da take sanye da shi kamar wani jirgin ruwa," in ji Mire.
Mire ta kuma dauki wannan hoton a Hamar Weyne, a wani titi da mutane ke kwalliyar sanya tufafin Larabawa.
"Wannan daya ne daga cikin hotunan da nake kauna da na dauka a Mogadishu," in ji ta.
"Na ga wannan mutumin yana tafiya a hanya, sai na ji ina ƙaunar tufafin da ya ke sanye da shi. Sai na tambaye shi ko zai amince na dauki hotonsa, ya ce me zai hana."
Mire na ƙaunar wannan hoton.
"Na kai ziyara birnin Shangani mai tarihi, duk da cewa ina iya ganin yadda yaƙi ya daidaita gine-gine, hakan ya tuna min da iyayena, da rayuwa mai dadin da suka yi a kyakkyawan birnin.''
Ta yi bayanin yadda ta yi shiru a lokacin da ta ke tunanin iyayenta da rayuwarsu, kawai sai ta hango yaron yana kallon teku.
"Na dauka ni ce, saboda ya tuna min da tawa ƙuruciyar."
Masu daukar hoton na ganin mutanen yammacin duniya sun dade da mamaye labaran da suka shafi Somalia tare da yada shi a matsayin kasar da ta fi hatsari a duniya, wadda yaki ya daidaita, da fari da cututtuka.
Mata masu daukar hoton, sun ce suna son karɓe ragamar labaran da suka shafi kasarsu, don bayar da labarin ainahin yadda rayuwa take a kasar.