Abin da ya sa ake samun ƙaruwar mata masu kashe kansu a Japan

    • Marubuci, Daga Rupert Wingfield-Hayes
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Tokyo
  • An wallafa

Kasar Japan tana bayar da rahoto game da kisan kai cikin sauri kuma mafi sahihanci fiye da dukkan kasashen duniya. Ba kamar sauran kasashe ba, a nan ana tattara bayanai kan kisan kai duk watan duniya. A lokacin annobar korona, lamarin ya yi kamari sosai.

A shekarar 2020, a karon farko a cikin shekara 11, alkaluman masu kashe kansu sun yi tashin da ba a taba ganin irinsa ba a Japan. Wani abin mamaki kuma shi ne, yayin da mazan da ke kashe kansu suka ragu, matan da ke kashe kansu sun karu da kusan kashi 15 cikin dari.

A wata daya kawai, watan Okotoba, matan da ke kashe kansu sun karu da kashi 70 a Japan idan aka kwatanta da watan Oktoban da ya gabace shi.

Mene ne yake faruwa? Me ya sa cutar korona take taka rawa wajen yawan matan da ke kashe kansu fiye da maza?

Gargadi: Wasu ba za su ji dadin karanta wani bangare na wannan labari ba.

Gaanawa da matashiyar da ta yi yunkurin kashe kanta sau da dama abin tayar da hankali ne. Hakan ya sa na kara girmama mutanen da ke aiki domin ganin sun hana masu son kashe kansu yin hakan.

Ina tafiya a kan wata hanya da ke tsakiyar birnin Yokohama, inda ake da wata kungiya da ke fafutikar hana mutane kashe kansu mai suna Bond Project.

Na gana da wata matashiya mai shekara 16. Ta yi kama da wacce ta ba motsi.

Ba tare da ta yi motsi sosai ba, ta gaya min labarinta. Ta ce lamarin ya fara ne lokacin tana 'yar shekara 15 a duniya. Babban yayanta ne ya soma cin zarafinta ta hanyar jima'i. Daga nan ne ta tsere daga gida, amma hakan bai kawo karshen matsalar ba.

Don haka take ganin kashe kanta ne kawai abin da zai cire kuncin da ke ranta.

Ta shaida mini cewa: "Daga irin wannan lokaci a bara zuwa yanzu na je asibiti sau da dama." "Na yi yunkurin kashe kaina sau da dama, amma ban yi nasara ba, don haka na yanke shawarar daina yunkurin kashe kaina."

Ta fasa kashe kanta ne saboda wa'azin da kungiyar Bond Project ta rika yi mata. Sun samar mata makwanci mai kyau da tsaro, sannan suka soma ba ta shawarwari.

Jun Tachibana ita ce ta kafa kungiyar Bond Project. Mace ce mai karfin rai da da kwarin gwiwa mai kimanin shekara 40 da doriya.

"Idan 'yan mata suka fada cikin mawuyacin hali, ba su san abin da za su iya ba," in ji ta. "Muna nan inda muke shirye mu ji abubuwan da ke damunsu, mu gaya musu cewa - muna tare da ku."

Ms Tachibana ta ce da alama cutar Covid ta ta'azzara halin da masu niyyar kashe kansu suke ciki. Ta bayyana irin yadda ma'aikatanta suka rika amsa wayoyin wadanda ke cikin mawuyacin hali a watannin baya bayan nan.

"Muna samun korafi daban-daban game da masu niyyar kashe kansu wadanda ke cewa 'ina son kashe kaina' da kuma 'Ban san dalilin rayuwata ba'," in ji ta. "Sukan ce 'Rayuwa ta yi mana kunci, ba mu ga tsuntsun ba mu ga tarko, muna son mutuwa'."

Cutar korona ta ta'azzara halin da matan da ake cin zarafinsu ta hanyar jima'i suke ciki.

"Wata yarinya da na yi magana da ita kwanakin baya ta gaya mini cewa mahafinta ne yake lalata da ita," a cewar Ms Tachibana. "Mahaifinta ba ya zuwa aiki saboda kullen korona shi ya sa kullum yake zaune a gida, don haka ba ta da mafita daga sharrinsa."

Yanayin 'da ba a saba shiga ciki ba'

Idan ka yi duba kan matsalokin da Japan ta fada a ciki a baya, irin su matsalar da bankuna suka shiga a 2008 ko kuma matsalar rushewar kasuwar hannun jarin kasar da kuma kasuwar gidaje ta farkon shekarun 1990, galibin wadanda suka fi jin jiki su ne masu matsakaicin karfi. A wadancan lokacin, an samun kari sosai na mazan da ke kashe kansu.

Amma akwai bamnacin game da annobar korona, domin kuwa tana shafar matasa, musamman mata. Dalilin hakan yana da sarkakiya.

A baya Japan ta kasance kasar da aka fi samun masu kashe kansu a tsakanin kasashen da suka ci gaba. Sai dai a cikin shekaru goma da suka wuce, kasar ta yi nasarar rage yawan masu kashe kansu inda take a mataki na uku.

Farfesa Michiko Ueda na daya daga cikin masana 'yan kasar Japan da ke kan gaba wajen bincike kan dalilan da ke sa mutane kashe kansu. Ta shaida mini yadda ta kadu da ganin yawaitar masu kashe kanu a watannin baya bayan nan.

"Wannan yanayi na yadda mata suke kashe kansu abu ne da ba a saba da shi ba matuka," in ji ta.

"Ban taba ganin irin wannan yanayi na karuwar mata da ke kashe kansu ba a shekarun da na kwashe ina gudanar da bincike kan wannan batu. Abin da ya sa cutar korona ta taka rawa wajen matan da ke kashe kansu shi ne, galibin masana'antun da aka rufe sakamakon dokar kulle sun shafi mata ne, irin su ma'aikatun yawon bude ido, da dillanci da kuma masana'antun sayar da abinci."

Watan da ya fi tayar da hankalin jama'a game da matan da ke kashe kansu shi ne na Oktoban da ta gabata, inda mata 879 suka kashe kansu. Hakan ya fi kashi 70 cikin dari na matan da suka kashe kansu a watan Oktoba na 2019.

Kanun labaran da jaridun kasar suka wallafa ne ya ja hankalin 'yan kasar. Wasu sun kwatanta adadin maza da matan da suka kashe kansu a Okotoba (2,199) da kuma yawan mutanen da suka mutu sanadin korona a Japan daga lokacin da ta barke zuwa watan na Oktoba (2,087).

Wani abu na ba kasafai ba ya faru a kusa da lokacin.

Ranar 27 ga watan Satumba na shekarar da ta wuce, an gano gawar fitacciyar tauraruwar fina-finai Yuko Takeuchi a gidanta. Daga bisani aka gano cewa kashe kanta ta yi.

Yasuyuki Shimizu wani tshon dan jarida ne da ke aiki a wata kungiya mai zaman kanta da ke aikin hana mutane kashe kansu a Japan.

"Daga ranar da aka bayar da rahoton mutuwar tauraruwar fina-finan, an samu karuwar masu kashe kansu kuma sai da aka kwana 10 ba tare da adadin ya ragu ba," in ji shi.

"Alkaluman da muka gani sun nuna cewa daga ranar 27 ga watan Satumba lokacin da tauraruwar ta kashe kanta, an samu karuwar mata 207 da suka kashe kansu cikin kwana 10 da suka biyo baya."

Wasu masana sun yarda cewa akwai dangantaka tsakanin kisan da tauraruwar ta yi wa kanta da kuma karuwar matan da ke kashe kansu.

Tasirin kisan da taurari ke yi wa kansu

Wannan lamari bai shafi Japan ita kadai ba, shi ya sa ma bayar da rahoto game da kisan kai yake da matukar wahala. Jim kadan bayan kisan kan da tauraruwar ta yi wa kanta, an rika tattauna batun a kafafen watsa labarai da shafukan sada zumuta, lamarin da ke da tasiri kan masu rauni a tsakanin mutane.

Mai Suganuma na cikin masu bincike kan mutanen da ke kashe kansu. Ita kanta lamarin ya shafe ta. Lkacin da take karamar yarinya, mahaofonta ya kashe kansa. Yanzu tana taimaka wa iyalan mutanen da suka kashe kansu.

A yayin da cutar korona ba ta barin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar su yi alhinin wadanda suka rasa, haka kuma tana ta'azzara yanayin da iyalin mutanen da suka kashe kansu suka fada a ciki.

"Idan na yi magana da mutanen da lamarin ya shafa, abin da suke cewa shi ne suna dora alhakin rashin iya ceto 'yan uwansu daga wannan hali a kansu," in ji Mai Suganuma. "Ni kaina ina dora alhakin rashin iya ceto rauwar mahaifina akaina.

Japan na cikin zagaye na uku na cutar korona, kuma gwamnati ta sanya dokar ta-baci karo na biyu. Watakila ta tsawaita dokar fiye da watan Fabrairu. Za a ci gaba da rufe karin gidajen abinci da otal-otal da gidajen sayar da barasa. Karin mutane za su rasa ayyukan yi.

Farfesa Ueda ta ce akwai karin tambaya. Ganin cewa hakan na faruwa ne a Japan, wacce ba ta sanya tsauraran dokokin kulle ba, sannan wadanda suka mutu sanadin korona ba su da yawa, mene ne yake faruwa a kasashen da cutar ta yi muni?