Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jam'iyyar APC: Yadda aka hana wasu manyan jiga-jiganta sabunta rijista a jihohinsu
Rikicin cikin gida a jam'iyyar APC mai mulki na ci gaba da ƙamari sanadiyyar sabunta rijistar ƴaƴan jam'iyyar da ke ci gaba da gudana a dukkanin jihohin ƙasar 36.
Wasu jiga-jigai a jam'iyyar daga yankunan daban-daban na kasar na zargin gwamnonin jihohinsu da shirya maƙarƙashiyar karkatarwa da kuma hana waɗanda ba sa ɗasawa da su sabunta katinsu na jam'iyyar.
Masu irin wannan ƙorafi sun fara kiran a soke aikin sabunta rijistar a wasu jihohi dungurungum, kowa ya huta.
Daga cikin irin waɗannan ƙusoshin jam'iyya masu irin wannan korafi har da ministan yaɗa labarai na kasar Lai Mohammed, wanda ya fito ƙarara ya soki yadda aikin sabunta rijistar ke gudana a jiharsa ta Kwara.
Ministan yaɗa labaran ya ce "idan dai har dalilin yin aikin shi ne sabunta rigistar dukan mambobi da kuma yi wa sabbi rijista, to me ya sa ake ware wasu?.
A cewarsa: "Tun lokacin da kwomitin rijistar ya je birnin Illori na jiharsa ta Kwara a karkashin jagorancin Sanata Dan Boye aka nemi kwomitin aka rasa shi ƙasa da sama, babu kuma wata ganawa da ya yi da halattattun 'yan 'yan jam'iyyar a wannan jiha domin tattauna batun rijistar.
Lai Mohammed ya ƙara da cewa "ganin yadda wannan salo ya soma, a bayyane take cewa ana ƙoƙarin hana wasu sabunta shaidarsu da gan gan, saboda biyayya ga wani jagoran jam'iyyar.
Ya ce kamata ya yi duk jihar da aka je gudanar da wannan aiki a tuntubi masu ruwa da tsaki da masu rike da mukamai a jam'iyya domin ganin an tafi da kowa ba tare da wariya ba, abin da ya saɓawa yadda ake gani a halin yanzu
Haka zalika tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasar Adams Oshiomole ya soki rijistar da ake ci gaba da gudanarwa a yanzu haka, yana cewa cike take da kura-kurai.
Tsohon gwamnan Legas, kuma jagoran jam'iyyar APC na ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya fara sukar sabuta rijistar, da ya kira a matsayin "ɓata lokaci."
A jihar Kano ma dai an samu irin waɗannan rahotanni, inda wani ɗan majalisar wakilai Sha'aban Sharada ke cewa jagororin jam'iyyar APC a jihar sun hana shi sabunta rijistarsa tare da magoya bayansa, saboda ya yi amanna da tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari.
Ana danganta masu sukar rijistar da goyon bayan jagoran jam'iyyar APC ƙasa Bola Ahmad Tinubu, wanda ake rade-radin cewa zai tsaya takara a kakar zabe ta 2023.
Me APC ta ce dangane da batun?
Mai Malam Buni gwamnan jihar Yobe kuma shi ne shugaban ruko na jam'iyyar APC na kasa baki daya ya ce duk dan jam'iyyar APC a fadin kasar baki daya babu wanda zai hanashi yin rijista kuma babu wanda aka ba ikon hana shi yin rijista ko sabinta katin zama dan jam'iyya.''
Bugu da kari shugaban jami'iyyar ya jaddada cewa da akwai kwamitin daukaka kara idan jama'a za su gabatar da koken su idan ba a masu rijista ba domin sanin matakin da za a dauka na gaba.
Ko da a kwanakin baya , Bola Ahmed Tunibu jagoran jam'iyyar ta APC ya furta cewa wannan rijista da ake yi aikin banza ne kawai.
Masu nazarin lamuren siyasa a Najeriya, na ganin cewa wannan matsaloli da ke faruwa a cikin jam'iyyar APC na iya bibiyar ta har zuwa babban zaben 2023 idan ba a tashi tsaye ba.