Ku San Malamanku tare da Dokta Zakariyya Sa'id Zakariyya

An wallafa

Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira da Dokta Zakariyya Sa'id Zakariyya:

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Dokta Zakariyya Sa'id ya shafe shekaru yana karatun Alkur'ani a gidansu, kafin daga baya ya tafi garuruwa da dama wajen neman ilimi.

An haifi Dokta Zakariyya a shekarar 1960, a wata tsangaya dake Kandi a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa.

Mahaifinsa Malami ne na Alkur'ani wanda yake da almajirai da dama.

Dokta Sa'idu ya shafe shekaru yana karatun Alkur'ani a gidansu, kafin daga baya tafi garuwa da dama da suka hada da Takai a jihar Kano da garin Bauchi da birnin Kano da biranen Zariya da Kaduna a jihar Kaduna.

Yawon karatun nasa ya kai shi ga shafe shekaru da dama yana daukar karatu a wajen babban malamin nan Sheikh Abubakar Mahmud Gumi a garin Kaduna.

"Duk karatun da na yi babu inda nake jin dadinsa nake ji na karu kamar karatun da na yi a gaban Sheikh Abubakar Mahmud Gumi," in ji Dokta Zakariyya.

Ya haddace Alkur'ani tun yana da kuruciya. To amma fa ya ce Suratul Waki'a ta bashi wahala sosai a lokacin da yake karatu, kuma har yanzu yana gwagwagwa da ita.

Ya ce a duk wuraren da ya yi karatu ba ya saka littafi a gaban duk malaman da ya yi karatu a wajensu, sai dai ya je ya zauna a inda ake karatu yana saurara, daga baya kuma ya koma gida ya yi bitar abin da ya koya.

Daga baya ya koma jihar Katsina inda ya shiga makarantar horar da malamai ta Katsina bayan ya dauki jarrabawa a jihar Kaduna a 1984 inda ya kammala karatun sakandare a 1990.

Ya halarci kwalejin horar da malamai ta Gumel a jihar Jigawa inda ya samu shaidar NCE, sannan ya halarci jami'ar Bayero Kano inda ya samu shaidar digir, sannan ya yi digiri na biyu da na uku a kasar Sudan.

Dokta Zakariyya ya fara karantarwa a firmare, sannan ya koyar a sakandare, a yanzu kuma yana koyarwa a kwalejin shari'ar addinin Musulunci ta Ringim a jihar Jigawa.

Shehin malamin yace babu abin da yake jin dadin mai da hankali a kai idan ba ya komai kamar bude littafi ya yi karatu.

Sai kuma jin labarai musamman daga gidajen rediyo na duniya.

Dokta Zakariyya yana da mata uku da 'ya'ya 18.

Ya auri matarsa ta fari a lokacin da yake Katsina, sannan ya auri sauran biyun a Dutsen jihar Jigawa.