Wariyar launin fata a Afirka ta Kudu: 'Har yanzu ba ma ma kallon kanmu a matsayin dan adam kafin komai'

Asalin hoton, Corbis
Nuna wariya game da launin fata a shari'ance a Afrika ta Kudu ta zo karshe ne lokacin da aka daina mulkin wariyar launin fata, sai dai har yanzu ana amfani da bambancin launin fata a gwamnatance lokacin da ake biyiyar sauyi a tattalin arziki wanda kuma hakan na janyo ce-ce-k-uce, kamar yadda Muhammed Allie ya rubuto mana makala daga birnin Cape Town.
Tuhumar da aka yi wa wani malamin makaranta Glen Snyman watanni uku baya, kan ware wani wurin sa hannu ga duk dan Afrika kan takardar neman aiki, a matsayin shugaban malamai a 2017, ta kara bankado matsalar da ake fama da ita a kasar game da wariyar launin fata.
Mista Snyman, wanda aka bayyana a matsayin wanda ke da tsatson baki da fari, an tuhume bisa irin wadannan ayyuka amma babu matakin da aka dauka.
Gwamnatin wariyar launin fata ce ta kirkiri kudurin dokar kidayar 'yan kasar ta hanyar sanin yawan ko wane jinsi. An kaddamar da shi a 1950 wanda hakan ya raba Afrika ta Kudu zuwa gida hudu, farare da 'yan Afrika da Indiya da kuma sauran jinsi - domin samar da tsarin gwamnati marasa rinjaye.
An soke ta a 1991, lokacin da kasar ta koma kan tsarin dimokradiyya a 1994, amma har yanzu bambancin launin fata na da wurin zama a wasu bangarorin kasar.


Gwamnatin tana amfani da shi domin tattara bayanain da za su taimaka mata wajen saita rashin daidaito da ake fama da shi game da kudin shiga da kuma damarmaki kan tattalin ariki wadanda wariyar launin fata a baya suka haddasa.
Amma mutane da yawa ciki har da Mista Snyman, wanda ya kirkiri wata kungiya mai yaki da wariyar launin fata ta (Parc) a 2010, sun yi amannar cewa babu damar nuna wariyar launin fata a dimokradiyyar Afrika ta Kudu.
"Duk da cewa an soke kudurin dokar kidayar, gwamnatoci da yawa da kuma kamfanoni masu zaman kansu ba su da 'yancin amfani da launin fata wajen bambance mutane a Afrika ta Kudu," ya rubuta ya mika wa Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasar.
'Amfani da matsayi maimakon launin fata'
Lokacin da aka amsa cewa akwai wani gibi na rashin daidaito kuma ake neman cike shi, Mista Snyman ya nemi gwamnati ta rika amfani da wadata ko rashinta domin maye gurbin bambancin al'umma da launinsu a matsayin hanyar taimakawa masu bukata.
"Ba a bukatar gwamnati ta san mutane ta hanyar launinsu, suna bukatar sanin mutane da suke bukatar aiki ko kuma wani abu makamancin hakan da abin da suke nema.
"Ya kamata gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu su fitar da komai kawai zuwa ga 'yan Afrika ta Kudu babu bambanci ko sanin asalinsu," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Ryland Fisher, tsohon edita a jaridar Cape Times, shi ne ya yi wani aiki da aka yi masa suna Birni guda al'adu da yawa a 1999.
Ya ce: "Idan muka dauki mukamin mutane a matsayin hanyar magance bambanci bakaken fata za su amfana."
"Bakaken fata sun fi yawa a kasar kuma su ne mafi yawan talakawa. Idan an ce za a magance bmnbanci ta fuskar matsayi, bakin mutum wanda ke rayuwa matsakaiciya ba zai cancanci damar da ke da akwai ba a bangaren tattalin arziki kan ma'aunin da gwamnati ke amfani da shi," in ji shi.
Amma a wasu lokutan kiran mutane da launinsu yana haifar da wani sauyi da ya kara munanan bambance-bambacen da ake tsakanin al'umma.
A yammacin Cape, inda yake da mutane da yawa da ake kira da launin fatarsu, akwai dogon buri a rayukan mutane na ganin an magance wannan matsalar, sai dai gwamnatin dimokradiyya ta yi watsi da wannan bukatar tasu.
Wasu masu fafutuka da ake kira da launinsu, sun kafa wata kungiya da ake kira Gatvol a 2018.
A wani bidiyo da kungiyar ta wallafa a shafinta na Facebook shugaban kungiyar Fadiel Adams ya yi bayani kan cewa "sai gwamnati a duka matakai sun dauki azamar yaki da tattalin arziki da ake yi da launin fata", yana cewa al'umma ba su da aikin yi duk da cewa su ne mafi ya yawa a yankin.
Mista Fisher wanda tsohon edita ne a wata jarida, ya ce mutanen da ake kira da launinsu sun yi farin cikin wannan gwagwarmaya tare da bakaken fata a wani yakin kawo karshen mulkin wariyar launin fata.
Amma ya dora alhakin komai kan gwamnatin jam'iyyar ANC da ta kara iza wutar bambance-bambancen launin fata.
"Gaskiya ANC ba ta mayar da hankali kan wadannan matsalolin ba. Sun alakanta kansu da mutanen da suke kiran kansu da launinsu. Me hakan yake nufi game da wadannan mutane"
Shi da wasu mutane sun zargi gwamnatin ANC ba ta yi abin da ya kamata ba kan rikicin, maimakon kuma ta mayar da hankali kan wadanda suka fi yawa a kasar, wadanda su ne 'yan Afrika ko kuma bakake.
'Muna daukar kanmu a matsayin bakar fata'
Akan wannan mahangar ne kuma Mista Snyman ya samu goyon bayan kungiyar malaman kasar.
"Da yawa daga cikinmu sun dauki matakin kar a rika ambatonsu da launinsu kamar yadda ake yi a lokacin mulkin wariyar launin fata. Muna daukar kanmu a matsayin bakar fata, 'yan Afrika kuma 'yan kasar Afrika ta Kudu in ji mai Magana da yawun kungiyar a yammacin Cape Jonavon Rustin.
Amma wasu na amfani da bambancin siyasa ko kuma al'ada don maganin bambancin da gwamnatin wariyar launin fata suka haifar.
Zodwa Ntuli, wata kwararriya kuma kwamishiniya ce a hukumar karfafa tattalin arziki ta Afrika ta Kudu ta ba da shawarar cewa a matsayin kasar da ke son magance matsalar wariyar launin fata da aka kaka ba mata a baya, hukumomi da gwamnati za su iya amfani da ma'aunin da aka rika amfani da shi a baya ta hanyar kididdiga.


Game da tasirin mulkin wariyar launin fata kan 'yan Afrika da 'yan Indiya da sauran mutane, ta kuma nuna cewa watsuwar da fafaren fata suka yi zai sa su ci gaba da mamaye bangaren tattalin arziki wajen mallakar masana'antu da kuma karfin yanke hukunci kan abubuwan rayuwa.
Amma ta maimaita cewa "babu wanda aka bai wa izini a Afrika ta Kudu ya yi amfani da launin fata ko jinsi wajen hana wani dan kasar damar da yake da yake da ita a hukumance.

Kganki Matabane, wanda ke jagorancin majalisar 'yan kasuwa bakaken fata, ya ce kodayake an kwashe shekara kusan 27 ana mulki dimokradiyya, amma ya yi wuri a daina nuna irin halin da aka shiga a baya.
"Akwai bukatar mu tambayi kanmu: muna tafiyar da bambance-bambancen da ke tsakaninmu yadda ya kamata. Idan ba ma yi, to ina mafita - idan muka duba manyan kamfanonin hada-hadar kudi na Johannesburg kashi 75 cikin dari fararen fata ne ke tafiyar da su - kuma dole ne mu ci gaba da su."












