Fitattun ƴan Afirka da suka mutu a 2020: Daga makaɗan Jazz zuwa taurarin ƙwallon kafa

Asalin hoton, Various
Yayin da shekarar 2020 ke daf da kawowa karshe, lokaci ya yi da za a tuna da wasu daga cikin mushahuran mutane a nahiyar Afirka da suka mutu a cikin shekarar nan.
Anan za mu duba 10 daga cikin wadanda suka bar duniyar wasan kwallon kafa da fannin kimiyya da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe da kasuwanci da aikin likita da siyas da fafutuka da wasan kwaikwayo.

Kwallon kafa: Papa Bouba Diop, shekaru 42
Dan wasan kwallon kafa na kasar Senegal, wanda ya mutu a cikin watan Nuwamba bayan ya sha fama da rashin lafiya, an karrama shi saboda gagarumar rawar da ya taka a gasar wa san kwallon kafa na duniya a shekara ta 2020, inda ya ciyo wa kungiyarsa kwallon da suka samu nasara kan kasar Faransa, ya kuma tabbatar da ganin kasar ta Senegal ta kai ga shiga zagayen kusa da na karshe.
Babu wata kungiyar kwallon kafa ta Afirka da ta kai ga wannan mataki.

Asalin hoton, Getty Images
Gagarumar nasarar da ya samu a sana'arsa ta kwallon kafa ita ce cin kofin FA na shekarar 2008 a kungiyar Portsmouth.
Ya kuma buga wa kungiyoyin Fulham, da West Ham United, da Birmingham City da French Club Lens.
Mun kuma yi rashin: Leon Mokuna, daga Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, da dan kasar Gambia Alhaji Momodu Njie (da aka fi sani da "Biri Biri"), wadanda dukanninnsu su ne na farko a fagen 'yan Afirka da ke buga wasa a kasashen Turai.
Da kuma dan kasar Kamaru Stephen Tataw, wanda dan wasa ne da shi ma ya mamaye kafafen yada labarai na duniya kan muhimmiyar rawar da ya taka a gasar wasan kwallon kaf ana duniya.
Kimiyya: Gita Ramjee, shekaru 63
'Yar kasar Afirka Ta Kudu kuma haifaffiyar kasar Uganda da ta yi fice a fannin ilimin kimiyya, ta mutu a cikin watan Maris sakamakon cutar korona.

Asalin hoton, Aurum Institute
Ta yi fice a fannin bincike kan rage barazanar yaduwar cutar nan mai karya garkuwar jiki a tsakanin mata masu zaman kansu.
Shekaru biyu da suka gabata cibiyar hadin gwiwar binciken cututtuka da maguguna ta bunkasa kasashen Turai ta ba ta lambar yabo ta mata masu ilimin kimiyya.
Mun kuma yi rashin: Simon Mallam, shugaban hukumar makamashin nukiliya na Najeriya, wanda ya mutu sakamakon fashewar tukwanen iskar gas a garin Kaduna.
Kade-kade: Manu Dibango, mai shekaru 86
Mai kaɗe-kaɗen da bushe-bushen zamani ɗan kasar Kamaru, wanda ya mutu a cikin watan Maris sakamakon cutar korona.
Yana hada kaɗe-kaɗe da bushe-bushen Jazz da na gargajiya, kuma ya yi fice a salon waƙoƙinsa na Soul Makossa a shekarar 1972.

Asalin hoton, AFP
Ya kai ƙarar shahararren mawaƙin nan Micheal Jackson a kan abin da ya kira satar wasu layuka biyu daga cikin wakokinsa, inda ya yi amfani da su a cikin kundin wakokinsa da suka yi fice, Thriller.
Amma sun daidaita kansu a wajen kotu.
Mun kuma yi rashin: Masu salon wakokin Afirka irin su na farko kamar Tony Allen, da 'Yan kasar Congo Aurlus Mabele da Kasongo wa Kanema da Balla Sidibé, wanda ya ƙirƙiro ƙungiyar mawaƙa na kasar SenegalOrchestra Baoba, da dan kasar Somalia Ahmed Ismail Hussein Hudeidi.
Sai ɗan kasar Kenya John Nzenze, da wanda ya kirkiro kungiyar mawakan Ladysmith Black Mambazo Joseph Shabalala.
Da dan kasar Rwanda mai wakokin yabo Kizito Mihigo, sai mawaƙi dan kasar Algeria Hamid Cheriet, da aka fi sani da Idir, da kuma fitaccen mawakin reggae dan Nigerian Majek Fashek da Hachalu Hundessa dan kasar Ethiopia.
Kasuwanci: Richard Maponya, shekaru 99
Dan kasuwa, wanda ya mutu a cikin watan Janairu, ana yi masa laƙabi da baban baƙaƙen fatar 'yan kasuwa a Afirka Ta Kudu, wanda ya kauce wa takunkumin gwamnatin nuna wariyar launin fata ya kafa katafaren kamfaninsa.

Asalin hoton, Getty Images
A birnin Soweto, birni mai yawan baƙaƙen fata a kasar, ya kafa kamfanin dillancin motocin BMW na farko kana ya gina katafaren rukunin shaguna mai suna Maponya Mall.
Aikin likita: Hawa Abdi, shekaru 73
Likita 'yar kasar Somalia kuma mai fafutukar kare hakkin bil adama, wacce ta mutu a cikin watan Agusta, an fi saninta da "Mother Teresa ta kasar Somalia".

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da masu gwagwarmaya da makamai suka kai hari a kan asibitinta a shekarar 2011 a yankin Lower Shabelle, ta jajirce, kuma maharan sun janye bayan wata zanga-zanga da daruruwan mata mazauna yankin suka yi.
Mun kuma rasa: Fitaccen likitan tiyatar nan na kasar Sudan Adil El Tayar, da dan Najeriya Emeka Chugbo, da Ashraf Emarah, da dan kasar Masar din nan ƙwararre a fannin tiyatar fata da ya yi aiki a kasar Kenya.
Da dan kasar Kamaru Tchouamo Michel, wanda ya mutu da cutar korona. Sai Catherine Hamlin, wata likitar mata 'yar kasar Australia da aka karrama ta hanyar ba ta takardar zama cikakkiyar 'yar kasar Ethiopia saboda ƙwazon aikinta wajen tiyatar mafitsarar mata, ita ma mutu.
Siyasa: Daniel arap Moi, shekaru 95
Mutumin da ya mamaye fagen siyasar kasar Kenya har na tsawon fiye da uku bisa hudu na karni, ya mutu a watan Fabrairu.
Shi ne shugaban kasar da ya fi dadewa a kan mulki a kasashen yankin gabashin Afirka, da ya yi shugabanci daga shekarar 1978 zuwa 2002.

Asalin hoton, Getty Images
Daniel Arap Moi ya yi shugabancin kasa tun daga shekarar 1978 zuwa 2002.
Aminansa sun yaba masa kan wanzar da zaman lafiya, amma masu sukar lamirinsa sun ce ya riƙa gallaza wa 'yan adawa kuma a shekarar 2004, ya nemi afuwa daga ''wadanda ya ci zarafi''.
Mun kuma rasa: Firaiminista mai ci na kasar Ivory Coast Amadou Gon Coulibaly, Ambrose Dlamini, da Firaiministan Eswatini, da shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza.
Akwai wasu tsofaffin shugabannin kasa da su ma suka mutu, da suka hada da na Ghana Jerry Rawlings, na Masar Hosni Mubarak, na Tanzania Benjamin Mkapa, na Mali Moussa Traoré da Amadou Toumani Touré, da na Niger Mamadou Tandja, da na Burundi Pierre Buyoya, da na Congo-Brazzaville Jacques Joaquim Yhombi-Opango da na Mauritania Sidi Ould Cheikh Abdallah.
Sauran fitatun 'yan siyasar da suka mutu akwai na kasar Libya Mahmoud Jibril, da na Somalia Hassan Abshir Farah, da na Sudan Sadiq al-Mahdi, da suka shugabanci kasashensu a matsayin firaiminista.
Fafutuka kan nuna wariyar launin fata: Zindzi Mandela, shekaru 59
'Yar autar marigayi shugaban kasa bakar fata na farko a Afirka Ta Kudu Nelson Mandela, tana kan matsayin jakadiyar Afirka ta Kudu a kasar Denmark lokacin da ta mutu da cutar korona a watan Yuli.

Asalin hoton, AFP
Ta girma a daidai lokacin da ake fafutikar nuna adawa da mulkin fararen fata marasa rinjaye yayin da aka kulle mahaifinta a gidan yari a tsibirin Robben, inda ya jure wa shekarun gallazawa daga mulkin nuna wariyar launin fata.
A watan Fabrairun shekarar 1985 ne a wani taron jin bahasin jama'a, ta karanta a bayyane ƙin amincewar da mahaifinta ya yi da tayin da Shugaba PW Botha ya yi na sakinsa daga gidan yarin a bisa wani sharadi.
Ta kuma rikiɗe ta zama mai fafutuka, inda ta rika yin matsin lambar a kawo sauye-sauye da gaggawa a kasar.
Mun kuma rasa: Lauya mai rajin kare hakkin bil adama George Bizos, wanda ya yi fice wajen kare Nelson Mandela, da Andrew Mlangeni da Denis Goldberg, da aka yanke wa hukuncin daurin tare da Nelson Mandela a wata shari'a maras farin jinni a Rivonia.
Wasan kwaikwayo: Nikita Pearl Waligwa, shekaru 15
Yarinya 'yar wasan kwaikwayo ta kasar Ugandan ta mutu a cikin watan Fabrairu sakamakon cutar kansar kwakwalwa.
Tauraruwar ta fim din 'Queen of Katwe' na kamfanin Disney, ita ce ta farko da aka gano tana da kansar kwakwalwa a shekarar 2016 kuma daratan fim din ya kafa gidauniyar neman tallfin kudin da za a yi mata magani a kasar India.
Shekara daya bayan da aka bayyana ta samu lafiya, amma daga bisani cutar ta sake bayyana a shekarar 2019.

Abokin fim din nata David Oyelowo ya ce ta kasance tamkar ''fitila'' mai haskaka fim din da kuma rayuwarta: "Faman da ta yi da kansar kwakwalwar abin tausayi ne.''
Mun kuma rasa: Mashahuran mutane daga Najeriya, marubuci Chukwuemeka Ike da marubucin wakoki John Pepper Clark; da dan kasar Kenya marbucin a harshen Swahili Ken Walibora, da fitaccen tauraron fim na kasar Masar Mahmoud Yassine da shahararren mai daukar hoton nan na Afirka Ta Kudu Santu Mofokeng.
Fafutika: Lina Ben Mhenni, shekaru 36
Marubuciya a shafin yanar gizo 'yar kasar Tunisia kana mai fafutukar kare hakkin bil adama ta mutu a cikin watan Janairu bayan ta dade tana fama da rashin lafiyar da ta shafi garkuwar jiki.

Asalin hoton, Getty Images
Ta fara samun daukaka ne a farkon juyin juya halin shekara ta 2011 ta hanyar rubuce-rubucen da ta yi wa laƙabi da 'Tunisian Girl'.
Daya daga cikin mutane kadan da suka yaɗa yadda aka rika gallazawa masu zanga-zanga a Sidi Bouzid - inda aka fara tashe-tashen hankulan da suka haifar da kifar da gwamnatin shugaba Zine el-Abidine Ben Ali suka fara, wanda ya haddasa zanga zangar da ta mamaye kasashen Larabawa da aka yi wa lakabi da 'Arab Spring'.
Mun kuma rasa: Barbara Allimadi, 'yar kasar Uganda da ta yi fice kan ''zanga-zangar saka rigar mama''.
Da kuma mai fafutikar yaki da aikata fyade a kasar Libyan Hanan al-Barassi, da kuma dan Najeriya mai zanga-zangar nuna kin jinin cin zalin 'yan sanda #EndSars Anthony Unuode.
Babban al'amari: Hachalu Hundessa, shekaru 34
Kashe fitaccen mawakin na kasar Ethiopia a cikin watan Yuni ya haifar da tashe-tashen hankula masu nasaba da ƙabilanci.
Kuma ya haddasa mutuwar mutane fiye da 160 da kuma fitattun 'yan adawar kasar da suka hada da Jawar Mohammed, da ke fuskantar tuhuma kan ayyukan ta'addanci.

Wakokin Hachalu sun mayar da hankali ne kan hakkin 'yan kabilar Oromo mafiya rinjaye a kasar ta Ethiopia, kana ta zama gama-gari a lokacin zanga-zangar da ta haifar da kawo karshen mulkin firaiministan kasar a shekarar 201
Mun kuma rasa: Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza, wanda ya shafe shekaru 15 yana Mulki. Lokacin da tsohon dan tawayen ya kama mulki bayan yakin basasa, ya nuna alamun wanzar da zaman lafiya a kasar.
Amma tun bayan da ya fara nuna aniyarsa ta yi tazarce karo na uku ne a shekarar 2015 kasar ta sake fadawa cikin tashe-tashen hankula.8.










