Mummunar guguwar tokar da ta firgita wani ƙauye a Brazil

    • Marubuci, Daga Vinicius Lemos
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Daga kallon farko, faifan bidiyon da aka yaɗa a shafukan sada zumunta na nuna mummunar ƙurar tokar.

Amma kuma hotunan an dauke su ne a yankin Pantanal na ƙasar Brazil, inda da wuya yanayin kan saisaita - musamman ba kusa da lokacin bazara ba a yankin kudanci.

Toka da kasa ce ke saukowa daga sama a Barra do Sao Lourenco, ƙauyen da mazaunansa suka kai kimanin 100, yanki mai damshi mafi girma a duniya.

Mazauna ƙauyen sun shaida wa BBC cewa guguwar ta ƙara ƙaruwa a cikin makonnin baya-bayan nan.

Kwararru sun ce hakan na faruwa ne saboda gobarar da ta mamaye yankin na Pantanal cikin wannan shekarar tun daga watan Janairu zuwa Oktoba.

Gagarumar gobarar ta lalata kusan faɗin murabba'in kilomita dubu 45, kamar yadda wata ƙungiya mai zaman kanta SOS Pantanal Institute ta bayyana.

(Faifan bidiyon wanda aka ga wani masanin kimiyyar halittu na kasar Brazil Hugo Fernandes ya wallafa, ya nuna guguwar tokar a yankin Sao Lourenco da ke kama da guguwar kankara.)

Wannan ya ninka fiye da hudu na birnin New York da kewaye.

Yayin da gobarar ta lafa, mutanen da ke zaune a yankin na cigaba da fuskantar matsalolin da ta haifar.

'Tokar na maƙale wa komai'

Maria de Souza, wata mazauniyar Sao Lourenco, ta ce ta shaida guguwar tokar a makonnin da suka gabata.

"Abin babu kyawun gani. Haka kuma ga hadari ga lafiya, gidanmu ya cika da datti, kana tufafinmu sun yi datti,'' ta ce.

"Tokar na maƙalewa komai.''

"Wata rana, na fita daga gida a lokacin da aka fara iska. Babu lokacin komawa ciki don saka takunkumi. Na fara tari sosai,'' in ji de Souza.

Alexandre de Matos, wani masani kan al'amuran muhalli da ke hukumar kare dazuka daga akuwar gobara ta ƙasar Brazil, ya bayyana cewa hasken na abkuwa ne saboda ɓaraguzai da burbuɗin da gobarar ta haifar.

"Iska mai karfi ce ke tayar da tokar, saboda babu isasshen ruwan sama da zai wanke su zuwa cikin kogi.''

Afkuwar hakan wani abu ne na ba-zata

Wannan shi ne karon farko da aka samu afkuwar bala'i irin wannan a yankin na Pantanal tun bayan da hukumomin Brazil suka fara sa ido kan abkuwar gobara a yankin cikin shekarun 1990.

Matos ya ce akwai rahotanni game da guguwar mai karfi na kwaye rufin dakuna da gidaje.

Matsalar ta kara ta'azzara ne saboda yadda gobarar da kone bishiyoyi da dama da suka saba kare al'umomin yankin daga iska mai karfi.

"Babu bishiyoyi da yawa yanzu. Da za su iya yin kariya daga guguwar tokar,'' Matos ya yi amanna.

Guguwar toka ta farko in ji masana, ta faru ne a tsakiyar watan Oktoba.

Serra do Amolar, wani wuri da ake dauka a matsayin mafi muhimmanci wajen alkinta yankuna masu dausayi, shi ma ya gamu da abkuwar guguwar tokar.

A lokacin da gobarar ke cigaba da ci, akwai hayaƙi tare da iska da kuma burbuɗin toka. Wannan kaɗai ya isa ya hana matuka jiragen sama masu kashe gobara iya ganin komai.

Rana ta koma tamkar dare

"Abin ban tsoro ne, na ba-zata,'' Angelo Rabelo, wani mai bincike da ke kungiyar IHP, mai sa ido kan al'amuran muhalli a yankin ke tunawa.

"Rana ta koma tamkar dare a cikin mintoci kuma har sai da ya kai da wayewar gari.''

Amma tun a wannan lokaci guguwar ba ta daina ba.

Masana sun ce duk da cewa ta ragu, amma sun ci gaba da haddasa matsaloli ga jama'ar yankin.

"Na riga na shaida irin wannan guguwar toka har sau biyu. Wannan ba sabon abu bane,'' in ji Rabelo

"Suna haifar da fargaba.''

Rabelo ya ce rashin damshi, da yanayi mai zafi da kuma farin da aka fuskanta a baya-bayan nan ya kara haddasa matsalar.

Babu wasu alƙaluma a hukumance kan adadin yawan guguwar tokar da aka fuskanta a yankin na Pantanal, amma kuma mazauna Sao Lourenco sun ce sun shaida abkuwar hakan a kullum a bayan nan.

''Tun cikin watan Oktoba, kusan ko wane mako sai an samu abkuwar wannan guguwa. A makon da ya wuce ma kusan kullum ne,'' in ji Leonida Aires.

Wani mai sana'ar kamun kifi a yankin Rosinei de Jesus, ya yi wa BBC bayani game da guguwar tokar da ya shaida a yammacin 30 ga watan Nuwamba.

"Kusan karfe biyu na yamma ne kuma ba ma iya ganin komai. Halin da muke ciki a nan akwai wahala'', ya ce.

Guguwar ta haddasa matsaloli na kiwon lafiya ga mazauna yankin bakin kogi. Rahotanni sun ce matsalolin da suka shafi numfashi sun zama ruwan dare a nan.

Hakan na kuma kara wa wadanda daman suke fama da matsalolin numfashin shiga hadari.

"Gurbacewar iska, da aka fi dangantawa da kona abubuwa kamar kashin dabbobi ko tsirrai, kan haifar da wasu ɓurɓushi.

Kuma yanayin kankantarsu, yanayin yadda za su iya shiga kofofin hanci,'' in ji Patricia Canto, wata likitar huhu daga Fiocruz, ɗaya daga cikin cibiyoyin binciken kiwon lafiya mafiya muhimmanci a ƙasar Brazil.

Matasalar ta kara zama babban abin damuwa lokacin annobar cutar korona.

"Akwai wasu bincike da suka nuna cewa akasarin adadi wadanda suka mutu da cutar korona a ƙasar a yankunan da ke da matsalolin gurbacewar muhalli,'' Canto ta kara da cewa.

Amma kuma matsalolin na kara bayyana ne bayan shekaru.

Kogi ma bai tsira ba

"Muddin matsalar ta ci gaba, za ta iya haifar da cutar kansar huhu, wacce za ta iya kama mutum a hankali ne musamman ga wadanda suka daɗe suna shakar irin wannan guguwa,'' in ji ƙwararriyar.

Tokar da kuma guguwar na nuni da ɗaya daga cikin halin kuncin da yankin Sao Lourenço ke ci gaba da fuskanta saboda gobarar yankin Pantanal.

Akwai ƙarancin ruwa da abinci a tsakanin al'ummomin, da ke zaune a gabar kogin Paraguay.

Kogin, wanda shi ne hanyar samun kudaden shiga na mazauna yankin, ya kara kafewa cikin shekaru da dama.

Haka kuma, gobarar ta lalata ingancin ruwan kogin, wanda ake ganin bai kamata mutane su yi amfani da shi ba.

"Ruwan sama bai wadata ba, ta yadda zai bunkasa kogin, kuma hakan ya sa harakar kamun kifi ta zama da matukar wahala.

Guguwar da kawo bubushi da kuma toka cikin kogin,'' masani kan harkokin alkinta muhalli Alcides Fariada ke aiki a yankin ya bayyana.

A ganin Faria, mazauna yankin da dana na fama da gudawa bayan shan ruwan kogin.

Kamun kifi na da matukar muhimmanci a Sao Lourenco, amma gurbacewar ruwan kogin ya kashe kifayen.

"Babban bala'i ne. Abin takaici, 'mutum ne sanadi' Leonida na kokawa.

Ta danganta sakamakon binciken masanan da cewa dan adama ne ke haddasa gobarar yankin Pantanal a shekarun baya-bayan nan.

Leonida wata mai zane-zane ce da ke amfani da ganyayen wata ciyawar ruwa wajen gudanar da aikinta. Ta ce su ma ciyayin sun bace.

"Yanzu irin wadannan tsirrai kadan ne yanzu, saboda gobara da kuma matsalar fari.''

Ta ce mazauma yankin suna rayuwa ne ta hanyar taimakon gaggawa da suke samu.

Kana wasu kan samu agajin abinci. "Wasu mutanen na zuwa da abinci wanda hakan na taimaka mana,'' ta ce.