Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tagwayen da aka haifa manne da juna sun ce 'mun san cewa mu mutane ne na musamman'
- Marubuci, Daga Rebecca Woods
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
A Disambar shekarar 2001 aka gudanar da wata tiyata a wani asibitin yara da ke Birmingham inda aka raba wasu tagwaye ƴan watanni uku da haihuwa da suke a manne da juna.
A yanzu wadannan tagwaye wato Sanchia da Eman, na da shekarar 19 kuma suna rayuwa kamar kowannne ɗan adam.
Likitocin da suka yi wannan tiyata sun ce an ɗan samu matsala a lokacin tiyatar da aka shafe sa'o'i 16 ana yi kan tagwayen da suke manne da juna, amma daga bisani an samu nasarar raba su.
Wannan tiyata ita ce ta farko da aka yi a asibitin kuma ta farko da aka yi a Birtaniya sannan ta uku da aka taba yi a duniya.
Tiyata ce mai haɗarin gaske saboda yadda ake raba tagwayen akwai fargaba sannan damar ci gaba da rayuwar irin waɗannan tagwaye da aka raba ba ta wuce 5 ko 25 cikin 100.
A wasu lokuta idan an samu nasarar raba irin su, to daga baya a kan samu wata mishkila ko tawaya daga wajen ɗaya daga cikinsu ko dukkansu.
To amma a ɓangaren tiyatar su Sanchia da Eman, abin sai son-barka, saboda an samu gagarumar nasara domin dukkansu suna cikin koshin lafiya babu wata tawaya kuma a tare da su.
A yanzu Sanchia da Eman na karatu a jami'a tare da kanwarsu Damaris, wadda aka haifa watanni 11 bayan an haifi tagwayen, kuma suna tare su uku a kodayaushe.
Eman ta ce: "Mutane ba su fiye magana a kan yadda aka haife mu ba, amma kuma mu mun san ko su waye mu".
Ita kuwa Sanchia cewa ta yi: "Likitoci sun yi hasashen cewa za mu iya rayuwa kamar kowa bayan an raba mu,to amma dukkanmu muna da matsalar laka wadda za ta iya shafar ƙwaƙwalwarmu, ga shi muna da matsala a kafafunmu guda wanda aka yi tunanin zai iya shafar girmanmu. Ba a zaci za mu iya tafiya ba, amma da aka gan mu muna gudunmu ko ina sai mutane su rinka cewa lallai akwai abin al'ajabi".
Tagwayen sun ce, kafar tasu da ke da rauni ba wai matsala take ba su ba, idan tafiya ta minti biyar ce, to su takan dauke su minti 20, wani lokaci sukan yi amfani da kujerar guragu.
Sanchia ta ce,"Mun rungumi nakasarmu tun muna kananan, ba mu ba da dama wani ya ce mana ba za ku iya komai ba".
Ta ce," Ba zan manta ba a lokacin da muke shekara hudu muna makaranta muna kuma wasa sai wani yaro yake ce mana ba za ku iya wannan wasan ba saboda kafarku, tabbas hakan ne amma ba mu bari mun gaza ba a wasan".
Tiyatar da aka yi ta raba Sanchia da Eman an raba lakarsu ne wadda take a tare, kuma sai da likitoci suka yi taka tsan-tsan wajen wannan rabo saboda ba a taba irin tiyatar a kan kowa ba sai a kansu.
Dakta Tony Hockley, shi ne likitan da ya jagoranci tiyatar raba wadannan tagwaye, ya ce sai da aka raba wasu muhimman sassan jikinsu kamar mafitsararsu.
Sanchia ta ce,"A lokacin da muke yara mutane kan tambaye mu a kan cewa wai mu tagwaye ne da aka raba? Amma sai mu yi shiru saboda muna son boye sirrinmu".
Tuni dai likitan da ya jagoranci tiyatar tagwayen ya zama abokin iyalansu, kuma baya manta duk ranar zagayowar haihuwarsu domin ya kai musu ziyara.
To amma kash, wannan likita ya rasu a shekarar 2009 yana da shekara 65, abin da ya girgiza tagwayen da ma iyayensu, kuma a yanzu haka su kan kai wa iyalan wannan likita ziyara lokaci-lokaci.
Tagwayen kan ziyarci asibitin da aka yi musu tiyata aka raba su, sun saba sosai da ma'aikatan wajen, haka kuma su kan dan koyi wasu ayyuka a asibitin.
A wasu lokutan su kan gana da wadanda suka yi musu tiyatar har su sha hirarsu.
Sanchia ta ce,"Muna jin dadi idan muka ga wadanda suka taimaka a tiyatar da aka yi mana, kamar likitan da ya yi mana allurar sanya bacci da kuma daliban da ke neman sanin makamar aiki aasibitin lokacin da aka yi mana tiyata aka raba mu".
Tagwayen na jin dadin yadda suke mu'amala da mutane a makaranta kasancewar suna jami'a a yanzu, huldarsu da jama'a gwanin dadi, inji Eman.
Saboda yanayin da ake ciki na annobar korona, zaman kullen da suka yi a gida tare da ƙanwarsu ya kara musu shakuwa da juna.
Sun ce sun rasa daya daga cikin 'yan uwansu na jiki saboda korona don haka suke taka tsan-tsan, suka ce yanzu karatunsu ma ta intanet suke yi.
Tagwayen sun yaba da yadda 'yar uwarsu Damaris ke kula da su ko kuma taimaka musu musamman a lokacin da suke kanana.
Suka ce a kodayaushe bata gajiyawa da mu, duk wani taimako da yakamata ɗan uwa ya yiwa ɗan uwansa Damaris na yi mana.
Muna jin dadin yadda muke komai tare mu uku, in ji tagwayen.
Sanchia na karatun jami'a ne a bangaren a kan tsaro na intanet, Eman kuwa na karanta fannin siyasa da dangantakar kasa da kasa, yayin da Damaris kuwa ke karatu a bangaren ilimi matasa.
Eman dai na da burin shiga siyasa inda take bayar da misali da dan siyasar nan na Amurka Alexandria Ocasio-Cortez, saboda yana burgeta.
Tagwayen a kodayaushe su kan ce suna godiya ga irin yadda suka samu rayuwa mai kyau, saboda yadda ba a zaci zamu rayuwarmu ba, sai gashi mun girma har muna rayuwa kamar kowa.