Zanga-zangar Belarus: Mutumin da aka lakaɗa wa duka saboda bai wa mata furanni

An wallafa

Ƴan adawa masu zanga-zanga a ƙasar Belarus sun ci gaba da nuna turjiya a birnin duk da lakaɗa musu dukan da jami'an ƴan sanda ke yi, kwanaki 100 bayan da suka fito kan tituna don nuna adawa da sake zaɓen shugaban kasar Alexander Lukashenko.

Daya daga cikinsu shi ne Maksim Khoroshyn, wani mai kantin sayar da furanni a tsakiyar birnin Minsk.

Fuskarsa sananniya ce a lokacin zanga-zangar farko kan nuna ƙin jinin gwamnati, yayin da yake raba ɗaurin furanni ga matan da suka shiga gangamin.

Cike da farin ciki da annashuwa, ya riƙa miƙa musu furanni don ƙarfafa musu guiwa. Ya ce yana son nuna jin daɗinsa kan jajircewar masu zanga-zangar da suke nuna adawa da cin zalin da ƴan sanda ke yi.

Amma ba da daɗewa ba ne, shi ma Khoroshyn ya samu kansa cikin halin irin wannan cin zarafi.

A wata safiya ne cikin watan Oktoba, yayin da shi da matarsa suke ƙoƙarin shiga cikin mota, sai kawai aka buɗe ƙofar motar da ƙarfi inda wasu gungun mutane da ba a san ko su wane ne ba suka fizgo shi daga cikin motar.

Suna shan alwashi tare da lakaɗa masa duka.

Da farko Khoroshyn ya zaci zolaya ce, da yake mutanen ba sa sanye da kayan sarki, kana ba su rufe fuskokinsu ba. Amma abin ba na wasa ba ne.

An saba ganin mutane rufe da fuskoki cikin motocin da babu lamba ko alamar yin awon gaba da masu zanga-zanga, tun bayan da aka sanar da Shugaba Alexander Lukashenko a matsayin wanda ya lashe zaɓen tara ga watan Agusta.

Masu zanga-zangar sun ce an tafka maguɗin zaɓe, yayin da shugaban ƙasar ke musanta zargin.

Masu sukar lamirin Lukashenko na daukarsa a matsayin 'mai mulkin kama-karya na ƙarshe a ƙasashen Turai', wanda ya shafe shekara 26 a kan mulki, tun da ya hau karagar a shekarar 1994.

Khoroshyn ya shaida wa BBC cewa, bayan da ya sha naushi uku masu karfi a fuska, ba ya iya ganin komai - jini ya riƙa kwarara a fuskarsa.

Idanunsa sun kumbura, leɓensa ya fashe. An kuma tilasta masa kwanciya cikin jininsa, yayin da mutanen suka riƙa bincika motarsa.

An jefa mai sayar da furannin a cikin wata motar a-kori-kura, inda aka tilsta masa ya durƙusa, kana aka kai shi caji ofis.

A caji ofis ɗin an sake lakaɗa masa duka da kulake a fuskarsa da jikinsa wanda ya bayyana an shafe sa'o'i.

Ya ce mutanen sun faɗa masa cewa ''Mene ne bai yi maka daɗi ba a wannan ƙasar? Za mu koya maka yadda za ka ƙaunaci ƴan sanda!''

Ya ce sun yi masa barazana da zargin ƙarya.

"Za mu bayar da shaidar cewa ka jefa gurneti! Za mu bayar da shaidar cewa ka so banka wa gidan jagoran ƴan sandan kwantar da tarzoma wuta!''

'Raunuka na ban mamaki'

Bayan wani lokaci mai tsawo, Khoroshyn ya suma.

Waɗanda suka cafke shin sun farfado da shi ta hanyar shaƙa masa sinadarin ammonia kana suka ci gaba da dukansa.

Daga nan ne cutar sarƙewar numfashi ta Asthma ta tayar masa, da hakan ya sa aka kawo motar ɗaukar marasa lafiya.

Khoroshyn na iya jin su suna zagin junansu, tare da nuna damuwar cewa akwai yiwuwar sun yi masa lahani sosai.

An yi rijistar raunukan da ya samu a asibiti - amma daga bisani ƴan sandan sun ce ba za su iya tabbatar da ko daga ina mai sayar da furannin ya ji rauni ba.

Khoroshyn ya yi amanna cewa raba furannin da ya rika yi wa masu zanga-zangar ne ya fusata ƴan sandan, da kuma zagayawa da mota da ya riƙa yi ɗauke da tutar Belarus mai launukan ja da fari, wacce ƴan adawar suka riƙa amfani da ita a matsayin alama.

Tun bayan faruwar abin, ya bar Belarus kasar Lithuania, inda ya samu aka duba lafiyarsa kuma yana murmurewa. Yana da samun dimuwa game da abinda ya faru, kuma ana yi masa magani.

Khoroshyn ya ce ba ya jin zai iya sake komawa can.

'Yan adawa sun ce an tsare dubban mutane saboda zanga-zangar. Wadanda aka cafke sun ce an lakada musu duka, an gana musu azaba har ma da fyaɗe.

Daruruwan mutane sun samu munanan raunuka, lalacewar ƙwaƙwalwa, karaya a gabobinsu da munanan raunuka a idanuwansu.

'Mun ji zafin abin da aka yi mana'

Khoroshyn ya yi mamakin samun saƙonnin nuna goyon baya daga su kansu mutanen da suka samu kansu cikin halin cin zarafin a hannun ƴan sandan a cikin makonnin bayan zaɓen mai cike da taƙaddama.

Yayin da yake a kasar ta Lithuania, ya haɗu da Svetlana Tikhanovskaya, jagorar 'yan adawar Belarus wacce ita ma ta ke a kasar.

Khoroshyn ya ce mataimakinta ne ya haɗa shi da ita yana mai cewa ''Wannan shi ne mutumin da kike nuna damuwa a kansa.''

A lokacin da mai sayar da furannin ke magana a kan Tikhanovskaya, sai ya fara murmushi.

Ya ce bayan haɗuwarsu da Svetlana kawai sai suka rungume juna suka fara kuka.

"Ina ga wannan shi ne halin da duk wani ɗan kasar Belarus ke ciki a yau: muna jin ciwon da ya samu junanmu, kana kanmu a haɗe yake.''

Duk da azabar da aka gana masa, Khoroshyn ya yi amanna gwamnatin Lukashenko ba za ta iya jure jajircewar masu zanga-zangar ba.

"Ni ba mai son ɗaukar fansa ba ne,'' ya ce, ''amma ina son in ga ranar da zan yi tozali da mutanen da suka yi min duka, a lokacin da suka shiga bayan kanta.''