Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Amurka na 2020: Halin da Trump ya shiga a ranar da ya sha kaye a zaɓe
- Marubuci, Daga Tara McKelvey
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC na Fadar White House
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
A shekaru huɗu da suka gabata, na ga Shugaba Donald Trump a cikin yanayi mai kyau da marar kyau. Amma ranar 7 ga Nuwamba, ranar da ya faɗi zaɓe, rana ce da babu irinta.
Yana sanye da baƙar rigar sanyi, da wando baƙi da farar hula, shugaban ya fice Fadar White House mintoci kaɗan kafin 10:00. Ya shafe rabin yininsa yana wallafa bayanai a Twitter game da maguɗin zaɓe.
Daga nan ya shiga baƙar motarsa zuwa filin ƙwallon golf, a Virginia kusan kilomita 40 daga Fadar White House.
A wannan lokacin, ya yi ɓaɓatun ƙwarin gwiwa inda ya ce wannan kyakkyawar rana ce, da ta fi dacewa ga golf, kuma a filin golf ɗin zai kwana.
Amma mutanensa da ke masa aiki kamar sun kaɗu.
"Da fatan kana lafiya?" Na tambayi ɗaya daga cikin ƙananan ma'aikata.
"Lafiya," in ji ta. Ta yi murmushi, amma idonta ya nuna. Ta sunkayar da kai tana kallon wayarta.
Ruɗanin zaɓe
Fadar White House ta kasance cikin wani mawuyacin hali tun lokacin zaɓen. Ya kasance a ranar Talata, amma kamar a shekaru.
Kujeru da dama sun kasance kamar an yi ruwa an ɗauke lokacin da na shiga cikin ginin a ranar Asabar da safe. Yawancin ma'aikatan sun kamu da cutar korona, kuma sun ƙauracewa zuwa ofis. Wasu kuma an killace su.
Misalin ƙarfe 11:30 yayin da shugaban ke filin ƙwallon golf, BBC da sauran kafofin yaɗa labaran Amurka suka fara sanar da Biden ne ya lashe zaɓe, babban mai hamayya da shi na jam'iyyar Democrat.
Ina zaune a wani wurin cin abinci na Italiya da ke kusa da filin Golf din, na ji labarin. Ina ɗaya daga cikin ƴan jarida masu aiko da rahotanni a Fadar White House, waɗanda ke balaguro tare da shugaban ƙasa. Mun tsaya muna ta jiransa a filin golf.
"Yana da guba," a cewar wata mata a wajen gidan cin abincin, wacce kamar yawancin maƙwabtanta suka zaɓi abokin hamayyarsa.
Wasu sun yi mamakin lokacin da shugaban zai fice filin golf ya koma Fadar White House. Mintina da awanni sun wuce.
Ya ɗauki lokaci wannan karon,"kamar yadda wani jami'in tabbatar da doka ya shaida wa wani abokin aikinsa.
Shugaban bai nuna alamun barin filin ba cikin gaggawa, abokanansa a kewaye da shi. A harabar shiga filin, magoya bayansa ne suka dinga yi min ihu da sauran masu aiko da rahotanni, suna bayyana kalamai na kyamar ƴan jarida.
Wata mata ta tsaya ɗauke da wata alama da ke cewa "A dakatar da fashin zaɓe."
Wani mutum ya tunkaro da motarsa ta ɗaukar kaya a kusa da harabar filin golf yana ɗaga tuta ciki har da wadda ke nuna shugaban a tsaye saman tanki, kamar wani kwamandan duniya.
Hakan ya nuna yadda magoya bayansa ke ganin sa da kuma yadda Mista Trump ya ga kansa tsawon shekaru huɗu da suka gabata.
Daga ƙarshe ya fito daga filin golf din ya kama hanyar zuwa gida.
Masu caccakarsa sun daɗe suna jiransa - su dubbai.
'Ka faɗi kuma mun yi nasara'
Tawagar shugaban da ayarinsa sun yi ta yawo a cikin Virginia, tare da ni a cikin ayarin motocin a cikin wata motar da ta yi fitar kutso ta kaucewa hatsari a wani wurin ajiye motoci na Fairfax County Parkway.
Yawan jama'a na ƙaruwa a yayin da muke tunkarar Fadar White House: mutane sun fito don murnar kayar da shi. Wani daga cikinsu ya daga wata alama da ke bayyana cewa "Ka sha kaye mun yi nasara." Mutane sun ta yin ihu da yin shaguɓe.
Daga nan muka dawo Fadar White House, shugaban ya shiga ta wata ƙofa, kofar da ba kasafai shugabannin ke amfani da ita ba, kansa kuma a ƙasa.
Ya ɗan leƙo ya kalle ni da sauran ƴan jarida ya jinjina muna ta hanyar amfani da babban yatsa. Wannan wata gaisuwa ce da ba ta kai zuci ba, bai ɗaga hannunsa sama ba, kamar yadda ya saba.
Ko a Fadar White House ko a filin Golf, shugaban bai taɓa yin kasa a gwiwa ba: ya yi ikirarin da ba shi da tushe game da maguɗin zaɓe kuma ya nace za a tabbatar da shi.
Ya rubuta shafinsa na Twitter game da abin da ya kira "ƙuri'un da aka kaɗa ba bisa ƙa'ida ba" kuma zuwa da yamma ya sake yin ikirarin cewa "NA LASHE ZAƁE."
Amma Trump na Twitter ya sha bamban da wanda na gani. Yayin da yake shiga ƙofar Fadar White House da yamma, yangar ta tafi.