Zaɓen Amurka na 2020:Wane ne Joe Biden, mutumin da ya dinga son zaman shugaban ƙasa tun 1987?

An wallafa

Joe Biden ya yi nasarar lashe zaɓen Amurka a karo na uku da yake tsayawa takarar shiga Fadar White House.

BBC ta yi hasashen yin nasarar shugaban da ƙuri'a 270 na wakilai na musamman a kwamitocin masu zaɓen shugaban ƙasa, wanda hakan ke nufin zai sha rantsuwar mulki a watan Janairu, bayan gama sauraron kararrakin zabe.

Tsarin da Mista Biden ya bi na rashin kwarmato a yaƙin neman zaɓensa ya sha bamban da na Shugaba Trump da ke haɗa manyan gangami, a yayin da ɗan takarar Democrat ɗin yake bayyana kansa a matsayin mutum mai sanin ya kamata ta hanyar bin ƙa'idodin annobar cutar korona.

Duk da cewa tsohon shugaban ƙasar Barack Obama ya kira shi da ''mataimakin shugaban ƙasar da Amurka ba ta taɓa samun irinsa ba'', an yi ta sukar Mista Biden kan yanayin kamun ludayinsa a muƙaman da ya riƙe na tsawon shekara 40.

To wane ne Joe Biden kuma ta yaya a ƙarshe ya cimma burinsa na zama shugaban ƙasa wanda yake da shi tun a shekarar 1987 da ya fara sanar da aniyarsa?

'Ɗan uwan Obama'

Mr Biden ya tsaya takarar zaɓen fidda gwani a jam'iyyyar Democrat a 2008 kafin daga baya ya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Obama.

Shekara takwas ɗin da ya shafe tare da Obama a Fadar White House - inda yake yawan kasancewa a gefen shugaban ƙasar - ya bai wa Mista Biden damar yin ikirarin shi ne ƙashin bayan samar da wasu daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatin Obama ke yi, ciki har da Shirin Kula Da Lafiya Mai Sauƙi, da kuma tallafin kuɗi da ake bayar wa lokacin da aka shiga matsalar tattalin arziki.

Tarayyarsa da Mista Obama - mutumin da yake yawan kira da ''ɗan uwa'' - wataƙila ta sake taka rawa a wajen samun goyon bayan Amurkawa baƙaken fata masu zaɓe da ya yi.

Bayanan ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka kaɗa a 2020 sun nuna yadda baƙaƙen fata suka yi tururuwar ƙada wa Mista Biden ƙuri'unsu, wanda hakan ya ba shi wata dama ta yin gagarumar nasara a manyan jihohin da aka fi fafatawa irin su Georgia da Michigan da kuma Pennsylvania.

A matsayinsa na wanda ya san ciki da wajen gwamnatin Amurka, Mista Biden ya san al'amuran da suka shafi harkokin ƙasashen waje sosai, ya kuma taimaka wa Obama wajen ƙara saka shi sanin sha'anin mulki.

Mista Joe ya kuma taka rawa wajen amfani da shi da aka yi don shawo kan fararen fata masu zaɓe waɗanda suka zama ƙalubale ga yin nasarar Obama.

Hakan ya yi tasiri, sannan ya sake yin tasiri a shekarar 2020, inda Mista Biden ya yi nasarar samun goyon bayan jihohin da ae wa laƙabi da ''blue wall'' waɗanda su ne matattarar manyan masana'antun ƙasar, waɗanda suka juya wa Democrat baya lokacin da Trump ya tsaya takara a shekarar 2016.

Ya daɗe ana damawa da shi a siyasa

Mr Biden ya mamaye kanun labarai a 2012 bayan da ya ce ''yana matuƙar goyon bayan auren jinsi'', kalaman da ake gani a matsayin waɗanda za su rage ƙimar shugaban ƙasar da a lokacin bai nuna goyon bayansa kan manufar ba.

Kwanaki kaɗan bayan nan kuwa sai Mr Obama ya aikata hakan.

Karo biyun da Mista Biden ya goyi bayan shugaban Amurka baƙar fata a farko sun biyo bayan doguwar tafiyar da ya daɗe yana yi ne a siyasa.

A shekarar 1972 ne aka fara zaɓarsa a matsayin sanata daga yankin Delware, inda ya yi ta riƙe mukamin har karo shida.

Ya tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 1988 amma sai ya janye bayan da ya yarda cewa ya saci wani jawabi daga shugaban ƙasa na wancan lokacin na jam'iyyar Labour, Neil Kinnock.

Tsawon lokacin da ya shafe a kujerar dan majlisar dattawa a baban birnin ƙasar ya bai wa masu suka isassun hujjojin da suke sukarsa da su.

A can farko-farkon rayuwarsa ta siyasa, Mista Biden ya goyi bayan dubbai masu nuna wariyar launin fata, wajen ƙin amincewa da umarnin da kotu bayar na tsarin samar da motar makaranta ta ɗaukar ɗalibai mai ɗaukar kowa da kowa.

Sannan a matsayinsa na shugaban Kwamitin kula da harkokin Shari'a na Majalisar Dattawa a 1991, ya jagoranci zaman tabbatar da Clarence Thomas a matsayin babban alkalin Kotun Ƙoli, kuma an caccake shi a kan yadda ya yi wasarere da batun zargin da Anita Hill ta yi na zargin lalata da ita da ta ce Clarence ya yi.

Mista Biden kuma ɗan gani kashenin wani ƙudurin doka ne na 1994 wanda masu ra'ayin kawo sauyi dama a yanzu ke ganin dokar tana sa ana yanke wa mutane dogon wa'adi na hukunci da kuma ɗaure mutane da dama a kurkuku bisa ƙanƙanin laifi.

Waɗannan abubuwan da ya yi a baya wasu na ganin bai dace da zama a tsarin jam'iyyar Democrat ta wannan zamanin ba.

Rasa masoya

Mr Biden ta yi ta cin karo da wasu jarrabawowi da suka shafi rayuwarsa.

A shekarar 1972, jim kaɗan bayan da ya yi nasarar a zaɓensa na farko a matsayin sanata, matarsa ta fari Neilia da ƴarsa Naomi sun mutu a wani hatsarin mota.

Ya yi fice sosai bayan da ya sha rantsuwar kama mulki a matsayinsa na sanata a karon farko daga asibiti inda ɗansa da ya tsira daga hatsarin Beau yake jinya.

A shekarar 2015, Buau ya mutu sakamakon cutar kansar ƙwaƙwalwa a lokacin yana da shekara 46. An yi ta kallon ɗan nasa a mstayin wani tauraro mai tasowa a siyasar Amurka, ya kuma ƙuduri aniyar tsayawa takarar gwamnan jihar Delware a 2016.

Mahaifin ya goyi bayan takarar ɗan nasa tare da ba shi ƙwarin gwiwar sake tsayawa takara, kuma a lokacin yaƙin neman zaɓe ya bayar da misalai da iftila'in da ya same shi ya bayyana dalilin da ya sa tsarin kiwon lafiya - babbar manufarsa da yake son cimma - ke da muhimmanci a gare shi.

Mutuwar Beau ta sa Mista Biden ya samu goyon baya da tausayawa daga mutane, inda suka fito da irin ƙarfin gwiwa da ƙwazo yake da shi: hakan ya ƙara fito da wata martabarsa a matsayin mutumin da ya damu da iyalinsa sosai.

To sai dai duk irin karsashin da ake ganin yana da shi ba a rasa ƴan matsaloli nan da can.

Bayan da ya tsaya takara a 2020 an zarge shi da yadda yake yawan haɗa jikinsa da mata bayan ɓullar wani bidiyo a matsayin shaidar hakan.

Wadannan hotonan sun sa wasu sun daina ɗaukarsa a matsayin mutumin da a baya suke ganinsa tamkar mumini.

Duk da haka dai Joe Biden ba shi da kwaramniya, salon yaƙin neman zaɓensa ya taimaka wajen nasararsa - wani lokaci na nasara a tsawon gwagwarmayar siyasarsa.

Mista Biden zai zamo shugaban Amurka na 46, bayan kammala sauraron duk wasu ƙararrakin zaɓe.

Zai cika shekara 78 a duniya a lokacin rantsar da shi a watan Janairu - shi ne shugaban ƙasa mafi yawan shekaru da aka taɓa samu a ƙasar.