'Na yi matuƙar farin ciki da aka sanya wa kunama sunana'

Kunama

Asalin hoton, Kovařík/Lowe/Elmi

    • Marubuci, Daga Damian Zane
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Idan da a ce za ka yarda a sanya wa wata halitta sunanka, ba makawa ba za ka so a sanya wa kunama sunanka ba, sai dai ba haka abin yake ba ga Ahmad Ibrahim Awale, domin shi yana ganin cewa hakan zai zama abin faɗakarwa ga sabbin masana kimiyya na Somaliya.

Masanin mai shekaru 66 daga Somaliland ya sami karramawa daga wasu masu bincike uku wadanda suka gano sabbin halittun kunama a yankin, da suka girmama shi saboda bajintar da yake nunawa wajen kare muhalli.

"Yawancin halittun da aka gano a Somalia da Somaliland an sanya musu sunan wani wuri, ko sunan wata shuka ko wata dabba daga Turai ko Amurka,'' kamar yadda ya shaida wa BBC a cikin muryarsa mai daɗi a kan layin gidansa da ke Hargeysa.

"Amma ga matasa da yawa a nan, zai ba su ƙwarin gwiwa su san cewa wannan jinsin an sa masa sunan Awale - bayan kuma Awale dan Somaliya ne, farin cikinsa da samun wannan girmamawar ya fito fili.''

Tun Ƙarni na 19, masu bincike, akasarinsu daga Turai, suka fara binciken yanayin halittu na yankin Somaliya, amma Mista Awale yana son ƙara wa da yawan 'yan Somaliyan da ke laƙantar ilimin dabbobi da na tsirrai.

An gano kunama mai girman santimita 15, wadda yanzu haka ke ɗauke da sunansa a wani wuri mai dausayi kusa da ƙauyen Agabara kimanin kilomita 50 (nisan mil 30) daga arewacin Hargeisa, babban birnin jamhuriyyar da ta ayyana kanta a matsayin Somaliland.

1px transparent line

To sai dai Awale ɗaya ce daga cikin nau'in kunama guda 50 wadanda ke rayuwa a cikin Somaliland, wasu kuma ana samun su ne kawai a yankin Somaliya.

Wannan wata hujja ce da ke nuna wadatar halittu, kama daga kan na tsirrai wadanda ke zaman mafaka ga kunamu, da kuma su kansu dabbobi, sannan akwai aƙalla nau'ikan tsirrai 3,000 waɗanda aka gano.

Wannan adadi na halittun da ake ci gaba da ganowa dai na ci gaba da karuwa, don haka a tsammacin samun karin wasu.

Mista Awale, wanda shi da kansa ya samo wata sabuwar kunama a shekarar 2014, ya ce "wannan ya bayyana sakon cewa ba duk abin da ke zuwa daga Somaliland ba ne ke zaman mugun abu.

Wani waje da aka gano kunaman

Asalin hoton, Ahmed Awale

Ma'anar sunan Awale a harshen Somali shi ne "mai sa'a.

Aloe plant close up

Asalin hoton, Ahmed Awale

'Barazanar gushewa'

Saƙon da Mista Awale ya bayyana game da ci gaban da aka samu na tare da barazana.

Kamar kowane wuri, nau'ukan halittun na fuskantar barazana wasu kuma suna mutuwa.

Sauyin waje daga karkara zuwa birni, da kuma sharar daji na taimaka wa wajen ƙara barazanar gushewar waɗannan halittu da muke magana a kai.

Baya ga hakan matsalar sauyin yanayi ma na ƙara barazanar ɓacewarsu.

1px transparent line

Don aika wannan saƙo ga al'ummar Somaliland, a shekarar 1995 ya taimaka wajen kafa kungiyar Candlelight, da nufin ankarar da jama'a a kan muhimmancin kula da yanayi.

Ya kuma rubuta littattafai da muƙalu, kuma ya bayyana a rediyo da talabijin don ƙara wayar da kan jama'a game da batun.

Mista Awale ya ce ya lura da wasu sauye-sauye a cikin manufofin gwamnati, amma mafi mahimmanci shi ne yadda matasa da dama ke karɓar aniyar hannu bibbiyu.

Duk da cewa an san shi ta hanyar samun kunama mai sunansa, masanin muhallin ya san cewa wannan ba gwagwarmayarsa ba ce shi kaɗai.

'Yan Somaliya na da wata karin magana da ke cewa ''Yatsa ɗaya ba ta wanke fuska.'"