Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matar da ke son mata su daina yi wa hotonsu kwaskwarima a Instagram da Snapchat
- Marubuci, Daga Emma Hallett
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Rariyar hotuna ta zama wata shahararriyar hanya ta sauya hotuna, musamman ma ga wadanda suka damu da nuna tsabarar kyansu a duniyar kafofin sada zumunta.
Wani binicke na baya-bayannan da kungiyar Girlguiding ta gudanar, ya nuna cewa 'yan mata na wallafa hotunansu na dauki da kanki ba tare da sun yi musu kwaskwarima ba.
Kaso 39% daga mutanen da aka tattauna da su 1,473 da shekarunsu suka kama tsakanin 11 -21 suna damuwa da ganin cewa kamanninsu a zahiri ba sa kai yadda suke a hoto ba.
Sakamakon binciken ya nuna irin damuwar da wata mai kwalliya Sasha Pallari, wacce a baya bayannan ta kaddamar da wani maudu'i #filterdrop da nufin ganin mata suna wallafa ainihin kamanninsu a Instagram.
"Kawai na yi tunanin cewa 'shin akwai wanda ya fahimci illar wannan kuwa?'" kamar yadda ta fada, a yayin da take bayani kan yadda ta ga wani babban kamfanin kayan kwalliya na duniya ya wallafa hoton wata shaharriyar mata da aka yi kwaskwarima tana tallata kayan kamfanin.
"Ba na so yara su taso da tunanin cewa ba su da kyau sosai, saboda abin da suke gani a shafukan sa da zumuta."
Matar mai shekara 28 daga Bristol, ta mayar da abin da take sakawa a Instagram zuwa wani "batu a intanet". Ta samu martani da dama, abin da ya sa ta kaddamar da gangamin #filterdrop.
Ta rinƙa tambayar mutane su daura hotunansu da ba a yi wa kwaskwarima ba a shafukansu sannan "su fi fifita su wanene fiye da yadda fuskarsu take".
"Muna son ganin fatun zahiri sosai," a cewarta.
'Wannan yarinyar shekararta hudu kawai'
Malamar makarantar firamare Katie McGrath, ta bibiyi Miss Pallari a shafukan sada zumunta fiye da shekara guda.
Ba ta taba tunanin cewa yadda take duba Instagram da yamma zai shafi aikinta ba, amma ta bayyana yadda abin yake a takaice.
"Kusan karshen kullen cutar korona, na samu wani sakon email daga wasu iyaye suna bayyana damuwa kan sauyawar halayyar 'ya'yansu," A cewar Miss McGrath.
"Sakon email din ya ci gaba cewa yarinyarsu tana da matsala da kamanninta. Sai na yi tunani. Shekarar yarinyar hudu kawai.
"Lamarin ya bata min rai sosai, a ce karamar yarinya kamar wannan wai tana lura da yadda kamanninta suke."
Malamar mai shekara 29 daga yankin Cwmbran, a kudancin Wales ta gano cewa yara suna kallon yadda ake koyar da kwalliya a shafukan sada zumunta.
"Ta yi min magana kan yadda ba ta son fuskarta ba tare da ta yi kwalliya ba, sannan tana so tsaya sauya launin gashinta.
"A nan ne gangamin #filterdrop ya zo ya taimake ni.
"Sai na ga ya kamata na fara yi wa yara magana kan yarda da kansu."
Yarinyar mai shekara hudu sai ta tambayi Miss McGrath me ya sa take yin kwalliya kullum - tambayar da ta kasa amsawa.
Da mako ya kewayo, sai ta tafi makaranta "ba tare da ta yi kwalliya ba".
Miss McGrath na daya daga daruruwan matan da suka amsa kiran Miss Pallari da labaransu.
Sauyi na Hakika
Miss Pallari na fatan cewa gangamin na ta ya samar da sakamako uku: A samar da wani tsari na tallata kaya, ta yadda shahararrun mutane sai sun bayyana cewa ko sun yi kwalliya ko kuwa; a cire rariyar tace hotuna a Instagram; sannan ta ga karin hotunan mutane na ainihi a Instagram".
Ba wai tana so ta ga an kawo karshen rariyar hotuna ba, sai dai tana so ne a cire rariyar yi wa fuska kwaskwarima.