Coronavirus: Yadda Musulmai ke shirin azumi lokacin kulle a Burtaniya

An wallafa

A wurin irin su Dakta Kiran Rahim, Ramadan din bana zai zama na daban, saboda sa'o'in da take kwashewa da takunkumin fuska mai zafi wajen kula da mutanen da ke fama da cutar korona da ke sashen kulawa ta musamman.

Ana kai yaranta ne wajen mahaifiyarta inda iyalan gidan ke cin abinci tare, ko kuma su fita zuwa cikin gari inda ake sayar da abinci don haduwa da 'yan matansu su sha ruwa tare.

A wannan shekarar za ta rika komawa gida ne daga asibitin Jami'ar Homerton dake arewa maso gabashin Landan, kuma zata rika komawa wajen mijinta da 'yaranta maza biyu a matukar gajiye - ko da kuwa a ranar da baza ta yi azumi ba saboda yawan ayyukan da take yi.

Watan Ramadan, wanda a wannan shekerar zai kama a yammacin Alhamis, ana daukarsa a wata ma fi tsarki cikin watannin Addinin Musulunci kuma cikinsa Musulmai ba sa ci ko shan wani abu da rana har sai rana ta fadi.

"Irina da yawa na zabar su hakura da azumi lokacin da muke aiki a sashen masu bukatar kulawa ta musamman," Dakta Rahim.

"Akwai wahala wajen amfani da kayan kariya, za ka iya sa'a daya ne ko biyu kan ka samu ka cire su ka sha ruwa."

Ta ce abokan aikinta na kungiyar likitoci ta Burtaniya sun tambayi shawarar malamai wadanda suka ce za ka iya ajiyewa idon kana aiki da yawa ko kuma aikinka mai mahimmanci ne.

Sauki ne amma dai babu dadi saboda ina son yin azumi," in ji Dakta.

Amma wasu da ke sashen kwararru za su sha nasu ruwan ne su kadai lokacin hutunsu na aikin sa'a 12 da suke, sabanin yadda suka saba a baya.

Duka wata damar daukar hutu cikin Azumin Ramadan kamar yadda wasu ke yi, ta kulle tun da aka fara wannan dokar hana zirga-zirga.

Da kuma wannan dokar da aka kakaba har zuwa 7 ga watan Mayu, Dakta Rahim mai shekara 33 ta ce, tana ganin bikin Sallar Idi da ake a karshen Ramadan da yiwuwar a yi shi a wannan yanayi.

"Ramadan a wani lokacin yana da wahala amma bikin sallar Eid na saukaka komi," ta ce. "Ba ni da tabbas ko za mu yi bikin salla karama a wannan shekarar."

Zai kasance na daban amma ta wasu hanyoyin zai zama na kara tsoron Allah. Muna rayuwa cikin wani matsin rayuwar duniya amma da yawa daga cikin mu na nuna jajircewa wajen yin abin da muke so.

"Har yanzu za mu iya aje abinci kan teburi. Akwai mutane da yawa da ba su da aiki ko kuma wadanda suke neman rufawa kansu asiri.

Kungiyar Musulmai ta Burtaniya ta ja kunnen mutane cewa za a fuskanci abubuwa na daban tare da shawartar masu ibada su zauna a gida.

Yayin da ake kulle masallatai ake kuma raba iyali, sau da dama har acikin gidajensu, Musulmai ba za su samu damar shan ruwa da yin sallah tare - wanda na cikin abubuwa masu muhimmanci a Ramadan.

Amma akwai abubuwan alkhairi da yawa a Ramadan, wadanda ke umartar al'umma da su rika sadaka, wadanda suka bukaci Musulmai su rika taimakawa mabukata a yankunansu.

A Stanmore, da ke arewa maso yammacin Landan Masallacin Hujjat na raba kayan buda baki a cikin wata kura, ana samar da samar da abincin sama da mutum 150 tun daga farko har karshen Ramadan.

'Yan sa kai ne ke raba kayayyakin da masu ba da taimako ke aikowa na abinci, kuma gidajen abincin yankin ake bai wa kwantaragin yin hakan.

"Ina ganin mutane na iya kokarinsu," in ji Asim Nurmohamed, daya daga cikin shugabani a masallacin,"Ina ganin ma'aikatan sa kai 200 cikin sa'a 48 ba karamar nasara ba ce.

Muna ciyar da mutane 1,500 ne a cibiyarmu a tsawon watan kuma wasu mutanen sun dogara ne a kanmu."

Fatan shi ne a isa gidan 200 kowanne daren Ramadan, yayin da a kalla mutum 1,000 sun yi rijista suna nuna sha'awarsu.

Kazalika cibiyar tana bai wa kungiyar Harrow Council aikin raba abincin ga wadanda ke bukata da kuma taimakon da ake samu daga wajen al'ummar Musulmai, in ji Nuemohammed.

Kamar dai sauran masallatai Masallacin Hujjat na gabatar da ajujuwan karatu da kuma maganganun malamai kai tsaye har zuwa karshen watan Ramadan.

Kungiyar Ahmadiyya wata kungiyar da ke aikin ba da agaji a Burtaniya, na gabatar da wani ajin motsa jiki da kuma al'amuran da suka shafi rayuwa da kuma salloli yayin azumin, amma suna ta fatan kai wa ga yankunan Musulmai da yawa cikin Ramadan.

Abdul Lodhi, daraktan walwala ne na kungiyar ya ce, ana samar da wadataccen abincin da ake gayyatar mutane su zo su ci su kuma ko yi abubuwa akan Ramadan da kuma Addinin Musulunci, amma suna fatan a kara samun mutane na da ke bibiyarsu a intanet.

"Wani abu daya da muke fatan zai taimaka a wannan lokacin da ake fama da rashin tabbas shi ne, darasin da ka koya daga azumi da kuma yadda za ka yi amfani da shi ya yi wannan hana zirga-zirgar," In ji Abdul Lodhi,

"Yanayi ne iri daya da lokacin da kake azumi. Ba kawai magana ce ta yunwa ba, akwai wasu karin abubuwan da yawa da ake bukatar ka yi.

"Bai kamata mutum ya rika zancen banza cikin azumi, kallon abubuwan da basu dace ba.

"Za ka zama cikin fushi ka yi ta fada to amma bai kamata ka rika sakin baki ba. Kowa yasan yadda ake ji ina mutum na fama da yunwa.

"Ina ganin wannan juriyar wani abu ne mai mahimmanci da ya kamata mutane su rika amfani da shi."

Imam Sabah mai shekara 26 mazaunin Landan, ya ce Ramadan zai zama da wahala a wajen masu ibada, wanda kuma hakan ba zai yuyu ba a wannan lokacin, zai rika gudanar da ajin da ya ke yi da kuma sallarsa a Instagram.

"Ramadan lokaci ne na neman kara kusanci zuwa ga Allah kuma dukkanmu muna da cikakken lokain da za mu yi hakan a wannan lokaci," ya kara da cewa.

Ya kara da cewa, "Amma sako mafi muhimmanci shi ne kowa ya zauna a gida kar ayi kokarin ziyarar iyali ko zuwa masallaci, wadanda za su kasance a kulle,