Coronavirus: Hausawan da ke gaba-gaba a yaki da cutar a Burtaniya

An wallafa

Hausawa kuma 'yan Najeriya na daga cikin dubban likitoci da ma'aikatan lafiya daga Afirka da ke sahun gaba-gaba wajen yaki da annobar korona a Burtaniya.

Dr Umar Jibrin Madigawa babban likita ne mai tiyata a Burtaniya kuma dan asalin jihar Kano ne, inda ita kuma Dr Hadiza Gachi ta fito daga jihar Katsina duka a Najeriya.

Likitoci da ma'aikatan jinya da sauran ma'aikatan asibiti fiye da 60 ne dai suka mutu sakamakon cutar korona a Burtaniya, ciki har da Dr Alfa Sa'adu dan asalin jihar Kwara a Najeriya.

A yanzu dai likitoci masu karbar mutanen da ke da cutar korona a kasashen Turai da Amurka na rubuta wasiyya sakamakon rashin tabbas na kwayar cutar.

Ko yaya wadannan likitoci biyu Hausawa ke yin aikin nasu?

Dr Hadiza Gachi:

Dr Hadiza Sulaiman Gachi, babbar likita ce a asibitin George Elliot da ke Burtaniya, inda ta ke bangaren masu kula da cutar korona, na jimamin halin da iyaye da 'yan uwanta ke ciki a jihar Katsina, inda ake da mutum 6 masu dauke da cutar.

Dr Hadiza ta ce "Muna ganin tashin hankali yadda ake kawo mana masu dauke da cutar musamman maza 'yan shekara 40 zuwa sama kuma da dama na mutuwa.

Ta kara da cewa "Ina fargaba saboda yadda muke ba su kula kuma mun san mu ma za mu iya daukar wannan cutar."

Sai dai Dr Hadiza ta ce suna duk iya bakin kokarinsu na ganin ba su dauki cutar ba, ballantana su shafa wa 'ya'yansu da ke gida.

"Idan na shiga mota ina goge sitiyari da kujeru da sauransu sannan ba na yarda 'yata ta yi mani sannu da zuwa idan na koma gida ta hanyar runguma saboda duk lokacin da na isa gida, ina wucewa ban daki ne kai tsaye domin tsaftace jikina kafin mu hadu", in ji Dr Hadiza Gachi.

A cewarta "'Yartawa na yawan shiga cikin firgici idan ta ji an ce likitoci sun mutu."

Dangane da halin da mahaifanta da 'yan uwanta ke ciki a jihar Katsina, Dr Hadiza ta ce "na shaida wa mahaifiyata cewa ta daina fita - ba zuwa biki ko suna ko gaisuwa da ma kasuwa."

To amma kwararriyar likitar ta yi kira ga kasashen Afirka musamman Najeriya cewa ya kamata a tallafa wa jama'a da abinci da kudi kafin a kulle su sakamakon dokar hana zirga-zirga.

"Kasashenmu na Afirka ba za a taba hada su da na nan Turai ba saboda haka jama'a na bukatar tallafi.", in ji Dr Hadiza.

Dr Umar Jibrin Madigawa:

Dr Umar ya ce dole ne akwai fargaba ga duk mutumin da yake ganin halin da masu cutar suke da yadda take zama ajalinsu.

Domin haka ne ya ce "muna aiki ne bisa kariyar ubangiji" kasancewar dole ne likita ya ceci ran jama'a.

"Muna ganin yadda dubban jama'a ke mutuwa kuma ina mamakin yadda a gida Najeriya mutanenmu ke yi wa wannan cuta kallon almara", in ji Dr Madugawa.

"Tabbas a kwai wannan cuta kuma ya kamata jama'a su kiyaye. Su bi ka'idodjin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta shimfida kamar gudun shiga cunkoso da yawan wanke hannu."

Daga karshe Dr Umar Farouk Madigawa ya tabbatar wa da 'yan uwansa na Arewacin Najeriya cewa cutar korona ba ta da magani, inda ya nemi su dauki matakan rigakafi.

Duk da cewa wadannan likitoci guda biyu, Dr Umar Madigawa da Dr Hadiza Gachi na Burtaniya ne inda suke fagen fama na a yi rai ko a mutu sakamakon wannan annoba ta korona, amma zuciyarsu na gida Afirka.

Hukumar Lafiya ta Duniya dai, WHO ta yi gargadin cewa nahiyar Afirkar ka iya zama cibiyar cutar korona nan gaba.

An samu karuwa sosai dangane da mutanen da ke kamuwa da cutar a nahiyar a makon jiya.

Mutum kusan 1,000 ne suka mutu sannan kimanin mutum 18,000 suka harbu da cutar ta korona a Afirka ya zuwa yanzu, ko da yake wannan adadi bai kai na Turai da Amurka ba.

Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniyar ta ce cutar na bazuwa daga manyan birane zuwa wasu yankuna a nahiyar.

Ta kara da cewa Afirka ba ta da isassun na'urorin da ke taimaka wa masu dauke da cutar korona yin numfashi.