‘Yan fashin Lagos: Gaskiyar abin da ya faru

- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo & Ajoke Ulohotse
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Daruruwan 'yan daba, mafi yawansu matasa da shekarunsu ba su haura 20 ba, da ke tserewa 'yan sanda a jihohin Najeriya biyu da aka sa wa dokar hana zirga-zirga sun sanya fargaba a zukatan mazauna jihohin, inda suka nuna masu cewa sun shirya yi masu fashi da makami.
'Yan sanda sun ce 'yan dabar sun cika burinsu na son tada wa mutane hankali.
Mazauna sun kakkafa shingaye da tayoyin da suka cinna wa wuta a unguwannin da ke kan iyakar Legas da jihar Ogun, bayan da suka kafa kungiyoyin 'yan sa-kai don kare kansu daga 'yan fashi da makamin da suke tunani za su far masu.
Tsawon kwanaki, gungu-gungu na mazauna unguwannin nan - yara da manya, kuma mafi yawansu maza - sun yi tsaiwar dare a titunan rike da adduna da kwalabe.
Sun shirya wa harin da ba a kai ba kwata-kwata.
An yi ta yada jita-jitar cewa wata tawagar 'yan fashi da makami ta mutum 200 da ke shirin kai farmaki.
Amma 'yan sanda sun shaida wa BBC cewa yaudara ce kawai da 'yan bangar suka shirya don kawai su daga wa mazauna hankali kuma mutane su taimaka masu ta hanyar yada labarin a shafukan sada zumunta.
Sai dai 'yan sandan sun dage a kan cewa babu wanda aka kai wa hari.
Ranar Litinin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da kara wa'adin dokar hana fita da zirga-zirga a jihohi uku a kasar, ciki har da babban birnin kasar Abuja, don rage yaduwar cutar korona, amma bai yi magana kan yanayin tsaro a jihohin ba, inda mazauna ke fargabar cewa matsin tattalin arzikin da dokar za ta janyo ya yi sanadiyyar karuwar aikata manyan laifuka.

Asalin hoton, Other
Ya aka fara yada jita-jitar?
Wasu hotuna da bidiyo sun bayyana a shafin Twitter inda suka nuna mazauna na dakon hare-haren ranar Alhamis da maudu'in #OgunUnrest da #LagosUnrest.
Amma babu wata shaidar da ta nuna cewa 'yan fashi da makami sun kai hari unguwannin, a cewar 'yan sanda.
Rahotannin farko-farko sun nuna cewa an kai hare-hare a unguwannin Agbado da Sango da Ijoko a jihar Ogun amma suke kan iyakar Legas.
A shafukan sada zumunta wasu mazauna sun yi ikirarin cewa sun ji harbin bindiga kuma wasu sun ce sun ga mutane suna shiga wasu gidaje da karfi da yaji kuma a wasu lokutan ma sun yi wa masu gidan rauni.
Wannan mai amfani da shafin Twitter din ta ce ba ta iya yin bacci ba saboda "an yi fashi a unguwarta."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Wannan bidiyon ya nuna mazauna wata unguwa suna wasa addunansu kuma suna "shirya wa yaki".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya shaida wa BBC cewa sun samu sama da kiran waya 300 kan "hare-haren bogi" ranar Asabar.
"A wani karo, wani ya kira mu ya ce mutane bakwai sun mutu amma da 'yan sanda suka isa wurin babu komai.
"Mai kiran wayar na can wani wuri mai nisa daga wurin da yake ba da rahoto a kai," a cewarsa.
Ya ce rikici ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan daba biyu a jihar Ogun bayan da daya daga cikin shugabannin kungiyoyin ya mutu a wani rikici. Wannan ya janyo aka kama mambobin kungiyar 150 yayin da daruruwansu suka tsere zuwa jihar Legas.

Jita-jitar fashi da makami ta yadu zuwa Legas a ranar Juma'a kuma akwai wasu hotuna da bidiyo na intanet, inda wasu ke nuna 'yan dabar jina-jina da fararen hula da suka kama su suna zargin su da zama 'yan fashi.
Abubuwa sun kara tabarbarewa ranar Lahadi inda aka samu rahotannin cewa an kai hari da rana a unguwar Ogba da ke Legas, wata unguwa da mafi yawan mazaunanta masu hali ne.
An yi fashi da makami?
'Yan sanda sun ce ba a yi fashi da makami ko sau daya, akalla dai ba kamar yadda ake ta yayatawa ba a shafukan sada zumunta.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Elkana Bala ya shaida wa BBc cewa sun kama 'yan daba 100 da suka shiga Legas daga jihar Ogun bayan karawar da suka yi a tsakaninsu.
Ya ce 'yan dabar sun sanya fargaba ta hanyar aika sakonni don su tsorata mutane.
"Sun san da wahala su kai hari unguwar da ke da tsari don haka sai suka yi kokari rikita mazaunan tukuna," a cewarsa.
We heard that there were some guys robbing around the area, so there was panicking."

Ya ce kungiyoyin 'yan sa-kai sun kara kambama matsalar ta hanyar daukar makamai da kona tayoyi, inda wasu mazauna suka rika tunanin su ne 'yan fashin.
Me mazauna suka ce?
A shafukan sada zumunta, martanin da aka mayar ya zama abin dariya, inda wata mazauniya daya daga cikin unguwannin ta bayyana cewa ta shiga kejin karenta ta boye wa 'yan fashin.
Daga baya ta goge sakon inda ta ce wasa take yi.
Wasu sun ce 'yan fashin sun je har kofar gidansu ko kuma gidajen makwabtansu kuma 'yan sanda sun ki amsa kiransu.
A tituna kuwa, ko ina jita-jitar ake ta yadawa. Kowa ya ji labarin hare-haren da ake cewa an kai a wasu titunan, amma ba a kai a nasu ba. Babu wanda ya ga ana fashin a zahiri.

Asalin hoton, Getty Images
Jamiu Ayofalaji, wanda ke zaune a unguwar Ogba da ke Legas ya ce ya ji karar harbin bindiga kuma ya tattara sauran mazauna unguwar su kona tayoyi don sanar da "'yan fashin cewa ba bacci muke yi ba".
Ya ce bai ga wasu 'yan fashi ba a kwanaki ukun da ya yi tsayuwar dare.
Deji Francis ya ce shi ma ya ji karar harbin bindiga kuma "wasu suna fashi a unguwar don haka aka shiga fargaba," amma bai ga komai ba.
"Mun ji daga majiya mai karfi cewa 'yan dabar sun shiga wani titi a kusa da mu sai muka fito don mu kare kanmu," in ji Olajide Boladale a unguwar Ogba, yayin da wani gungun maza ya dabaibaye shi.
"Mun rike sanduna da sauran abubuwa don mu kare kanmu," a cewarsa.

Su waye 'yan daban?
Legas ta dade tana da matsalar 'yan daba da ake yi wa lakabi da 'agberos' ko kuma 'area boys', wadanda ke karbar kudi da karfin tsiya a hannun 'yan kasuwa da mazauna.
Hukumomi sun kau da kai daga kanana-kananan sace-sacen da suke yi, a jihar da ke fama da yawan matasa marasa aikin yi.

Asalin hoton, Getty Images
Amma ana zargin cewa wani nau'i na 'yan daba ya shirya "hare-haren" na baya-bayan nan ne da sigar 'yan bindiga masu tsari da shugabanci.
'Yan dabar, da ake kira 'yan kungiyar asiri a Najeriya saboda yadda suke shigar da mutane kungiyar ta hanyar tsaga jiki da amfani da tsafi, na neman su samu karfin iko kan wasu yankuna sannan su aikata manyan laifuka.












