Coronavirus: Masu yi wa gawa wanka na sa-kai a Iran

Asalin hoton, Hawzah News Agency
- Marubuci, Daga Behrang Tajdin da Louise Adamou
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Mutane na sa kansu aikin yi wa gawarwakin da ake tarawa a dakin ajiye gawa wanka, inda rahotanni ke nuna cewa wasu gawarwakin kan yi kwana biyar zuwa shida ba a yi masu wanka ba.
An yi masu lakabi da 'Matan Korona". Masu aikin sa-kai a birnin Qom na Iran na aikin da kwararru da yawa ke tsoron yi - wanke gawarwakin mutanen da cutar korona ta kashe, kamar yadda Musulunci ya tanada.
Iran ce kasar da ta fi kowacce yawan mutanen da suka mutu dalilin cutar a Gabas Ta Tsakiya.
Zai yi matukar wahala a samu sahihan bayanai daga kasar, amma wasu bayanai da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna cewa dakunan ajiye gawarwaki a kasar sun cika makil.
A wani bidiyo da aka wallafa a intanet, wani ma'aikacin dakin ajiye gawa ya nadi hotunan gawarwaki a jejjere a kasa kafin a yi masu wanka. Ya ce wasu mutanen sun kai kwana biyar zuwa shida da mutuwa.
Bayan da aka yi ta yada bidiyon, hukumomi sun mayar da martani nan da nan.
Daga farko, an kama shi sannan aka mayar da hankali wajen dakile bacin ran da ya taso dangane da wulakanta gawarwakin wadanda suka mutu dalilin Covid-19.
Yayata batun 'Matan Korona' na daya daga cikin hanyoyin da aka bi wajen yin hakan.
An buga labarinsu a shafukan intanet da yawa, inda aka nuna su a matsayin mata masu jarumta da ke yi wa gawarwaki wankan karshe kamar yadda musulunci ya ce, wato wankan gawa.
A bayan rigunansu an rubuta kalamai haka: 'Idan ba ka da jarumtar zaki, ba za ka iya shiga fagen soyayya ba'.

Asalin hoton, Hawzah News agency
A shari'a, dole ne a bisne mutumin da ya mutu.
Amma kafin a bisne, shari'a ta bukaci a wanke gawar da ruwa sau uku.
Wannan shi ake kira Ghosl-e Meyyet wato wankan gawa. Ana zuba ganyen magarya a ruwan farko.
A karo na biyu kuma sai a sa kafur, daga karshe kuma sai a wanke gawar da ruwa kawai.
Bayan wankan sau uku, sai a rufe gawar da likkafani sannan a sallace ta a kai ta makwancinta.
Ko ya wannan tsarin zai shafi masu yi kan wadanda cutar korona ta kashe?
A farkon annobar, shawarwarin da aka bayar na da rikitarwa - a fadin duniya da kuma a Iran.
Daga farko gwamnati ta bada shawarar cewa a daina yi wa gawa wanka da ruwa, inda ta ce a rika yi masu taimama kawai.
Amma a farkon watan Maris, shugaban kasar ya ce dole ne a yi wa gawarwakin cutar korona irin jana'izar da ake yi wa kowa; a wanke, a rufe da likkafani kuma a sallace ta.

Ya kara da cewa dole ne wadanda za su yi jana'izar su kula da dokokin kare lafiyarsu.
Shin wadanne ne dokokin?
Duk da cewa ba a tunanin ana iya daukar cutar korona daga jikin gawa, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayar da shawarar 'daukar matakan kariya' saboda har yanzu akwai abubuwa da dama da ba a sani ba dangane da cutar.
WHO ta bukaci masu aiki da gawarwaki su sa kayan kariya na musamman har da safar hannu da takunkumin rufe fuska.
A Italiya, misali, hukumomin lafiya sun ce duk da cewa idan mutum ya mutu ba ya iya yada cutar, amma tana iya rayuwa a kan kayansa - don haka ana nannade gawa nan take kuma ana haramtawa iyalai ganin gawar 'yan uwansu.
Duk da hadurran da ba a sani ba, Matan Korona na ci gaba da aiki ba dare ba rana a Iran.
Sun kunshi tawagogi uku, ko wacce na aiki tsawon sa'o'i bakwai.
Suna addu'o'i da kasidoji na Musulunci don saukaka masu aikinsu. Sun ce idan suka gama yi wa gawar matasa wanka suna addu'o'insu da karfi don kara wa kansu karfin gwiwar aikin da ke jiransu a gaba.

Asalin hoton, Instagram
Kuma ba su kadai ne ma'aikatan sa-kai a Iran ba - a makarantar koyon addini a Mashhad, dalibai na yi wa gawarwaki wankaa lokacin cin abincinsu na rana.
Fargaba da Alkalumma
Ba wai fargaba a tsakanin ma'aikatan wurin ajiyar gawarwaki ce kawai ke janyo matsalar tara gawarwakin ba tare da jana'iza ba, yawan mutanen da suke mutuwa a kasar ne.
Alkaluman da hukumomi suka fitar sun ce sama da mutum 60,000 ne suka kamu da cutar kuma kusan 4,000 sun mutu ya zuwa 8 ga watan Afrilu.
Amma wasu masu bincike 'yan Iran a amurka na ganin alkaluman sun fi haka girma.
Biyu daga cikinsu su ne Hazhir Rahmandad, wani farfesa a Jami'ar kimiyya ta Massachusetts Institute of Technology da navid Ghaffarzadegan, farfesa daga Jami'ar Kimiyya ta Virginia.
Maimakon dogara da alkaluman gwamnati kawai, sun ce sun kirkiri wani tsarin kwaikwayon yadda cutar ke yaduwa.
Tsarin ya kunshi bayanai kan 'yan Iran matafiya da aka gano suna dauke da cutar a lokacin da za su shiga wasu kasashe, da kuma wasu alkaluman kungiyoyin lafiya don gano abin da suka ce alkaluman da suka fi sahihanci.
Sun yi kiyasin cewa, zuwa 20 ga watan Maris, sama da mutum 15,000 sun mutu kuma yawan masu dauke da ita na iya kaiwa kusa da miliyan daya.
Alamomi a doron kasa
Yayin da wannan bincike guda ne kuma ba lallai mu taba sanin girman barnar da annobar ta yi a Iran ba, ana iya ganin wasu alamomi da ke nuna yawan mutanen da suka mutu a bisne a cikin kasa.

Asalin hoton, Mehr news agency
Maimakon bisne mutane kowanne a kabarinsa, ana hada gawarwaki da dama a wasu ramuka masu tsawo.
Wani likita a yankin arewa na Mazandaran - wanda ba ya so a bayyana sunansa - ya bayyana wa BBC cewa an tura kwararru kan kariya don sa ido kan yadda ake sa likkafani da bisnewa da rufe gawarwaki da lemun tsami, wanda jami'ai suka ce na taimakawa wajen kashe kwayoyin cuta kuma yana hana cutar yaduwa.
Likitan ya ce duk da cewa takardun shaidar mutuwa na nuna cewa sanadin mutuwar bugun zuciya ne ko mura, tura wadancan kwararru da aka yi na nuna cewa akwai yiwuwar cutar korona ce ta kashe mutanen.
Wasu iyalai sun ce ba su da masaniya kan inda gawarwakin 'yan uwansu suke. An ce masu za a ba su duk wani bayani da zarar an shawo kan annobar, don su kai wa kaburburan 'yan uwansu ziyara.
A halin yanzu, shugabannin addini na kokarin kwantar wa 'yan uwa hankali suna cewa ana kula da 'yan uwansu yadda ya kamata kuma ba a wulakanta su sannan ana yi masu jana'iza daidai da yadda addinin Musulunci ya ce a yi.











