Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus na iya zama silar durkushewar Gabas Ta Tsakiya
Yaki da cuta sun hadu sun samar da bala'i a tarihin Gabas Ta Tsakiya, kuma yayin da coronavirus ke shiga yankin a hankali, barnar da za ta yi ga al'umma da siyasa na iya yin muni matuka.
Kwayar cutar ta riga ta shiga yankin. Isra'ila- kasar da ke da tsarin lafiya na zamani kuma na gani na fade, sannan take da karfin aiki da arzikinta- a yanzu ta fara shiga halin ka-ka-ni-ka-yi kan illar da coronavirus za ta yi mata.
Tana fuskantar irin matsalolin da Yammacin turai da Amurka suka fuskanta. Haka ma Iran , wadda annobar ta yi mata mummunan kamu. Tana fusknatar mace-mace, kuma wasu masu sharhi ma na ganin cewa ba ta fadin gaskiyar yawan mutanen da suka mutu.
Sai dai Gabas ta Tsakiya na da wasu matsaloli na daban da ka iya kara mata girman matsalar. Dokokin addini, misali, na taka muhimmiyar rawa a rayuwar 'yan yankin da yawa.
Irin wadannan al'ummun kan fuskanci sauyi sannu a hankali.
Don haka, bai zo da mamaki ba yadda Isra'ila, wadda al'umarta mai tsattauran ra'ayin addini ta Haredi ta bata lokaci kafin ta fara daukar matakan barin tazara kuma cutar ta yi barna a tsakanin al'umar sosai. Mabiya mazhabar Shi'a da suka koma kasar daga Iraki da Syria sun koma dauke da cutar covid-19, inda hakan ya nuna cewa balaguro irin wannan na yada cutar.
Kasashen da suka gaza
Lallai ne wannan ya fi karfin annobar cuta kawai domin ko ya shafi tattalin arziki. Rikicin mai tsakanin Saudiyya da Rasha ya janyo farashin mai ya fadi kuma wannan ya jefa tattalin arzikin yankin cikin matsi.
Gwamnatocin Gabas ta Tsakiya ba su da arzikin da mutane za su zuba hannun jari a ciki don biyan albashi da tallafa wa kamfanonin da ke daf da durkushewa.
Sannan kuma, rikicin da ke ci gaba a Gabas ta Tsakiya da dubban mutanen da yaki ya daidaita ne babbar matsalar yankin yayin da annobar ke ci gaba da yaduwa.
Za a iya cewa Syria da Libya da Yemen kasashe ne da suka durkushe saboda arzikinsu bai kai ya kawo ba kuma ba su da tsarin lafiya mai karfi.
Lallai ne a yankunan 'yan tawaye a Syria, an kai hare-hare a asibitoci da sauran cibiyoyin lafiya daga gwamnati da kawayen Rasha.
Don haka, babu mamakin cewa kungiyoyin agaji na kira da a gaggauta kai dauki kuma kasashen duniya su yi wani abu a kan yakin.
Cutar za ta fi yaduwa
Gwamnatin Syria ta sanar da mutum na farko da ya kamu da coronavirus ranar 23 ga watan Maris. Kawo yanzu, babu wanda aka ce ya kamu da cutar a yankin Idlib mai fama da yaki.
Amma mai yiwuwa an samu hakan ne saboda rashin kayan gwaji.
Kungiyar agaji ta Medicines Sans Frontieres (MSF) ta yi gargadin cewa "cutar na iya yaduwa da sauri a yankin, musamman a sansanoni, inda mutane da yawa ke rayuwa a cunkushe kuma a yanayi na kazanta."
Cibiyoyin lafiya na daf da durkushewa inda suke fama da wadanda suka samu raunuka a yakin.
MSF ta ce ba yadda rayuwar wadanda suka rasa muhallansu a Syria ne kawai damuwarsu ba, ta ce har ma da halin da yawan 'yan gudun hijirar da suka tsere zuwa sansanoni a Turkiyya.
Karin labaran da za ku so ku karanta
Kungiyar agaji ta Refugees International ta fitar da wani rahoto mai tsawo kan mawuyacin halin da wadanda rikicin ya daidaita a fadin duniya suke ciki.
Ita ma ta yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta yin wani abu. Mataimakin shugabanta, Hardin Lang, ya ce "a wannan lokacin annoba, dole ne mu tuna da mutanen da ke mawuyacin hali."
"Gwamnatoci," ya ce "sun mayar da hankali wajen kare al'ummominsu kuma wannan dai-dai ne. amma dole duk wani taimako da za a yi a lokacin covid-19 a sa kowa da kowa a cikinsa idan har ana so ya yi aiki."
Ya ce "muna manta wa da mutane miliyan 70 da aka tilastawa rabuwa da muhallansu. Daukar matakai don kare su shi ne ya fi dacewa."
Gwamnatocin da ba sa aiki
Sai dai yayin da kasashen da suka ci gaba ke fama kuma tattalin arzikinsu ke cikin mawuyacin hali, tare da hana zirga-zirgar jiragen sama a hanyoyi masu muhimmanci, samar da taimako zai yi wahala. Kuma matsalar Gabas ta Tsakiya na da girma.
Kungiyar Refugees International ta ce a kalla 'yan gudun hijira da mutanen da rikici ya daidaita miliyan 12 ne ke zaune a Iraki da Syria da Lebanon da Turkiyya.
Ana iya saurin shiga ta iyakoki a fadin Gabas ta Tsakiya inda 'yan gudun hijira da 'yan ci rani da wasu mutanen suke yawan bin hanyoyin da ba na ka'ida ba.
Rashin wadatattun asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na daga cikin manyan kalubale da yankin ke fuskanta a yakinsa da coronavirus.
Kungiyar Refugees International ta kuma yi nuni ga Syria inda ta ce abin dubawa ce, kuma sama da mutum miliyan 5.6 ne suka tsere daga kasar inda wasu miliyan 6.5 suka kasance cikin kasar amma sun rabu da muhallansu.
Har wa yau, abu ne mai wuya 'yan gudun hijira su iya bin dokokin samar da tazara da kula da lafiya, musamman tunda suna rayuwa ne a wurare masu cunkoso da rashin tsafta.
Mawuyacin hali
Ko a wuraren da ba a yaki, akwai inda ake tunanin coronavirus za ta jefa su cikin halin ka-ka-ni-ka-yi.
Yankin yamma da kogin Jordan da zirin gaza da Isra'ila ta mamaye na wasu daga cikin irin wadannan wuraren.
Hukumomin Falasdinu, wanda ke da ikon kusan kasha 40 cikin dari na yankin Yamma da kogi Jordan, na cikin wani hali saboda rashin damar tsayar da annobar, inda suke fargabar cewa- matafiya masu tafiya tsakanin Isra'ila da yankin- su ne suka taimaka wajen yada cutar.
Amma al'amarin zirin Gaza, mai dumbin mutane, ya fi muni. Al'umar zirina kebe suke, Isra'ila da masar, sun dates zirin daga samun abubuwan more rayuwa, inda suke cewa hakan wani mataki ne na tsaro a kan 'yan bindiga.
An dade ana sa-in-sa tsakanin Isra'ila da kasashen duniya kan mamaye yankin da ta yi. Dakarun Isra'ila sun dade da barin Zirin Gaza kuma Isra'ilar ta dage kan cewa ba ta da hannu a duk wani da ke faruwa a can, wanda yanzu ke karkashin ikon shugabannin Hamas.
Shi ya sa kwararru a Falasdinu da kungiyoyin agaji ke ta kira Isar'ila ta cire datsewar da ta yi wa Gaza, kuma a hada kai tsakanin Falasdinawa da ke Gaza da yamma da kogin Jordan da Isra'ila su yaki annobar.
An ja daga
Lamarin zai yi kyau idan za a ajiye rashin jituwa a gefe a yanzu. Daga bayan fage, Isra'ila na tura wa Falasdinawa a yankin yamma da Kogin Jordan kayan aiki, kuma an ta horar da wasu likitocinta.
Amma yiwuwar ajiye rashin jituwa daga gefe ba shi da yawa. Bangarorin da ke da hannu a rikicin Yemen sun rungumi tsagaita wuta wadda kawo yanzu ba ta fara aiki ba, inda aka kai harin makami mai linzami 'yan kwanaki da suka wuce.
Kuma matsin lambar da Amurka ke yi wa Iran ta hanyar kakaba mata takunkumai ya nuna har yanzu an ja daga. Lallai ne, kwararru a Amurka na ganin cewa takunkumin, na kara dagulawa Iran lamurra musamman wajen sayen kayan asibiti da magunguna daga kasashen waje.
Karin labarai masu alaka
Idan aka saurari masana harkokin siyasa a Amurka, nan da nan za a fahimci cewa ana ganin annobar coronavirus za ta kara lalata martabar gwamnatin Iran.
Akwai annoba a gaba
Ana yi iya tambayar cewa, shin wane tasiri wannan annoba za ta yi idan ta samu wurin zama a yankin?
Gwamnatoci kalilan ne a Gabas ta Tsakiya suke da gaskiya. An lalata duk wani buri na matasa masu tasowa.
Juyin-juya halin da aka yi a yankin bai haifar da wani abin a zo a gani ba.
Ko a Isra'ila da ke da demokuradiyya, annobar ta jefa kasar cikin rikicin siyasa. Bukatar a yaki cutar ya zama kamar tursasa wa jagoran hamayya Benny Gantz shiga cikin gwamnatin Benjamin Netanyahu (abin da ya ce ba zai taba yi ba, kuma matakin da yai daidaita sabuwar jam'iyyarsa).
Kuma rufe kotuna ya janyo tsaiko a sauraren karar Firai Minista Netanyahu kan cin hanci da rashawa, kuma yan ci gaba da jagorantar kasar.
Yaki da cuta sun yi kane-kane a tarihi. Muna bakin ciki cewa, wannan ya faru ne a farkon wannan annoba. Gabas ta Tsakiya na iya fadawa cikin hali mai muni fiye da na yanzu kuma abin da za a gani bayan haka, ba lallai ne ya fi abin da muke gani ba a yanzu.