Coronavirus: Rufe Lagos da Abuja ya sa masu karamin karfi a halin ni 'yasu

Street scene in Lagos

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lagos ne birni mafi girma a yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka
An wallafa

Sama da mutum miliyan 25 ne za su killace kansu a gida tsawon mako biyu a wasu sassan Najeriya don takaita yaduwar coronavirus, masu karamin karfi a unguwannin da ke da cikowa na fargabar yadda za su rayu, kamar yadda wakilin BBC Nduka Orjinmo ya rubuta daga cibiyar kasuwanci, Legas.

"A ina za mu samu isasshen ruwan da za mu wanke hannuwan namu da ake ta magana?" Debby Ogunsola mai shekara 36 ta tambaya, yayin da muke tafe a wani kwararo da zai kai mu dakinta da ke unguwar Alapere a jihar Legas.

Dokar hana zirga-zirga da aiki a Legas- cibiyar kasuwancin Najeriya, da makwabciyarta jihar Ogun da birnin tarayya Abuja- ta fara aiki ne da daren Litinin, bayan sanarwar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi don yaki da cutar, wadda ya ce 'lamari ne na ko a mutu ko a yi rai".

Ga Misis Ogunsola, zai yi wuya ta iya zama a gida ba tare da ta fita ba. Ita da yaranta na rayuwa ne a daki guda cikin wani gida mai dakuna 20, wanda ake kira a kasar 'kalle ni, in kalle ka' saboda kusancin dakunan ga juna.

Babu wutar lantarki, kuma lokacin da na kai mata ziyara, haske na shigowa ta kafar kofa. A waje, akwai ban-daki biyu da wurin wanka da duka iyalan gida ke amfani da su.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

A Abuja ma, akwai mutane da dama masu karamin karfi wadanda ke zaune a irin unguwarsu Misis Ogunsola.

Daya daga cikin irin wadannan mutanen ta shaida wa wakilin BBC cewa ta dogara ne da kasuwancinta na sayar da abinci a bakin titi shi ya sa ta fita wajen sana'arta duk da dokar.

"Ko na zauna a gida, ni da yarana ba mu da abin da za mu ci ko mu sha, shi ya sa na fito wajen sana'ata."

Matar ta bayyana cewa saboda dokar hana zirga-zirgar, ba ta yi ciniki yadda ta saba ba.

Ana gobe dokar za ta fara aiki, kasuwannin Abuja sun cika makil da mutane masu sayen kaya su jibge, sannan kudin kaya, musamman kayan miya, ya yi tashin gwauron zabi.

Masu karamin karfi, wadanda ba su da halin sayen kayan su ajiye sun shiga wani irin yanayi, kamar yadda wata ta shaida wa wakiliyar BBC da suka hadu a kasuwar Utako.

"Na saba sayen attarugu na nair 200 da yawa, kuma yana isata in yi girki mu ci ni da yara mu koshi, amma yanzu na zo an ce ba za a iya ba ni na 200 ba. To ya zan yi kenan?"

Matar ta dade a tsaye tana rokon mai kayan miyar ya rage mata farashin attarugu amma ya yi watsi da ita.

Daga karshe ta mika masa kudin ya zuba mata attarugun da bai taka kara ya karya ba a 'yar karamar leda.

A girl washes her hands in Abuja on 20 March

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wanke hannaye na taimakawa wajen hana kamuwa da cutar

'Tsoron yunwa, ba cuta ba'

Babu ruwan famfo a unguwar Alapere, kuma sai Misis Ogunsola ta yi tafiyar mita 50, ta debo ruwa.

"Yarana nake ji," ta ce.

Dukansu hudu na kwance a kasa yayin da ruwan sama ke ta zuba. Taga daya ce a dakin, kuma da dare a kan yi zafi sosai.

"Idan ban fita na yi kasuwancina ba, ya za su rayu?" in ji Ms Ogunsola, wadda ke sayar da kayan marmari da kayan lambu a bakin titi.

Mijinta na aiki a wurin hakar mai a garin Warri da ke kudancin kasar kuma sai wata-wata yake zuwa gida.

Amma jihohi da yawa- ciki har da Ribas da Delta da Kano da Bayelsa- sun rufe iyakokinsu.

Don haka idan aka ci gaba da dokar zirga-zirgar, za ta dade ba ta ga mijinta ba.

"Na fi damuwa da yunwa kan cutar. Na ma ji an ce ba ta kashe matasa da yara," Ms Ogunsola ta shaida wa BBC.

Duk da cewa tsofaffi da masu wata cuta ta daban ne suka fi mutuwa, kananan yara ma na mutuwa sanadiyyar cutar- kuma suna iya yada ta idan basu bi dokokin ba.

Babu kudin sayen abinci a ajiye

A can tsallaken kwata daga gidan Ms Ogunsola, akwai wasu gidajen irin nata. Daya daga cikinsu na da baranda mai fadi inda wasu maza tsofaffi ke zaune suna magana.

A biranen Najeriya, sau da yawa dangi da suka manyanta kan zo su zauna da 'yanuwansu na birni.

Kuma fargabar ita ce wadannan tsoffin na cikin hadarin kamuwa da cutar.

"Suna gida kuma har yanzu suna taruwa a wuri guda. Da za a samu wani mai dauke da cutar a nan, akwai yiwuwar za ta yadu sosai," in ji Dakta Oyewale Odubanjo, wani kwararre a harkar lafiya.

A Italiya, iyali masu bambancin shekaru da dama na zaune ne a gida daya kuma wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa aka samu yawan mace-macen coronavirus fiye da kowace kasa.

An haramta duk wata tafiya da ba ta zama tilas ba a mafi yawan jihohi kuma ma'aikata da dama, har da ma'aikatan gwamnati, na aikinsu ne daga gida.

Amma da rashin tsayayyiyar wutar lantarki da layukan intanet marasa tabbas, zai yi wuya mutane su yi aikinsu yadda ya kamata.

A manyan kantuna, mutane sun yi jerin gwano bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da dokar hana zirga-zirgar da dakatar da ayyuka, inda suke ta sayen kayan masarufi don ajiyewa.

Amma 'yan Najeriya da yawa na rayuwa ne hannu-baka hannu-kwarya, sau da yawa suna rayuwa a kasa da dala 1 kuma ba za su iya sayen kayan abinci ko kayan masarufi da yawa ba.

Bayanan bidiyo, Fauziyya Kabir Tukur ta yi dubakan yadda Coronavirus ta yi illa ga tattalin arzikin Afirka

Akwai ma'aikata da yawa da har yanzu ba a biya su albashinsu na watan Maris ba, don haka akwai fargaba sosai kan yadda dokar za ta shafi mutane ta fuskar kudin kashewa.

Buhari ya zayyano wasu matakai da za su rage wa mutane radadin yanayin da aka shiga, ciki har da biyan kudin watan gobe na kudin wata-wata da gwamnati ke bai wa marasa galihu, amma mafi yawan mutane na ganin miliyoyin 'yan Najeriya da ke dogara da kansu za su shiga mawuyacin hali.

"Mutanen da ke kudi ne kawai za su iya sayayya. Idan ba ka da shi, ya z aka yi?" in ji wani direban tasi da ya ajiye motarsa a wajen wani babban kanti.

Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

Akwai ma'aikata da yawa da har yanzu ba a biya su albashinsu na watan Maris ba, don haka akwai fargaba sosai kan yadda dokar za ta shafi mutane ta fuskar kudin kashewa.

Deserted road in Lagos on 26 March

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An hana tafiye-tafiye a a Legas
People on motorcycles temperature are measured at a border between Abuja and the Nasarawa State on March 30, 2020,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ana gwada yanayin zafin jikin 'yan acaba a yayin da suke barin birnin Abuja
Wannan layi ne

Karin labarai masu alaka