Coronavirus: Yadda attajiran Nigeria suke bayar da tallafi kan yaki da cutar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Tun da annobar coronavirus ta bulla kasar China, inda ta kashe dubban mutane kafin ta yadu zuwa sauran sassan duniya, mutane daban-daban ke yin kira ga attajirai da 'yan kasuwa masu zaman kansu da ma manyan kamfanoni, su bayar da gudunmawa domin yaki da cutar.

Ya zuwa ranar Juma'a 27 ga watan Maris na 2020, alkaluma daga Jami'ar Johns Hpkins da ke Amurka, sun nuna cewa fiye da mutum 558,00 suka kamu da cutar yayin da sama da mutum 25,251 suka mutu.

A Najeriya, ya zuwa ranar Juma'a, cibiyar yaki da cutuka ta kasar ta tabbatar cewa mutum 81 ne suka kamu da koronabairus, uku sun warke, yayin da daya ya mutu a kasar.

Hakan ne ya sa hukumomin lafiya da gwamnatoci da ma daidaikun mutane ke yin kira a fitar da kudi da kayan aiki domin dakile koronabairus.

A wani bangaren kuma, ana yin kira ga attajiran da sauran masu wadata su tallafa wa marasa karfi da kayan abinci da abubuwan more rayuwa da ma kudade a yayin da gwamnatoci suke umartar 'yan kasar su zauna a gidajensu don hana baza cutar.

Attajirai irin su Bill Gates, mai kamfanin Microsoft; da Jack Ma, mai kamfanin Ali Baba; da Elon Musk, mamallakin kamfanin motocin Tesla na cikin mutanen da suka bayar da tallafin biliyoyin dalar Amurka da kuma kayan aiki domin yaki da annobar.

Hakan lamarin yake a Najeriya inda attajirai da bankuna da manyan kamfanoni suka bayar da gudunmawar biliyoyin naira domin yaki da cutar.

Attajirai irin su Aliko Dangote, Femi Otedola, Abdulsamad Rabiu, Herbert Wigwe da kuma, Segun Agbaje ko wannensu ya ba da gudunmawar naira biliyan daya don a dakile koronabairus

Alal misali, mai kamfanin BUA Group, Abdul Samad Rabiu, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya kara da cewa baya ga kudin, kamfaninsa ya bayar da kayan aiki da suka hada da injina da na'urorin gwaji da sauransu ga jihohi 9 na kasar.

Shi ma bankin United Bank for Africa (UBA) ya bayar da gudunmawar naira biliyan biyar domin sayen gadaje da kayan aiki da za a sanya a cibiyoyin killace wadanda suka kamu da cutar.

"Dole ne mutane da gwamnati da 'yan kasuwa su hada hannu domin yakar wannan annoba da ta addabi duniya -- cikin gaggawa.

A yayin da ake samun karin mutanen da suka kamu da coronavirus a Najeriya da Afirka, 'yan kasuwa za su yi aiki kafada da kafada da gwamnatoci wajen dakile yaduwar cutar," in ji shugaban bankin Tony Elumelu, a wata sanarwa da ya fitar.

Ya kamata gwamnati ta bai wa kowanne magidanci N10,000

A nasa bangaren, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayar da tallafin naira miliyan 50 domin yaki da annobar ta koronabairus.

Kazalika ya yi kira ga gwamnatin Shugaba Buhari ta bai wa duk wani magidanci a kasar tallafin N10,000 domin rage radadin da mutane ke fuskanta yayin da suke bin umarnin gwamnati na zama a gidajensu don hana yaduwar cutar.

"Yayin da muke da magidanta kusan miliyan 30 a Najeriya, ya kamata gwamnati ta samar da hanyoyin da za ta bai wa kowane magidanci naira 10,000 a matsayin tallafi na kayan abinci," Atiku ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa da kansa a shafinsa na intanet.

Da alama wannan gudunmawa da attajiran Najeriyar suka bayar domin yaki da annobar Covid-19 ta faranta ran shugaban kasar Muhammadu Buhari.

A sanarwar da ya fitar ranar Juma'a wacce kuma aka wallafa a shafukan sada zumunta, Shugaban Buhari ya jinjina musu bisa dattakun da suka nuna wajen bayar da tallafin.

"Shugaban kasa yana jinjina ga sauran mutane da kungiyoyi wadanda suka bayar da tasu gudunmawar, wasu ma ba tare da sun bayyana a fili ba, yana mai cewa Allah zai saka musu da alheri," in ji sanarwar.