Duniya ta kyamaci juyin mulkin Thailand

Juyin mulkin Thailand bai sami karbuwa ba

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Juyin mulkin Thailand bai sami karbuwa ba
An wallafa

Kasashen duniya sun yi Allah-wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Thailand.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce babu dalilin yin juyin mulki.

Shi ma sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-Moon ya yi kiran da a gaggauta dawo da Dimokradiyya kasar; kamar yadda mai magana da yawunsa Stephane Dujarric ya shaidawa BBC.

A bangare guda kuma gwamnatin Sojin kasar ta bukaci tsohuwar Firai-Minista Yingluck Shinawatra da masu fada a ji a harkokin siyasar kasar da su bayyana a gabanta.