Maciji ya hadiye kada a Australia

Asalin hoton, AFP
An wallafa
Wata mesa ta haɗiye wani kada, bayan shafe sa'oi da dama suna gumurzu, a gefen wani tafki a Queensland a Australia.
Mutane sun yi dandazo a lokacin da macijin mai tsawon mita uku, ke kokawar haɗiye kadan.
An ɗauki hoton al'amarin a wayar komai da ruwanka, inda macijin ya kanannaɗe kadan.
Daga bisani dai gamshekar ta samu nasarar hadiye kadan, inda ake ganin alamunsa a cikinta.








