Daga Bakin Mai Ita tare da Maryam Bakasee
An wallafa
Daga Bakin Mai Ita shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsu zalla.
A wannan kashi na 105, BBC ta tattauna da wata mawakiya a masana'antar Kannywood Maryam Bakasee kuma ta amsa tambayoyi da suka shafi rayuwarta.
Daga cikin tambayoyin akwai tarihin mawakiyar da fitattun wakokinta da kuma yadda ta samo sunanta na Bakasee.