Daliban Indiya da suka makale a dakin karkashin kasa a Ukraine na neman a cece su
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ɗaliban Indiya suna neman mafaka a wani ɗaki na ƙarƙashin ƙasa a Kharkiv, birni na biyu mafi girma da ke kusa da kan iyakar Rasha, a yayin da ake ci gaba da jefa bama-bamai.
Suna neman gwamnatin ƙasarsu ta Indiya ta kai musu agaji saboda yanayin da suke ciki na rashin abinci da ruwa.