Bidiyo: Bukukuwan da mutane suke yi kan harin da Rasha ta kai wa Ukraine
An wallafa
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Dakarun Rasha sun kwashe dare suna kai hare-hare a Ukraine kwanaki kadan bayan Shugaba Rasha Vladimir Putin ya amince da yankuna biyu da ke gabashin Ukraine a matsayin masu 'yancin kansu.
Kungiyar tsaro ta Nato da kawayenta sun bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na mamayar Ukraine.
Wasu 'yan kasar ta Rasha sun yi matukar murna kan matakin shugaban kasar, yayin da wasu suke sukarsa.