Bidiyon Ku San Malamanku tare da Dokta Zakariyya Sa'id Zakariyya

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Dokta Zakariyya Sa'id Zakariyya
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An haifi Dokta Zakariyya a shekarar 1960, a wata tsangaya dake Kandi a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa.

Mahaifinsa Malami ne na Alkur’ani wanda yake da almajirai da dama.

Dokta Sa’idu ya shafe shekaru yana karatun Alkur’ani a gidansu, kafin daga baya ya tafi garuruwa da dama da suka hada da Takai a jihar Kano da garin Bauchi da birnin Kano da biranen Zariya da Kaduna a jihar Kaduna.