Bidiyon Ku San Malamanku tare da Ustaz Husaini Zakariyya

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Ustaz Husaini Zakariyya
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A wannan makon mun kawo muku tattaunawar da muka yi da Ustaz Husaini Zakariyya, wani malamin addinin Musulunci a Abuja, babban birnin Najeriya.

An haifi Ustaz Hussaini Zakariyya Yawale a garin Kaduna ranar 1 ga watan Oktoban 1960 a unguwar Abakwa, wanda ya yi daidai da 10 ga Rabi'u Thani shekara ta 1380 bayan Hijira.

Mahaifinsa malamin addinin Musulunci ne na Mazhabar Malikiyya kuma a hannunsa ya fara karatu.