Sifaniya ta bayyana ƴan wasan ƙwarya-ƙwarya 29 don Euro 2024
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a fagen wasanni a fadin duniya a wannan lokacin.
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
Sifaniya ta bayyana ƴan wasan da za ta je da su Euro 2024
Tawagar Sifaniya ta bayyana wadanda za su buga mata gasar Euro 2024 da za a yi a Jamus daga watan gobe.
Cikin ƴan wasan na ƙwarya-ƙwarya 29 har da na Chelsea, Marc Cucurella da na Manchester City, Rodri da na Brentford, David Raya, wanda ya buga wasannin aro a Arsenal.
Cikinsu har da mai taka leda a Real Madrid, Joselu
Sifaniya za ta bayyana ƴan wasa 26 daga 29 da ta bayyana kafin 7 ga wwatan Yuni.
Asalin hoton, Spanish Football
Ba a fayyace makomar Casemiro a Man United a badi ba
Ana tantama kan makomar Casemiro a Manchester United a badi, wanda bai buga wasan da ƙungiyar ta lashe FA Cup ba ranar Asabar.
Tun kan wasan da United ta doke Manchester City 2-1, Erik ten Hag ya sanar cewar ɗan wasan tawagar Brazil bai da lafiya, ba zai iya buga karawar ba.
Sai dai kociyan ya saka sunan ɗan kwallon cikin masu zaman benci daga baya Casemiro ya ce ba zai yi wasan ba a cire shi daga wadanda aka bayyana a wasan na karshe.
Tuni dai tawagar Brazil ba ta gayyaci Casemiro gasar Copa America ba da zaa fara a watan gobe a Amurka, saboda baya kan ganiya a bana.
Tuni ake ta alakanta tsohon wanda ya taka leda a Real Madrid da cewar zai koma Saudi Arabia kan fara kakar badi.
Asalin hoton, Getty Images
Duk wanda ya karbi aikin kociyan Barcelona zai sha wahala
Tsohon kociyan Barcelona, Xavi ya ce duk wanda ya karbi aikin horar da ƙungiyar zai sha wahala.
An sallami kociyan mai shekara 44 tun kan ya ja ragamar wasan karshe a La Liga da Barcelona ta yi nasara 2-1.
Ana sa ran tsohon kociyan tawagar Jamus da Bayern Munich, Hansi Flick ne zai maye gurbinsa a ƙungiyar Camp Nou.
Wasu ƴan wasan Ipswich za su haska a Premier League a badi
Mai tsaron bayan Southampton, Taylor Harwood-Bellis yana cikin wadanda ake sa ran zai taka rawar gani daga Southampton a Premier League a badi.
Ɗan ƙwallon dake taka leda aro daga Manchester City ya buga wasan karshe da suka doke Leeds United 2-1 ranar Lahadi.
Asalin hoton, Getty Images
Kociyan Ipswich baya cikin masu neman aiki horar da Chelsea
Kociyan Ipswich Town, Kieran McKenna baya cikin masu takarar karbar aikin horar da Chelsea, bayan da Manchester United da Brighton ke fatan yin zawarcinsa.
Chelsea na tattaunawa da koci da yawa don maye gurbin Mauricio Pochettino da ta kora, cikin wadanda take son dauka har da na Brighton, Roberto De Zerbi da na Leicester, Enzo Maresca da kuma na Brentford, Thomas Frank.
Shin ya kamata Man United ta ci gaba da aiki da Ten Hag?
Ranar Asabar Manchester United ta lashe FA Cup, bayan da ta doke Manchester City 2-1 a Wembley ranar Lahadi.
Hakan ya sa United za ta buga Europa League a badi, duk da karewa a mataki na takwas din teburin Premier League.
A bara United ta kare a mataki na uku a teburin Premier League da ta samu buga Champions League da daukar League Cup.
Asalin hoton, Getty Images
Wasu batuwan da Man City za ta magance kafin badi
Bayan da kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya yi murnar lashe kofin Premier League ranar Lahadi, akwai wasu batutuwan da ƙungiyar ya kamata ta fuskanta kafin fara kakar badi.
Cikin batutuwan sun hada da
Kevin de Bruyne yana da shekara 32, duk da saura kwantiragin kaka daya ya rage masa a Etiihad, sai dai yadda ya kasa taka rawar gani a wasan karshe a FA Cup da Manchester United ta lashe alama ce ta fara gajiya.
Watakila Kevin Philips ya bar ƙungiyar kafin fara kakar nan, bayan da ta kai an bayar da aronsa ga West Ham United.
Ana kuma tantama kan mai tsaron raga, Ederson, wanda ake alakanta shi da zai koma Saudi Arabia da taka leda kan fara kakar badi.
City ta biya Wolverhampton £53m wajen daukar Matheus Nunes cikin Satumba, sai dai wasa bakwai kadai ya buga a Premier League daga nan ya koma zaman benci.
Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta yi bikin lashe Premier League ranar Lahadi
Yayin da Southampton ke murnar lashe kofin cike gurbin shiga Premier League ranar Lahadi a ranar Manchester City ta yi shagalin lashe babbana kofi na bana na hudu a tarihi.
Sai dai ƙungiyar ta Etihad ta yi rrashin nasarar FA Cup, bayan da Manchester United ta doke ta 2-1 ranar Asabar ta lashe na 13 jimilla.
Pep Guardiola da jami'ai da ƴan wasa sun shiga budaddiyar bas, suka ratsa birnin, inda magoya baya suka ta yi musu tafi kan rawar da suka taka a kakar nan da ta hada da lashe Premier League da Club World Cup da kuma Uefa Super Cup..
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Man City
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Martin zai shiga cikin manyan masu horar da tamaula a Premier
Russell Martin ya taka rawar gani da ya kai Southampton gurbin shiga Premier League ta badi, bayan da ya doke Leeds United1-0 a wasan cike gurbi a Championship ranar Lahadi a Wembley.
Mai shekara 38 ɗan kasar Scotland zai zama mai horar da tamaula a Premier League, wanda ya fara daga MK Dons mai buga League One.
Ya ja ragamar Southampton ta kare a mataki na hudun teburin Championship, bayan da ya koma ƙungiyar daga Swansea City.
Asalin hoton, Getty Images
Beatrice Chebet ta kafa tarihin lashe gudun fanfalaki
Ƴar kasar Kenya, Beatrice Chebet ta kafa tarihin lashe gudun fanfalaki na mita 10,000 cikin sama da minti 28 a Prefontaine Classic Diamond League a Eugene, Oregon.
Mai shekara 24, mai lambar yabo biyu ta zinare a mita 5,000 ta doke tarihin da yar Habasha, Letesenbet Gidey ta kafa a Hengelo ranar 8 ga watan Yunin 2021, cikin sama da dakika 29.
Wannan nasarar da Chebet ta samu ya sa an fara dora ta cikin wadanda ake hasashen za ta taka rawar gani a gasar Olympic a birnin Pari cikin watan Agusta.
Rafli Mata za su yi alkalanci a Copa America a karon farko
A karon farko a gasar Copa America da za a fara a watan gobe a Amurka za ta kunshi alkalai mata da za su ja ragamar wasu daga fafatawar, in ji hukumar kwallon kafar Kudancin Amurka CONMEBOL.
Za a fara gumurzun daga 20 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yuli a Amurka da alkalai 101 da mata takwas daga ciki.
Wannan ce gasa ta 48 karo na biyu da za a yi a Amurka da tawagogi 16 za suyi tata burza a tsakaninsu, inda Argentina ce mai rike da kofin.
Duk wadda ta zama zakara za ta raba raini a 2025 da wadda za ta lashe Champions League na Turai a bana.
Ranar 1 ga wayan Yuni za a buga wasan karshe tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund a Wembley.
Asalin hoton, Getty Images
A bara Southampton ta fadi daga Premier
Southampton ta doke Leeds United 1-0 ranar Lahadi a Wembley a wasan cike gurbi a Championship ta samu gurbin shiga Premier League a badi da ladan £140m.
A bara ne Southampton ta fadi daga babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan kaka 11 da ta yi a gasar, amma za ta koma taka leda daga badi tare da Leicester City, wadda ta lashe kofin Championship da kuma Ipswich wadda ta yi ta biyun teburi.
Adam Armstrong ne ya ci wa Southampton ƙwallon kuma na 22 jimilla a bana, shi ne kan gaba a yawan ci wa ƙungiyar ƙwallaye.
Asalin hoton, Getty Images
Southampton za ta koma buga Premier a 2024/25
Southampton ta samu gurbi na uku na shiga Premier League a badi, bayan da ta ci Leeds United 1-0 a wasan cike gurbi ranar Lahadi a Wembley.
An buga karawar cike gurbi tsakanin wadda ta yi ta uku a kakar wato Leeds United mai maki 90 da wadda ta yi ta hudun teburi Southampton mai maki 87.
Da wannan sakamakon Southampton ta samu gurbi na uku, bayan da Leicester City ta lashe kofin Championship na bana da maki 97, sai Ipswich Town ta biyu da tazarar maki ɗaya tsakani da ƙungiyar King Power.
Tun farko ƙungiyoyi uku ne daga Premier League a bana suka bar gasar da suka hada da Luton Town da Burnley da kuma Sheffield United - a kakar bara Leicester City da Southampton da Leeds United suka bar babbar gasar tamaula ta Ingila
Adam Armstrong ne ya ci kwallo na 22 a bana, shi ne kan gaba a yawan ci wa kungiyar kwallaye a bana ya tofa albarkacin bakinsa tun kan karawar.
Asalin hoton, Getty Images
Yadda ta kaya a wasan cike gurbin shiga Premier, Southampton 1-0 Leeds United
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Ko Kompany zai taka rawar gani a Bayern Munich kuwa?
Kociyan Burnley, Vincent Kompany ya zama wanda zai ja ragamar Bayern Munich, wadda ta yi fama da kalubale a kakar bana.
Tuni kuma ya amince da ƙunshin ƙwantiragin da zai kare a karshen kakar 2027, ya maye gurbin Thomas Tuchel.
Ƙungiyar dake buga Bundesliga ta nemi wanda zai maye gurbin Tuchel, wanda cikin Fabrairu ya sanar da zai ajiye aikin da zarar an kammala kakar nan.
Kociyan Bayer Leverkusen, Xabi Alonso da na tawagar Jamus, Julian Nagelsmann da na Austria, Ralf Rangnick duk sun ki amincewa da tayin da aka yi musu.
Haka kuma an kasa rarrashin Tuchel ya sauya shawara, amma hakan bai yiwuba, hakan ya sa ƙungiyar take ta neman kociyan da ya kamata ta dauka.
Kompany ya taka rawar gani a lokacin da ya horar a Anderlecht da kuma Burnley, wadda ya kai gasar Premier League a bara daga Championship a kakar farko.
Ko da yake ta kasa taka rawar gani a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana, wadda ta kare a mataki na biyun karshe, ke nan za ta koma buga Championship a badi.
Haka kuma ƙungiyar dake buga Bundesliga na tuna rawar da ɗan kwallon ya taka a Hamburg lokacin da yake taka leda, sannan yana jin harshen Jamus.
Bayern Munich ta karkare kakar bana ba tare da lashe kofi ba karkashin Tuchel da yin ta uku a teburin Bundesliga da Leverkusen ta lashe, Stuttgard ta yi ta biyu.
Asalin hoton, Getty Images
Barkanmu da kasancewa cikin shirin
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan kasance da ku wajen kawo muku labarin wasanni kai tsaye.
Da fatan za ku kasance da ni har zuwa yammacin nan, za ku iya bayar da gudunmuwa a BBC Hausa Facebook da Twitter kai tsaye.