Duk wanda ya karɓi aikin horar da Barcelona zai sha wuya - Xavi

Xavi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Tsohon kociyan Barcelona, Xavi ya ce duk wanda ya karbi aikin horar da ƙungiyar zai sha wahala.

An sallami kociyan mai shekara 44 tun kan ya ja ragamar wasan karshe a La Liga da Barcelona ta yi nasara 2-1.

Ana sa ran tsohon kociyan tawagar Jamus da Bayern Munich, Hansi Flick ne zai maye gurbinsa a ƙungiyar Camp Nou.

Xavi, wanda yake da ƙunshin yarjejeniyar da ya kamata ta kare a 2025 ya sanar cikin Janairu cewar zai bar Barcelona da zarar an kammala kakar nan.

Daga baya aka rarrashe shi, wanda cikin watan Afirilu ya amince zai ci gaba da aikin horar da ƙungiyar

Ya ce: ''Zan gaya maka sabon kociyan Barcelona: Za ka sha wuya', wannan wata ƙungiya ce mai ɗan karen wahalar aiki. Sai dai ka hada da hakuri.''

Tsohon dan wasan tawagar Sifaniya ya karbi aikin kociyan ƙungiyar a cikin Nuwambar 2021 da lashe La Liga da Spanish Super Cup a kakar farko.

Sai dai a bana, Barcelona ta kare a mataki na biyu a teburin La Liga, bayan da Real Madrid abokiyar hamayya ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Haka kuma Real Madrid, wadda za ta buga wasan karshe a Champions League da Borussia Dortmund ta bai wa Barcelona tazarar maki 10 a La Liga.

Barcelona ta kori Xavi tsohon ɗan wasan ƙungiyar wata ɗaya tsakani da ya amince zai ci gaba da jan ragamarta.

An kuma sallami Xabi sakamakon kalamai da ya yi kan matsin tattalin arziki da ƙungiyar ke fuskanta, hakan ya sa mahukuntanta suka harzuka suka raba gari.

''Na fahimci dukkan abinda na gudanar da nasarar da na samu a shekara biyu da rabi ba ta yiwa ƙungiyar dadi ba, ''An yi ta harin bakanta min a lokaci da yawa.''

Xavi ya kara da cewar ''Ba a yaba aikin da na gudanr a ƙungiyar ba, kan batun sallamarsa kuwa ya kara da cewar ''Na amince da hukuncin, ba abinda zai sauya kan batun da na yi ko na amince da abinda ƙungiya ke bukata.''

Xavi ya ce a shirye yake ya ci gaba da horar da tamaula duk lokacin da aka tuntube shi, amma yanzu zai dan huta daga baya ya koma harkar.

''Zai yi wahala ka gudanar da aiki a Barcelona,'' in ji Xavi ''Na fuskanci ƙalubale a makon da ya wuce, amma na fayyace matsayi na, sannan ina cike da farinciki.''