Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda Man United ta dauki FA Cup na 13 jimilla

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a fagen wasanni a fadin duniya a wannan lokacin.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Da fatan kun ji dadin shirin da muka gabatar ranar Asabar.

    Za mu ci gaba da kawo muku sharhi da bayanan wasanni daga ranar Litinin da fatan za ku tara a lokacin.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper ke yi muku fatan alheri.

  2. Muhawarar da aka tattauna a BBC Hausa Facebook

  3. Ƙyaftin Fernandes ya daga FA Cup, Man City 1-2 Man Utd

    Ƙyaftin din Man United, Bruno Fernandes ya daga FA Cup, inda magoya baya suka yi kuwa da murnan daukar kofin na bana.

  4. Minti 20 da tashi daga wasa magayo bayan United na cikin fili

  5. Man United za ta buga Europa League a badi, Man City 1-2 Man Utd

    Ba wwai kawai FA Cup da Manchester United ta dauka ba, ya kuma ba ta damar shiga gasar Europa League a badi, kuma hakan gagarumar ci gaba aka samu a ƙungiyar Old Trafford.

    Kenan kakar bana ta yi wa Manchester United kyau.

  6. Man City za ta yi bikin lashe Premier ranar Lahadi a birnin Manchester

  7. Man United ta fara murnar daukar FA Cup

  8. Ko wannan ne wasan karshe da Erik ten Hag ya ja ragamar United, duk da haka ya yi kokarin ganin ƙungiyar za ta buga Europa League a badi, bayan da ta kare a mataki na takwas a Premier Pleague.

    Sai ɗaga jajayen tutoci ake yi a filin Wembley.

  9. Manchester United ta lashe FA Cup na bana na 13 jimilla

    United ta dauki fansa kan abokiyar hamayya Manchester City, wadda a bara a wasan karshe ta ci 2-1 ta lashe kofin na bakwai jimilla, wadda ta hada da na Premier League da kuma Champions League.

    Wannan shi ne daya daga cikin wasa mafi kayatarwa da United ta buga, yayin da daya daga mafi muni da City ta yi.

    United ta lashe FA Cup na 13 jimilla, kuma hakan ya sa za ta buga Europa League kai tsaye a badi

  10. Doku ya sa matsi tun bayan da ya shiga karawar

  11. Man United ta bari an farke kwallaye a kakar nan

    Manchester United ta barar da damar cin wasa, wadda take fara cin kwallo daga baya a farke, wadda ta yi haka a wasa da Chelsea, haka kuma a FA Cup daf da karshe ta ci Coventry uku daga baya aka farke ta kai ga bugun fenariti.

  12. Ya kamata ace Onana ya tare ƙwwallon

    Ya kamata ace Onana ya tare ƙwallon. Yanzu matsi zai hau kan United, inda City za ta matsa kaimi ko za za zare dayar.

    Sai dai lokaci ya kusan karewa, ba a kai ga karin lokaci ba.

  13. GOAL, Man City 1-2 Man

    Jeremy Doku ya zare daya.

  14. Man United tana nuna ta gaji, Man City 0-0 Man United

    Ba za a yi mamaki da an wasan Manchester United ke nuna gajiya, bayan da ta yi fama da masu rauni.

    An canja Marcus Rashford da Lisandro Martinez.

    Martinez ya harzuka Kyle Walker bayan da yake tafiyar kasaita da zai fita daga fili.

  15. Alejandro Garnacho shi ne na uku matashi da ya ci kwallo a wasan karshe a FA Cup, bayan Norman Whiteside (1983 da Brighton) da Cristiano Ronaldo (2004 da Millwall).

  16. , Man City 0-2 Man Utd

    Alejandro Garnacho ya samu ƙwallo a cikin da'ira a ɓangaren hagu ya kuma buga zuwa raga, amma mai tsaron bayan Manchester City, Stefan Ortega ya ture zuwa kwana ta farko da United ta samu bayan da aka koma zagaye na biyu.

    Ai kuwa nan da nan Guardiola ya dafa kai ya ɗauka an kara musu na uku.

  17. , Man City 0-2 Man Utd

    Dama mai kyau daga Manchester City!

    Julian Alvarez ya buga wata ƙwallo da ya samu mai kyau, amma ta yi fadi ta fita waje.

  18. , Man City 0-2 Man Utd

    Bayan da aka koma zagaye na biyu Manchester United ta koma tsare gida.

  19. GREAT SAVE!, Man City 0-2 Man Utd

    Onana ya hana ƙwallo ya shiga raga

    Kyle Walker ya samu damar cin ƙwallo, amma Onana ya tare.

  20. , Man City 0-2 Man Utd

    Kevin de Bruyne bai taka rawar ba a tsakanin ƴan wasan Manchester City wajen raba ƙwallo a wasan karshen FA Cup.