PSG za ta biya Mbappe Fam miliyan 51
An sami rahotannin cewa PSG za ta biya Kylian Mbappe fam miliyan 51 a matsayin wani kari na musamman idan har ya kasance a kungiyar zuwa ranar 1 ga watan Augusta.
Wannan ya biyo bayan wadansu sharudda ne da aka gindaya a kwantaraginsa.
Hakan ya sa masana harkan wasanni ke tunanin zai bar kungiyar da zarar ya karbi kudin.
Ana sa ran dan wasan na Faransa zai bar kungiyar kafin a fara kakar wasa ta bana bayan ya bayyana cewa ba zai kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar ba.
PSG sun sanya dan wasan a kasuwa domin suna gudun rasa shi a kyauta a shekara mai zuwa inda kwantaraginsa zai kare kuma sun sanar da masu sha'awar dan wasan da su mika tayi.
Kungiyoyi da dama na sha'awar dan wasan wanda suka hada da Real Madrid da Chelsea, da Newcastle da Manchester United da Inter Milan da kuma Tottenham amma babu kungiyar da ta kawo tayi da ya kai na kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya.
Kungiyar kwallon kafa ta Saudi Pro League ta gabatar da wani gagarumin tayi ga Mbappe, wanda ya kai fam miliyan 259.
Amma ana ganin kamar dan wasan ba ya sha'awar komawa Saudiya a halin yanzu.