Balotelli na tsammanin tayi daga saudiya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. PSG za ta biya Mbappe Fam miliyan 51

    Mbappe

    Asalin hoton, EPA

    An sami rahotannin cewa PSG za ta biya Kylian Mbappe fam miliyan 51 a matsayin wani kari na musamman idan har ya kasance a kungiyar zuwa ranar 1 ga watan Augusta.

    Wannan ya biyo bayan wadansu sharudda ne da aka gindaya a kwantaraginsa.

    Hakan ya sa masana harkan wasanni ke tunanin zai bar kungiyar da zarar ya karbi kudin.

    Ana sa ran dan wasan na Faransa zai bar kungiyar kafin a fara kakar wasa ta bana bayan ya bayyana cewa ba zai kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar ba.

    PSG sun sanya dan wasan a kasuwa domin suna gudun rasa shi a kyauta a shekara mai zuwa inda kwantaraginsa zai kare kuma sun sanar da masu sha'awar dan wasan da su mika tayi.

    Kungiyoyi da dama na sha'awar dan wasan wanda suka hada da Real Madrid da Chelsea, da Newcastle da Manchester United da Inter Milan da kuma Tottenham amma babu kungiyar da ta kawo tayi da ya kai na kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya.

    Kungiyar kwallon kafa ta Saudi Pro League ta gabatar da wani gagarumin tayi ga Mbappe, wanda ya kai fam miliyan 259.

    Amma ana ganin kamar dan wasan ba ya sha'awar komawa Saudiya a halin yanzu.

  2. Balotelli na tsammanin tayi daga saudiya

    Balotelli

    Asalin hoton, BBC Sport

    Mario Balotelli a halin yanzu baya cikin tsarin FC Sion amma an samo rade-radin cewa zai iya samun tayi mai tsoka daga Saudi Arabiya nan ba da jimawa ba.

    Balotelli bai sami yadda ya ke so ba sosai bayan tafiyarsa daga Liverpool a 2016, inda ya shafe ɗan lokaci tare da Nice da Marseille da Brescia da Monza, da Adana Demirspor sai kuma yanzu Sion.

    An ruwaito cewa Balotelli yanzu ya fice daga tsarin FC Sion kuma yana atisaye shi kadai inda ya ke jiran kungiyar da za ta taya shi.

    Yana da sauran shekara daya a kwantiraginsa da kungiyar FC Sion.

    An sami rade-radin cewa nan ba da jimawa ba za a aika tayi mai tsoka daga Saudiyya ga dan wasan na Italiya, amma kawo yanzu Sion ba ta ji komai kan wannan batun ba.

    A kakar wasan da ta wuce, Balotelli ya zura kwallaye tara a raga a wasanni 19 da ya buga wa kulob din na Switzerland.

  3. Igor Julio ya koma Brighton daga Fiorentina

    Igor Julio

    Brighton ta sayi dan wasan baya na Brazil Igor Julio daga Fiorentina kan fan miliyan 14.5 .

    Dan wasan mai shekaru 25 ya amince da kwantiragin shekaru hudu da kungiyar ta Seagulls.

    Koci Roberto de Zerbi ya mayar da hankalinsa ga Igor bayan tsada ta hana shi siyan dan wasan Chelsea da Ingila na kasa da shekara 21, Levi Colwill.

    Igor ya isa filin wasa na Amex bayan da chelsea ta yi watsi da tayin fan miliyan 40 da Brighton ta yi kan Colwill mai shekara 20.

    Mai tsaron baya na Chelsea da ya zo a matsayin aro ya taimaka wa Seagulls har suka ka mataki na shida a gasar Premier na bara da kuma samun gurbin shiga gasar cin kofin Europa na bana.

    Dan wasan bayan wanda ya fara taka leda a gasar Bundesliga ta Austria tare da Red Bull Salzburg kafin ya koma Italiya, ya koma Fiorentina daga SPAL a watan Janairun 2020 kuma ya buga wasanni 110 a kungiyar ta Serie A.

  4. Tottenham ta karbi tayin Spartak Moscow kan Davinson Sanchez

    Davinson Sanchez

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham ta amince da tayin fam miliyan 12.9 kan Davinson Sanchez daga Spartak Moscow, amma dan wasan ba ya son komawa kungiyar ta Rasha.

    Dan wasan bayan Colombia ya buga wa Spurs wasanni 205 tun lokacin da ya koma kungiyar a kan fan miliyan 42 daga Ajax a shekarar 2017.

    Dan wasan mai shekaru 27 a halin yanzu yana tare da Tottenham a rangadin da suke yi na shirin tunkarar kakar wasanni mai zuwa.

    An kuma alakanta Sanchez da Galatasaray, wanda aka ruwaito sun nemi shi a watan Yuni.

    Sanchez ya buga wa Tottenham wasanni 18 a gasar firimiya yayin da ta kare a matsayi na takwas a kakar da ta wuce.

    Gasar Firimiya ba za ta iya hana kungiyoyi yin mu'amala da kowane bangare na kasar Rasha ba, amma an fahimci cewa za su yi kakkausar suka ga kungiyoyin da suka kulla yarjejeniya da kungiyoyin kasar a yayin da a ke ci gaba da mamaye kasar Ukraine.

  5. Guardiola ya jinjinawa matasan Man City bayan sun doke Bayern Munich

    Man City

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ce basirar da suke da ita a makarantar horar da 'yan wasan kulob din tana da matukar ban mamaki bayan da kungiyarsa ta doke Bayern Munich da ci 2-1 a wasan sada zumunci da aka buga a Tokyo.

    Dan wasan tsakiya James McAtee, mai shekara 20, ne ya fara zura kwallo a farkon rabin lokaci bayan kyakkyawan aiki daga Rico Lewis mai shekaru 18.

    Mathys Tel ne ya rama wa Bayern a minti na 81 kafin Aymeric Laporte ya sake ci ma City bayan minti biyar.

    City ta samu nasarar lashe wasan sada zumuntar sda suka buga karo na biyu a filin wasa na kasar Japan bayan ta doke Yokohama F Marinos da ci 5-3 a karshen mako.

    Guardiola da tawagarsa za su je birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu domin karawa da Atletico Madrid a ranar Lahadi, kafin su kara da Arsenal a gasar Community Shield ranar 6 ga watan Agusta.

  6. Bayern Munich na zawarcin golan Brentford

    David Raya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayern Munich ne ke neman golan Brentford David Raya, wanda hakan zai bude kofa ga Yann Sommer ya koma Inter Milan.

    A watan Fabrairu Raya ya ce "ya na matukar farin ciki" a Brentford duk da cewa ya ki amincewa da sabon tayin kwantiragi biyu da kungiyar ta yi masa.

    Brentford ta sanya wa Raya farashin Fam Miliyan 40 wanda masan harkan kasuwanci 'yan wasa ke ganin kamar ya yi yawa.

  7. Man City na son rike Silva

    Bernardo Silva

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun bayyana cewa Manchester City ta shaida wa dan wasanta na tsakiya Bernardo Silva cewa ba su da niyyar sayar da shi a bazarar nan, duk da cewa dan wasan mai shekara 28 na neman ya kara gaba.

    Silva ya sanar da City a bazarar da ta gabata cewa yana son cigaba da taka leda a wani wuri daban yayin da Barcelona suka yi zawarcinsa. Sai dai yarjejeniyar ba ta cimma ruwa ba.

    Silva ba shi da sha'awar tayin da ke kan tebur daga Saudi ya don komawa Al-Hilal. Duk da haka, dan wasan na da mabiya da suka hada da Barcelona da kuma Paris Saint-Germain, dukansu yana da sha'awar tattaunawa da su.

  8. Nawrocki ya koma Celtic

    Maik Nawrocki

    Asalin hoton, Getty Images

    Celtic ta sayi dan wasan baya Maik Nawrocki daga Legia Warsaw kan kudin da ba a bayyana ba.

    Dan wasan mai shekaru 22 ya amince da kwantiragin shekaru biyar da zakarun na Scotland.

    Nawrocki ya buga wasanni 30 a gasar Ekstraklasa ta Poland inda kungiyarsa ta Legia Warsaw ta zo ta biyu a kakar wasan da ta wuce, inda ya ci kwallaye hudu.

    Kocin Celtic Brendan Rodgers ya bayyana shi a matsayin " matashin dan wasa mai matukar daraja kuma wanda muka yi imanin zai zama babban kari ga kungiyar".

    Ya kara da cewa "Har ila yau, dan wasa ne da na sani sosai, ganin yadda ya taka leda a Legia Warsaw a gasar Europa kuma na san yana matukar sha'awar komawa Celtic," kamar yadda ya shaida wa shafin Intanet na kungiyar Celtic

  9. An tuhumi mai Tottenham Hotspur da laifin keta dokar kasuwanci

    Joe Lewis

    Asalin hoton, Getty Images

    An tuhumi mai kungiyar Tottenham Hotspur Joe Lewis da "laifin keta dokokin kasuwanci," in ji lauyan Amurka Damian Williams.

    Mista Williams ya yi amfani da sanarwar faifan bidiyo inda ya zargi hamshakin attajirin na Burtaniya da yin amfani da bayanan sirri wajen yin “kyaututtuka ga abokansa da masoyansa”.

    Mista Lewis "an tuhume shi kuma zai fuskanci shari'a" a gundumar Kudancin New York (SDNY), Mista Williams ya ce.

    Lauyan Mista Lewis, David Zornow ya ce tuhumarsa "babban kuskure ne".

    Lauyan ya kara da cewa dan shekaru 86 ya zo Amurka ne bisa radin kansa domin kare kansa daga tuhumar da ake masa.

    Mai magana da yawun Tottenham Hotspur ya ce a cikin wata sanarwa: "Wannan lamari ne na doka da ba shi da alaka da kulob din kuma saboda haka ba za mu yi wani bayani a kai ba."

    Mista Lewis na daya daga cikin attajiran Biritaniya. Ya mallaki daruruwan kadarori, ciki har da kulob din Tottenham Hotspur na Premier da ya saya a hannun Sir Alan Sugar a shekara ta 2001 kan fan miliyan 22.

  10. Fulham ta dauki Jimenez daga Wolves

    Raul Jimenez

    Asalin hoton, Getty Images

    Fulham ta sayi dan wasan gaban Mexico Raul Jimenez daga kungiyar Wolves ta Premier kan kudi kusan fan miliyan biyar.

    Dan wasan mai shekaru 32 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyu da Fulham, inda kungiyar ke da zabin kara shekara ta uku.

    Jimenez ya zura kwallaye 57 a wasanni 166 a kakar wasanni biyar da ya yi a Molineux bayan da ya koma daga kungiyar Benfica kan fan miliyan 30.

    Fulham sun yanke shawaran daukan Jimenez sabili da shakku kan makomar dan wasan gabansu Aleksandar Mitrovic.

  11. Man City ba za ta bar Walker ya tafi Munich ba a bana

    Kyle walker

    Asalin hoton, Getty Images

    Pep Guardiola ya dage cewa ba za a iya maye gurbin Kyle Walker a Manchester City ba, kuma kungiyar za ta yi iyakacin kokarinta wurin ganin cewa dan wasan bai koma Bayern Munich ba.

    An ruwaito cewa tuni dan wasan na Ingila ya sanar da kungiyar cewa yana son komawa kungiyar ta Bundesliga.

    Ana rade-radin cewa Bayern ta bai wa dan wasan bayan kwantiragi na shekaru biyu wanda ya hada da zabi na uku, wanda hakan ya sabawa tsarin kungiyar na mika dogon kwantaragi ga 'yan wasan da suka haura shekaru 30.

    Yayin da Bayern ke ci gaba da neman ganin ta shawo kan yarjejeniyar cikin gaggawa, Guardiola ya dage cewa kulob din za ta yi iya kokarinta don rike dan wasan bayan na Ingila.

  12. West Ham na tattunawa kan Maguire

    Harry Maguire

    Asalin hoton, Getty Images

    An sami rahotanni cewa West Ham ta fara tattaunawa da Manchester United game da daukar dan wasan baya Harry Maguire da dan wasan tsakiya Scott McTominay.

    Tattunawan farko da aka yi tsakanin kungiyoyin ya nuna akwai tazarar kima kan 'yan wasan biyu kuma rahotanni sun bayyana cewa United na ganin Maguire da McTominay a matsayin manyan 'yan wasa da kuma muhimman mambobin kungiyar.

    A halin da ake ciki, kocin Man Utd Erik ten Hag na sa ran cewa 'yan wasan biyu za su zama manyan ‘yan wasan kungiyar a kakar wasa mai zuwa.

    Maguire, wanda kwanan nan aka cire shi daga mukamin kyaftin din Man Utd, na da kungiyoyi a gasar Premier da kasashen waje da ke bibiyarsa.

  13. Wrexham ta doke Man united a wasan sada zumunci

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wrexham ta doke Manchester United da ci 3-1 a wasan sada zumunci da kaka buga a filin wasan Snapdragon da ke California.

    Nasarar da kungiyar ta samu ya zo da matsala inda dan wasanta Paul Mullin ya samu mummunar rauni.inda huhunsa ta huje yayin da ya yi a karo da golan United Nathan Bishop. .

    Ryan Reynolds bai samu damar halartan wasan ba, amma mamallakin Wrexham Rob McElhenney ya halarci ganin kungiyarsa ta samu nasara mai ban mamaki a gaban taron mutane 34,248.

    Kocin United Erik ten Hag, wanda manyan 'yan wasansa suka yi tattaki zuwa Texas kafin karawarsu da Real Madrid, ya kalli wasan da matasansa suka yi da ya ke galibi 'yan wasan kasa da shekara 21 ne.

    Haka kuma kungiyar ta fara wasan da gogaggen dan wasa Jonny Evans, wanda ya koma Manchester United daga Leicester City a karshen kakar wasan bara.

  14. Gasar cin kofin duniya: Sifaniya da Japan sun ketara zuwa zagaye na biyu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jenni Hermoso da Alba Redondo sun zira kwallaye biyu a raga yayin da Spain ta jaddada matsayinta a matsayin wacce za ta iya lashe gasar cin kofin duniya ta mata ta Fifa bayan da ta lallasa Zambia5-0 domn ta samu ketarawa zuwa zagaye na biyu a gasar.

    Sifaniya ta bude gasar a rukunin C inda ta doke Costa Rica 3-0 a makon da ya gabata, inda suka kai hare-hare 46 a ragar Costa Rica.

    Sun cigaba daga inda suka tsaya da Zambia, inda Teresa Abelleirata zura kwallo na farko a raga cikin minti tara da fara wasa.

    Hermoso ta kara ta biyu bayan mintuna hudu, daga nan sai Redondo ta zagaye mai tsaron ragar Zambia inda ta ci kwallonta na uku a wasan. Kafin Hermoso ta ci kwallonta ta na biyu bayan an dauki tsawon lokaci ana duban mataimakin alkalin wasa na bidiyo (VAR).

    Nasarar ta kuma tabbatar da cewa Japan - wacce ta doke Costa Rica 2-0 a wasan farko ranan Alhamis - ita ma ta samu ketarawa zuwa zagaye na biyu. Yanzu kasashen biyu za su kara a fafatawar neman matsayi na daya a ranar Litinin, 31 ga watan Yuli.