Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
James Milner zai koma Brighton
James Milner zai koma Brighton & Hove Albion a watan Yuli, bayan kammala kaka takwas a Liverpool.
Kungiyoyin da ke buga Premier League ne suka sanar da wannan labarin ranar Laraba.
Brighton ta sanar cewar, Milner, mai shekara 37 ya amince da kunshin yarjejeniyar kaka daya, domin ya taka mata leda a kaka mai zuwa.
James Milner ya lashe kofuna a Liverpool, ciki har da Champions League da Premier League da FA Cup da League Cup a wasa 332 da ya yi wa kungiyar.
Brighton za ta buga gasar zakarun Turai ta Europa League a badi, wanda shi ne karon farko a tarihin kungiyar.
Daraktan tsare-tsaren Brighton, David Weir ya ce kwarewar Milner za ta taimaka wa kungiyar a wasannin da za ta buga a kaka mai zuwa.
Milner har yanzu yana buga wa tawagar Ingila tamaula, wanda ya fara buga wa Leeds United tamaula a 2002, yana da shekara 16 da haihuwa.
Milner shine na uku a yawan buga wasanni a gasar Premier League inda ya buga wasa 619, bayan Gareth Barry mai karawa 652 da kuma Ryan Giggs mai fafatawa 632.