Kwazon da Rashford ya yi a Manchester United

Asalin hoton, BBC Sport
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.
Mohammed Abdu

Asalin hoton, BBC Sport
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
An dade ana ta alakanta Victor Osinhen da cewar zai bar Napoli kan fara kakar bana.
Dan wasan tawagar Najeriya ya taimakawa kungiyar ta lashe Serie A, kofin da ta dade ba ta dauka ba.
Tuni ake cewa kungiyoyi da dama na son sayen dan wasan, inda ake cewa Manchester United tana gaba-gaba wajen sayen dan wasan.

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon dan wasan Manchester City, Benjamin Mendy ya koma Lorient kan yarjejeniyar kaka biyu.
Dan kwallon tawagar Faransa ya koma kungiyar da ke buga babbar gasar Faransa, kwana biyar tsakani bayan da aka wanke shi da soso da sabulu kan zargin fyade.
Mendy ya bar Manchester City a watan jiya, bayan da kwantiraginsa ya kare, bayan da kungiyar ta dakatar da shi sakamakon tuhumarsa da ake yi.

Asalin hoton, Getty Images
Randal Kolo Muani ya nuna kansa a Eintracht Frankfurt
Dan wasan tawagar Faransa ya ci kwallo 15 ya bayar da 11 aka zura a raga a gasar Bundesliga da aka kammala ta 2022/23.

Asalin hoton, Getty Images
Amdouni ya ci kwallo 12 a babbar gasar Swistzerland ta Super League a kakar da ta wuce, shine kan gaba a yawan cin kwallaye a Uefa Conference League mai kwallo bakwai a raga.

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron bayan tawagar Sifaniya Jordi Alba ya koma Inter Miami da taka leda in ji shugaba Jorge Mas.
Mas ya ce tuni tsohon dan wasan Barcelona mai shekara 34 ya saka hannu kan kunshin yarjejeniya zai kuma buga karawar da kungiyar za ta yi da Atlanta.

Asalin hoton, Getty Images
Ana alakanta Rasmus Hojlund da cewar zai motsa a bana
Ana cewa mai shekara 20 dan kasar Denmark zai koma Manchester United da taka leda, bayan da ya ci wa Atalanta kwallo tara a wasa 32 a gasar Serie A da aka kammala.

Asalin hoton, Getty Images
Burnley ta kammala daukar Zeki Amdouni mai shekara 22 daga FC Basel.
Ana ta alakanta Harry Kane da cewar zai koma Bayern Munich da taka leda a bana, to sai dai Tottenham ba ta son sayar da dan kwallon.
Ko Kane zai yadda ya ci gaba da taka leda a Tottenham ko zai amince ya koma wata kungiyar kan fara kakar bana?

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta amince ta sayi Andre Onana kan fam miliyan 47.2 daga Inter Milan.
Kungiyar Old Trafford za ta biya jimillar kudi fam miliyan 43.8 don daukar golan tawagar Kamaru har da karin tsarabe-tsarabe.
United na san dan wasan mai shekara 27 zai samu buga mata wasannin sada zumunta a Amurka, wadda za ta kara da Lyon ranar Laraba daga baya ta je Amurkan.
Ya koma kan kwantiragin kaka biyar da cewar za a iya tsawaita masa shekara daya.

Asalin hoton, Getty Images
Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni kai tsaye a rana irin ta Laraba.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw zan gabatar da shirin.
Za ku iya bayar da gudunmuwa kai tsaye a BBC Hausa Facebook.