Bikin gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa na 2022

Wanann shafin zai ke kawo yadda ake bikin bayyana gwarzon kwallon kafa na duniya na Fifa na 2022

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Nan muka kawo karshen da fatan za ku tara a nan gaba.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun Wada ke muku fatan alheri.

  2. Wadanda suka lashe kyautar a baya:

    2016: Cristiano Ronaldo (Real Madrid)

    2017: Cristiano Ronaldo (Real Madrid)

    2018: Luka Modric (Real Madrid)

    2019: Lionel Messi (Barcelona)

    2020: Robert Lewandowski (Bayern Munich)

    2021: Robert Lewandowski (Bayern Munich)

  3. Labarai da dumi-dumi, Gwrazon dan kwallon kafa na duniya, Lionel Messi

    Fifa

    Asalin hoton, BBC Sport

  4. Sauran kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Fifa na 2022

    Masu takara

    Lionel Messi Argentina/PSG

    Karim Benzema Faransa/Real Madrid

    Kylian Mbappe Faransa/PSG

  5. Gwarzuwar kwallon kafa ta duniya, Alexia Putellas

    Fifa

    Asalin hoton, BBC Sport

  6. Masu takarar macen da ba kamarta a tamaula a duniya a 2022

    Beth Mead (England/Arsenal)

    Alex Morgan (USA/Orlando Pride/San Diego Wave)

    Alexia Putellas (Spain/Barcelona)

  7. Kyautar macen da ba kamarta a duniya a 2022

    Muna shirin shiga zangon bayyana gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta duniya ta mata ta 2022.

    Yanzu za a shakata kadan.

  8. Iyayen cin kwallaye Messi da Mbappe da Benzema da kuma Haaland? Kwallo....raga....kwallo.....raga...

  9. Labarai da dumi-dumi, 'Yan wasan Fifa 11 maza da ba kamarsu a 2022

    'Yan kwallon sun hada da Thibaut Courtois, Achraf Hakimi, Joao Cancelo, Virgil van Dijk, Kevin de Bruyne, Luka Modric, Casemiro, Lionel Messi, Kylian Mbappe, Karim Benzema da kuma Erling Haaland.

    Fifa

    Asalin hoton, BBC Sport

  10. Mata hudu daga ciki daga tawagar Ingila suka fito.

  11. Kyautar 'yan wasan Fifa 11 mata da suka yi fice

    'Yan wasan sun hada da Christiane Endler, Lucy Bronze, Mapi Leon, Leah Williamson, Wendie Renard, Alexia Putellas, Kiera Walsh, Lena Oberdorf, Alex Morgan, Sam Kerr da kuma Beth Mead.

  12. Labarai da dumi-dumi, Magoya baya da ba kamarsu, Argentina

    Wanda ya karbi kyautar shine Carlos 'Tula' Pascual. Ya fara goyon bayan Argentina tun daga gasar kofin duniya a 1974 zuwa ta Qatar a 2022.

  13. Magoya bayan Argentina da yawa da suka je Qatar suka mara baya, sannan dandazon da suka yi a kasar bayan lashe kofin duniya na uku jimilla.

    Fifa

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Kyautar magoba baya

    Magoya bayan Japan da suka dunga tsayawa bayan tashi wasa suka dunga tsince abubuwan da aka zura a wuraren zama.

    Fifa

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Labarai da dumi-dumi, Kyautar Fifa Fair Play, Luka Lochoshvili

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Sai kyautar wasa ba tare da gaba ba wato Fair play

    Wannan kyautar akan yi ga dan wasa ko kunyiya ko tawaga da sauransu ga duk wadanda suka nuna wasa ba tare da gaba ba

  17. Labarai da dumi-dumi, Kociyan da ba kamarsa a tamaula, Lionel Scaloni

    Fifa

    Asalin hoton, BBC Sport

  18. Fifa

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, PEP GUARDIOLA (Manchester City) A 2021-22, Guardiola ya ja ragamar Manchester City ta lashe Premier League na hudu a kaka biyar a kungiyar.
    Fifa

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, CARLO ANCELOTTI (Real Madrid) Ya lashe La Liga da Champions League a Real Madrid, bayan barin Everton. Ya kuma dauki Fifa Club World Cup da Uefa Super Cup.
  19. Yanzu sai takarar kocin da ba kamarsa

  20. Labarai da dumi-dumi, Kociyar da ba kamarta a 2022, Sarina Wiegman

    Fifa

    Asalin hoton, BBC Sport