Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Everton ta kammala daukar Dwight McNeil

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Suarez ya kammala komawa tsohuwar kungiyarsa Nacional

    Tsohon dan kwallon Liverpool da Barcelona, Luis Suarez ya kammala komawa kungiyarsa ta Nacional, wadda ya fara tun yana da kuruciya a Uruguay.

    Mai shekara 35, bai da yarjejeniya kawo yanzu tun bayan da kwantiraginsa ya kare a Atletico Madrid a karshen kakar da aka kammala.

    Ana sa ran Suarez zai koma Nacional a kalla lokacin da za a fara gasar kofin duniya a cikin watan Nuwamba.

  2. An amince da yarjejeniyar yuro miliyan 50 ...

    The Guardian ta ce Kounde zai koma Nou Camp kan kudi yuro miliyan 50.

    Idan har batun nan ya tabbata Chelsea ta yi rashi kenan? Wane dan kwallon za ta dauka ya maye gurbinsa.

  3. Shin ko Kounde ya kusan komawa Barcelona?

  4. Barkanmu da kasancewa

    Jama'a barkanmu da kasancewa a shirin labaran wasanni da yadda kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ke gudana a rana irin ta yau.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan gabatar da shirin da fatan za ku kasance da BBC Hausa a koda yaushe.

    Za ku iya bayar da gudunmuwa ko tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko a Twitter.