Suarez zai sake komawa kungiyarsa Nacional wadda tun yana da kuruciya

An wallafa

Tsohon dan kwallon Liverpool da Barcelona, Luis Suarez ya ce ya amaince zai koma kungiyarsa ta Nacional, wadda ya fara tun yana da kuruciya a Uruguay.

Mai shekara 35, bai da yarjejeniya kawo yanzu tun bayan da kwantiraginsa ya kare a Atletico Madrid a karshen kakar da aka kammala.

Ana sa ran Suarez zai koma Nacional a kalla lokacin da za a fara gasar kofin duniya a cikin watan Nuwamba.

A wani faifan video a kafar sada zumunta, Suarez ya ce ''Ina sa ran za mu kammala komai, ina fatan za mu cimma yarjejeniya kamar yadda muke da buri''.

Kimanin magoya bayan Nacional 20,000 saka sa fuska ta kwali mai dauke da hoton Suarez a wasannin kungiyar a baya-bayan nan tun lokacin da aka fara alanta dan kwallon da zai koma Uruguay da wasa.

Ya fara taka leda a matakin kwararren dan wasa a Nacional yana da shekara 18 a 2005, wanda ya taimaka kungiyar ta lashe lik din Uruguay daga nan kungiyar Turai, Groningen ta dauke shi.