An nada Ibrahim Galadima sabon shugaban Kano Pillars

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Ko Everton za ta sayar da Richarlison da Gordon a

    Tsohon dan kwallon Everton, Matt Jones ya sanar cewar idan kungiyar ta rabu da Richarlison da Anthony Gordon a bana, watakila za su ji jiki a kakar da za a fara a cikin watan Agusta.

    Tuni dai Tottenham ta cimma yarjejeniyar daukar dan wasan, ana kuma alakanta Gordon da cewar kungiyoyi da yawa na son daukarsa a bana.

    Everton

    Asalin hoton, Getty Images

  2. An nada Ibrahim Galadima sabon shugaban Kano Pillars

    Gwamnatin jihar Kano ta nada Ibrahim Galadima a matakin shugaban Kano Pillars na rikon kwarya, domin maye gurbin, Surajo Shuaibu Yahaya wanda aka fi sani da suna Jambul.

    An kori Jambul daga shugabancin Pillars, bayan cin zarafin mataimakin alkalin wasa a karawa da Pillars ta yi da Dakkada a gasar Firimiyar Najeriya fafatawar mako na 31 a Kano.

    Tun daga lokacin mahukuntan gasar Firimiyar Najeriya ta dakatar da Surajo Yahaya daga dukkan sabgogin Fimiyar.

  3. Labaran da jaridu ke yi kan cinikin 'yan kwallo, Daga jaridu

    Tottenham na sa ran kammala ciniki tsakaninta da Everton kan dan wasan gabanta Richarlison.(Football.London)

    Kazalika Spurs na tattaunawa game da batun daukar mai tsaron bayan Barcelona Clement Lenglet. (Sky Sports)

    Su kuwa kungiyoyin Chelsea da Tottenham da Arsenal za su gana da Torino don kulla cinikin da mai tsaron bayanta Gleison Bremer, wanda kungiyar ke neman fam miliyan 43 kansa, in ji Jaridar(90min).

    Liverpool ta yi watsi da tayin Nottingham Forest na fam miliyan 15, kan mai tsaron bayanta Neco Williams.(Mail)

  4. Takarar fitatcen dan kwallo kungiyoyin Afirka na bana

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Bernabei ya zama dan Argentina na farko da zai buga wa Celtic tamaula

    Celtic ta dauki dan kwallon Argentina, mai tsaron baya daga gefen hagu, Alexandro Bernabei, wanda ya amince da kunshin kwantiragin kaka biyar.

    Mai shekara 21 zai koma Scotland da taka leda daga Lanus kan fam miliyan 3.75.

    Bernabei zai zama na farko dan kasar Argentina da zai buga wa Celtic tamuala.

    Bernabei

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Tottenahm ta kusan daukar Richarlison daga Everton

    Tottenham ta kusan kammala daukar dan kwallon Everton, Richarlison, wanda ake sa ran za su karkare cinikin ranar Alhamis.

    An fahimci cewar dan wasan mai shekara 25 an tattauna da shi kan kunshin kwantiragi, wanda ke burin komawa Tottenham.

    Dan kwallon tawagar Brazil, ya koma Everton daga Watford kan fam miliyan 50 a 2018, kawo yanzu ya ci kwallo 53 daga 152 a kungiyar Merseyside.

    Shi ne ya zama wanda ke kan gaba a cin kwallaye a Everton a kakar da aka kammala, wadda da kyar kungiyar ta sha daga faduwa a babbar gasar tamaula ta Ingila.

    Richarlison

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Lukaku ya sake komawa Inter Milan domin buga wasannin aro

    Romelu Lukaku ya kamamal komawa Inter Milan, domin buga wasannin aro kaka daya, bayan shekara daya da Chelsea ta saye shi.

    Dan wasan tawagar Belgium ya ci kwallo 15 a dukkan wasannin da ya yi wa Chelsea a kakar da aka kammala har da takwas da ya zura a raga a wasa 26 a gasar Premier League da Manchester City ta lashe.

    Chelsea ta sayi dan wasan daga kungiyar da ke buga Serie A a matakin wanda ta dauka mafi tsada a tarihi, kan kwantiragin kaka biyar.

    Romelu Lukaku

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Barkanmu da wannan lokacin

    • Jama'a barkanmu da kasancewa a shirin labaran wasanni da yadda kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ke gudana a rana irin ta yau.Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan gabatar da shirin da fatan za ku kasance da BBC Hausa a koda yaushe.Za ku iya bayar da gudunmuwa ko tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko a Twitter.