Inter Milan ta karɓi aron Darmian

Asalin hoton, Inter Milan
Inter Milan ta sayi Matteo Darmian daga Parma a matsayin aro tare da zaɓin sayensa kan fan miliyan £2.2.
Ɗan ƙwallon mai shekara 30 zai ci gaba da wasa tare tsofaffin abokan wasansa a Manchester United Ashley Young da Romelu Lukaku da kuma Alexis Sanchez a filin wasa na San Siro.
Inter ta ɗauke shi ne kan yarjejeniyar shekara ɗaya.


