Katin gargaɗi ga Bayern, PSG 0-0 Bayern Munich
Sule ya yi wa Di Maria ƙeta a kusa dakurin tsakiyar fili kuma lafari ya ba shi katin gargaɗi.
Kati na huɗu kenan a wannan wasa.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku yadda ake fafatawa kai-tsaye tsakanin Bayern Munich da PSG a wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai ta Champions League na 2019-2020.
Umar Mikail
Sule ya yi wa Di Maria ƙeta a kusa dakurin tsakiyar fili kuma lafari ya ba shi katin gargaɗi.
Kati na huɗu kenan a wannan wasa.
Fili ya ɗauki sowa bayan an sake kayar da Neymar cikin ƙasa da minti ɗaya, har ma an bai wa Gnabry katin gargaɗi sakamakon ƙetar da ya yi masa.
'Yan wasan PSG sun harzuƙa, abin da ya jawo aka bai wa Paredes katin gargaɗi shi ma.
'Yan wasan benci na atasaye a gefen fili duk da cewa babu wata alamar gajiya a wannan wasa - kamar ana zuba musu wuta.
Wannan ƙwallon ta Mbappe, da ta shiga da an ci ƙwallo mai kyau sosai ganin yadda Di Maria ya shirya masa ita.
Amma ba mamaki mu sake ganin ire-irenta.
Wannan ne karon farko da aka tafi hutun rabin lokaci Bayern ba ta jefa ƙwallo a raga ba tun bayan dawowa ƙwallon ƙafa a watan Yuli.
Turƙashi! Ko za su ci ɗin? To wa ya sani ne!
Ƙwallon ce kawai ta rage ba a ci ba a wannan wasa amma komai ya zo.
Kowacce ƙungiya ta nuna ƙarewa matuƙa - da ma ba mu tsammaci ganin akasin haka ba.
Amma kamr yadda ake iya gani a hoton jadawalin da ke ƙasa, Bayern ta fi riƙe ƙwallo duk da cewa an fi ta kai hari.
Mbappe ya ɓarar da ƙwallo a cikin yadi na 18 - kai-tsaye ya buga ta hannun Neuer.
Duk irin ƙoƙarin da Di Maria ya yi na ba shi ƙwallon amma bai iya neman lokon zare ya lafa ta ba - da ma kuma Neuer sai an yi da gaske kafin ya bar ta ta wuce.
Saura minti biyu a tafi hutun rabin lokaci. Duk da cewa Bayern sun matsa amma ba wani alamun ci zuwa yanzu.
Gnabry ya so ɗauko ƙallo daga gefen dama bayan Kimmich ya tsikaro masa ita tun daga baya, sai dai Bernat ya tunkuɗa ta kwana.
Marquinhos ya kayar da Lewandowski kuma an bia wa Bayern bugun tazara.
An buga kuma ba tare da wata barazana ba ga PSG.
Ba za ku daina jin sunan nan ba - Lewandowski - har sai an busa usur ɗin ƙarshe a filin nan.
Ya ɗaɗa wa Navas ƙwallon da bai iya kama ta ba sai da 'yan bayansa suka kawo ɗauki.
Jerome Boateng ya fita, Niklas Sule ya karɓe shi.
Boateng ya tafi zuwa gefen raga kuma da alama rauni ya ji.
An bai wa Alphonso Davies katin gargaɗi
Di Maria ya samu ƙallo mai matuyƙr kyau amma ya ɗaɗa ta sama.
Neymar ne ya shiryoi ƙwallo tun daga tsakiya har zuwa ragar Bayern amma Di Maria bai kwantar da ƙafarsa ba. Da tuni 1-0.
Da ma dama kawai yake jira; ya ɗaɗa ƙwallon ta daki turke; Kylo Navas bai iya yi mata komai ba.
Saura ƙiris Neymar ya cilla ƙwallo a zaren Neuer; da ƙayar mnayen gpolan ya tare ta kuma Mbappe ma mayar da ita amma ta fita bugun kwana.
Mummunan hari kenan na farko a wannan wasa kuma masu aikin ne dai suka yi aikinsu - Neymar da Mbappe.
Wasa ya fara ɗumi fa, domin yanzun nan Mbappe ya ɗaɗa ƙwallo har sau biyu a cikin yadi na 18 ɗin bayern.
Sai dai sau biyu tana dukan jikin 'yan bayan Bayern ɗin tana dawowa.
Bayer na ci gaba da shafa ƙwallo amma duk da haka hankalinsu ba a kwance yake ba.
Thiago ya yi wa Mbappe ƙeta a ɓangaren hagu , sai dai an bugo bugun tazara amma babu haɗari ga Manual Neur - Davies ya tsige ta da ka.
Marquinhos ya bayar da ƙallo a gaban ragarsu amma Bayern ba ta iya amfana da ita ba.
Kingsley Coman ya samu bugun tazara a gefen hagu kuma an buga babu wani haɗari ga PSG.